عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بِن مَسْعُودٍ رضي الله عنه قَالَ: سَأَلْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَيُّ العَمَلِ أَحَبُّ إِلَى اللَّهِ؟ قَالَ: «الصَّلاَةُ عَلَى وَقْتِهَا»، قَالَ: ثُمَّ أَيٌّ؟ قَالَ: «ثُمَّ بِرُّ الوَالِدَيْنِ» قَالَ: ثُمَّ أَيٌّ؟ قَالَ: «الجِهَادُ فِي سَبِيلِ اللَّهِ» قَالَ: حَدَّثَنِي بِهِنَّ، وَلَوِ اسْتَزَدْتُهُ لَزَادَنِي.
Daga Abdullahi dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanne aiki ne mafifici a wurin Allah? ya ce: "Sallah akan lokacinta", Ya ce: Sannan wanne? Ya ce: "Sannan biyayya ga mahaifa" Ya ce: Sannan wanne? Ya ce: Yaki a tafarkin Allah" ya zantar dani su, da na nemi ya kara min da ya karamin.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
An tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanne aiki ne mafi soyuwa agurin Allah? Sai ya ce: Sallar farilla a lokukacinta wanda mai shari'a ya iyakance shi, sannan biyayya ga mahaifa, da kyautata musu, da tsayuwa da hakkinsu, da barin saba musu, sannan yaki a tafarkin Allah, dan daukaka kalmar Allah - Mai girma da daukaka -, da kare addinin Allah ma'abotansa, da bayyanar da alamominsa, hakan yana kasancewa ne da rai da dukiya.
Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ya bani labarin wadanan ayyukan; da na ce masa: Sannan wanne? da ya karamin.
Fa’idoji
- Fifikon ayyuka a tsakaninsu gwargwadon yadda Allah yake son su .
- Kwadaitarwar muslmi akan kwadayi akan ayyuka mafifita sai mafifita.
- Fifikon amsawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da mafifitan ayyuka gwargwadan sabanin mutane da halayensu, da abinda yake mafi yawan amfani ga kowanne daya daga cikinsu.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 112) (527).
صحيح مسلم (1/ 90) (85).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 70).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص84).
تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 108).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «إِنَّ أَثْقَلَ صَلَاةٍ عَلَى الْمُنَافِقِينَ صَلَاةُ الْعِشَاءِ وَصَلَاةُ الْفَجْرِ، وَلَوْ يَعْلَمُونَ مَا فِيهِمَا لَأَتَوْهُمَا وَلَوْ حَبْوًا، وَلَقَدْ هَمَمْتُ أَنْ آمُرَ بِالصَّلَاةِ فَتُقَامَ، ثُمَّ آمُرَ رَجُلًا فَيُصَلِّيَ بِالنَّاسِ، ثُمَّ أَنْطَلِقَ مَعِي بِرِجَالٍ مَعَهُمْ حُزَمٌ مِنْ حَطَبٍ إِلَى قَوْمٍ لَا يَشْهَدُونَ الصَّلَاةَ، فَأُحَرِّقَ عَلَيْهِمْ بُيُوتَهُمْ بِالنَّارِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai cewa mafi nauyin sallah a kan munafukai (ita ce) sallar Issha'i da sallar Asuba, da sun san abin da ke cikinsu da sun zo musu ko da da jan ciki ne, haƙiƙa na yi niyyar in yi umarni da sallah, sai atsai da ita, sannan in umarci wani mutum ya yi wa mutane sallah, sannan in tafi a tare dani da wasu mazaje a tare da su akwai ɗauri na itatuwa zuwa mutanen da ba sa zuwa sallah, sai na ƙona gidajensu da wuta".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana ba da labari game da munafukai da kasalarsu a kan zuwa sallah, musamman ma sallar Issha'i da Asuba, kuma cewa su da ace suna sanin girman lada da sakamako a halartarsu tare da jama'ar musulmai da sun zo musu ko da da rarrafe ne kamar rarrafen yaro da hannaye da kuma gwiwoyi.
Haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi niyyar ya yi umarni a tsai da Sallah, sai ya sanya wani mutumin ya yi wa mutane limanci a maimakonsa, sannan ya tafi tare da shi akwai wanda zai ɗauki ɗauri na itatuwa zuwa mazajen da ba sa zuwa sallar jama'a, sai ya ƙona gidajensu da wuta; sabo da tsananin abin da suka aikata na laifi a hakan, - sai dai bai aikata ba - sabo da abinda ke cikin gidaje na mata da yara da babu-ruwansu da kuma wasunsu cikin masu uzuri waɗanda ba su da wani laifi.
Fa’idoji
- Haɗarin ƙin zuwa sallar jam’i a masallaci.
- Munafukai ba sa nufin komai a ibadarsu sai riya da jiyarwa, ba sa zuwa sallah sai lokacin da mutane suke ganainsu.
- Girman ladan sallar issha'i da Asuba tare da jama'a, kuma cewa su sun cancanci a zo musu ko da da rarrafe ne.
- Kiyaye sallar Issha'i da Asuba kubuta ce daga munafunci, kuma ƙin zuwar musu yana daga siffofin maunafukai.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 451) (651).
صحيح البخاري (1/ 132) (657).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 88).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص107).
تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 136).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ جَرِيرِِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ رضي الله عنه قَالَ: بَايَعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلَى شَهَادَةِ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ، وَإِقَامِ الصَّلاَةِ، وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ، وَالسَّمْعِ وَالطَّاعَةِ، وَالنُّصْحِ لِكُلِّ مُسْلِمٍ.
Daga Jariri Dan Abadullahi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi caffa - akan shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu Manzon Allah ne, da tsaida sallah, da bada zakka, da ji da bi, da nasiha ga kowanne musulmi.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Sahabi Jariru Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa shi ya dorawa kansa ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alkawari akan tauhidi, da yin salloli biyar a yini da dare, da sharuddansu da rukunansu da wajibansu da sunnoninsu, da kuma bada zakka ta dole, ita ce ibada ta dukiya wajiba, ana karba daga mawadata ana bada ita ga macancanta daga talakawa da wasunsu, da kuma biyayya ga shugabanni, da nasiha ga kowanne musulmi, hakan ta hanyar kwadayi akan amfanar da shi, da sadar da alheri gare shi, da tunkude sharri daga gare shi ta hanyar magana da aikatawa.
Fa’idoji
- Muhimmancin sallah da zakka, su biyun suna daga rukunan Musulunci.
- Muhimmancin nasiha da yin nasiha tsakanin musulmai, har Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa sahabbai - Allah Ya yarda dasu - caffa akanta.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 111) (524)، (3/ 72) (2157).
صحيح مسلم (1/ 75) (56).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 272).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص145).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 398).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 206).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comوعن جابر رضي الله عنه قال: سُئِل رسول الله صلى الله عليه وسلم أي الصلاة أفضل؟ قال: «طُول القُنُوتِ».
An rawaito daga Jabir -Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah ya ce: An tambayi Manzon Allah SAW wace Sallah ce tafi? ya ce: Mafi tsawon Al=qunuti"
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين؛ للإمام أبي زكريا النووي، تحقيق د. ماهر الفحل، دار ابن كثير-دمشق، الطبعة الأولى، 1428ه .
- نزهة المتقين شرح رياض الصالحين؛ تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة-بيروت، الطبعة الرابعة عشر، 1407هـ.
- صحيح مسلم؛ للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبد الباقي، دار عالم الكتب-الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ.
- تطريز رياض الصالحين؛ تأليف فيصل آل مبارك، تحقيق د. عبد العزيز آل حمد، دار العاصمة-الرياض، الطبعة الأولى، 1423هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم كان يقول: «الصَّلَوَاتُ الْخَمْسُ، وَالْجُمُعَةُ إِلَى الْجُمُعَةِ، وَرَمَضَانُ إِلَى رَمَضَانَ، مُكَفِّرَاتٌ مَا بَيْنَهُنَّ إِذَا اجْتَنَبَ الْكَبَائِرَ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce "Salloli biyar, da Juma'a zuwa Juma'a, da Ramadan zuwa Ramadan, masu kankare a binda ke tsakaninsu ne idan ya nisanci manyan zunubai".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa; Salloli biyar ababen faralantawa a yini da dare ne, da sallar Juma'a a kowane mako, da azimin watan Ramadan a kowacce shekara, masu kankare abinda ke tsakaninsu ne na kananan zunubai da sharadin nisantar manyan zunubai. Amma manyan zunubai kamar zina da shan giya ba mai kankaresu sai tuba.
Fa’idoji
- Zunubai daga cikinsu akwai kananu a kwai kuma manya.
- Kankare kananun zunubai abin shardantawane da nisantar manyan zunuban.
- Manyan zunubai su ne zunuban da haddi yazo a cikinsu, ko narko a lahira ya zo a cikinsu, ko fushi, ko akwai tsawatarwa a cikinsu, ko la'anta ga mai aikatasu, kamar zina da shan giya.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 209) (233).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 183).
نزهة المتقين بشرح رياض الصالحين، لمصطفى سعيد الخن (1/ 158).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص108).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم بن عيد الهلالي (1/ 209).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ مَعْدَانَ بْنِ أَبِي طَلْحَةَ الْيَعْمَرِيُّ قَالَ: لَقِيتُ ثَوْبَانَ مَوْلَى رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقُلْتُ: أَخْبِرْنِي بِعَمَلٍ أَعْمَلُهُ يُدْخِلُنِي اللهُ بِهِ الْجَنَّةَ؟ أَوْ قَالَ قُلْتُ: بِأَحَبِّ الْأَعْمَالِ إِلَى اللهِ، فَسَكَتَ. ثُمَّ سَأَلْتُهُ فَسَكَتَ. ثُمَّ سَأَلْتُهُ الثَّالِثَةَ فَقَالَ: سَأَلْتُ عَنْ ذَلِكَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: «عَلَيْكَ بِكَثْرَةِ السُّجُودِ لِلَّهِ، فَإِنَّكَ لَا تَسْجُدُ لِلَّهِ سَجْدَةً، إِلَّا رَفَعَكَ اللهُ بِهَا دَرَجَةً، وَحَطَّ عَنْكَ بِهَا خَطِيئَةً» قَالَ مَعْدَانُ: ثُمَّ لَقِيتُ أَبَا الدَّرْدَاءِ فَسَأَلْتُهُ فَقَالَ لِي: مِثْلَ مَا قَالَ لِي: ثَوْبَانُ.
Daga Ma’adan ɗan Abu Dalha Al-Ya'amury ya ce: Na gamu da Sauban 'yantaccen bawan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai na ce: Ka ba ni labari da wani aikin da zan aikata shi Allah Ya shigar da ni Aljanna da shi? ko ya ce, na ce: Da mafi son ayyuka zuwa ga Allah, sai ya yi shiru. Sannan na tambaye shi, sai ya yi shiru, sannan na tambaye shi a karo na uku sai ya ce: Na tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - game da wannan, sai ya ce: "Na umarce ka da yawan sujjada ga Allah, domin kai ba za ka yi wata sujjada ga Allah ba, sai Allah Ya ɗaga darajar ka da ita, kuma Ya sarayar da kuskure da ita" Ma'adan ya ce: Sannan na gamu da Abu al-Darda'i sai na tambaye shi sai ya fada min abinda Sauban ya faɗa mini.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
An tambayi annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da aikin da zai zama sababin shiga aljanna, ko game da mafi soyuwar ayyuka a wurin Allah?
Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce wa mai tambayar: Ka lazimci yawan sujjada a cikin sallah, domin kai ba za ka yi wa Allah sujjada ba sai Ya ɗaga darajarka da ita, kuma Ya kankare kurakuranka da ita.
Fa’idoji
- Zaburar da musulmi akan kwaɗayi ga sallah ta farilla da nafila, saboda yadda ta kunshi sujjada.
- Bayanin zurfin ilimin sahabbai da saninsu cewa aljanna ba'a samunta - bayan rahamar Allah - sai da aiki.
- Sujjada a cikin sallah tana daga mafi girman sabubban ɗaga darajoji, da gafarta zunubai.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 353) (488).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين.
بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (1/ 188).
نزهة المتقين، لمجموعة من الباحثين (1/ 137).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 105).
شرح النووي على مسلم، (4/ 205).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أَبِي مُوسَى الأَشْعَرِيِّ رضي الله عنه: أَنَّ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم قَالَ: «مَنْ صَلَّى الْبَرْدَيْنِ دَخَلَ الْجَنَّةَ»
Daga Abu Musa al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya sallaci sanyaya biyu zai shiga aljanna".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zaburar da kwaɗaitarwa akan sallar sanyaya biyu ; su ne sallar asuba da la'asar, kuma Ya yi wa wanda ya yi su da haƙƙinsu na lokaci da jama'a da wanin haka albishir cewa sun zama sababi na shigarsa aljanna.
Fa’idoji
- Falalar kulawa akan sallar asuba da la'asar; domin asuba tana kasancewa ne a lokacin daɗin bacci, la'asar kuma tana kasancewa ne lokacin shagaltuwar mutum da aikinsa, wanda ya kiyayesu ya kasance mafi cancanta ya kiyaye ragowar salloli.
- An ambaci sallar asuba da la'asar da sanyaya biyu; domin sallar asuba a cikinta akwai sanyin dare, sallar la'asar kuma a cikinta akwai sanyin rana, koda sun kasance a lokaci na zafin rana, saidai wannan lokacin ya fi saukin (zafi) kafin wannan lokacin, ko kuma ambatansu ya zama ta babin rinjayarwa kamar yadda ake cewa: Watanni biyu ga rana da wata.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 119) (574).
صحيح مسلم (1/ 440) (635).
نزهة المتقين، لمجموعة من الباحثين (1/ 159).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 187).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّهُ سَمِعَ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «أَرَأَيْتُمْ لَوْ أَنَّ نَهَرًا بِبَابِ أَحَدِكُمْ يَغْتَسِلُ فِيهِ كُلَّ يَوْمٍ خَمْسًا، مَا تَقُولُ ذَلِكَ يُبْقِي مِنْ دَرَنِهِ؟» قَالُوا: لَا يُبْقِي مِنْ دَرَنِهِ شَيْئًا، قَالَ: «فَذَلِكَ مِثْلُ الصَّلَوَاتِ الخَمْسِ، يَمْحُو اللَّهُ بِهِ الخَطَايَا».
Daga Abu Huraira Allah ya yarda da shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Shin kuna ganin cewa da ace akwai wata korama a kofar dayanku yana wanka a cikinta kowacce rana sau biyar, shin kuna zatan wani abu na dattinsa zai rage ?" Suka ce: Ba abin da zai rage dattinsa, ya ce: "To hakan tamkar salloli biyar ne, Allah Yana shafe kurakurai da su".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kamanta salloli biyar a kowanne yini da dare a kawarwa da kankarewarsu ga kananan zunubai da kurakurai da korama a kofar mutum da yake wanka a cikinta kowacce rana sau biyar, babu wani abu da zai ragu daga dattinsa.
Fa’idoji
- Wannan falalar ta kebanci kankare kananun zunubai ne, amma manya babu makawa daga tuba daga gare su.
- Falalar yin salloli biyar da kiyayewa akansu da sharuddansu da rukunansu da wajibansu da sunnoninsu.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 112) (528).
صحيح مسلم (1/ 462) (667).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين (2/ 773).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص610).
المعجم الوسيط، (1/ 282).
النهاية في غريب الحديث والأثر، لابن الأثير (2/ 115).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com