Ammar Ibnu Yasir - Allah Ya yarda da su - ya shiga masallaci sai ya yi sallar nafila, kuma sallar ta kasance sassauƙa ce, lokacin da ya fita daga cikin masallaci, sai Abdullahi Ibnu Anamah ya bi shi ya kuma ce da shi: Ya Aba Yaƙazan, haƙiƙa na ganka ka sauƙaƙa sallarka! Ammar ya ce: Shin ka ganni ne na tauye wani abu daga rukunanta ko wajibanta ko sharuɗɗanta?! ya ce: A'a, ya ce: Lallai cewa ni na sauƙaƙata ne tun kafin shaiɗan ya shagaltar da ni. Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: Lallai bawa zai yi sallah, amma ba za'a rubuta masa (komai) daga ladanta ba sai ɗaya bisa gomanta, ko ɗaya bisa taranta, ko ɗaya bisa takwas ɗinta, ko ɗaya bisa bakwanta, ko ɗaya bisa shidanta, ko ɗaya bisa biyar ɗinta, ko ɗaya bisa huɗunta, ko ɗaya bisa ukunta, ko rabinta.
- Kwaɗayin magabata akan yin nasiha a tsakaninsu.
- Neman tabbatarwa da kuma tambaya kafin yin inkari.
- wadatuwa a bada amsa game da tambaya da kuma rikitarwa, da faɗin maganar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Tawayar ladan sallah da tawayar khushu'i da tadabburin ma'anoninta a cikinsa.
- Kwaɗaitarwa mai ƙarfi da kuma zaburarwa mai tsanani akan yin khushu'i a cikin sallah da kuma halarto da zuciya tare da Allah - Maɗaukakin sarki -.
سنن أبي داود (2/ 97) (796). عون المعبود (3/3). شرح سنن أبي داود للعباد (103/ 15). فيض القدير (2/ 334). التيسير بشرح الجامع الصغير (1/ 283).