عَنْ أَنَسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: أَنَّ رَجُلًا سَأَلَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنِ السَّاعَةِ، فَقَالَ: مَتَى السَّاعَةُ؟ قَالَ: «وَمَاذَا أَعْدَدْتَ لَهَا». قَالَ: لاَ شَيْءَ، إِلَّا أَنِّي أُحِبُّ اللَّهَ وَرَسُولَهُ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: «أَنْتَ مَعَ مَنْ أَحْبَبْتَ». قَالَ أَنَسٌ: فَمَا فَرِحْنَا بِشَيْءٍ، فَرِحْنَا بِقَوْلِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَنْتَ مَعَ مَنْ أَحْبَبْتَ» قَالَ أَنَسٌ: فَأَنَا أُحِبُّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَأَبَا بَكْرٍ، وَعُمَرَ، وَأَرْجُو أَنْ أَكُونَ مَعَهُمْ بِحُبِّي إِيَّاهُمْ، وَإِنْ لَمْ أَعْمَلْ بِمِثْلِ أَعْمَالِهِمْ.
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - daga alkiyama, sai ya ce: Yaushe ne alkiyama? Ya ce: "Mai ka tanadar mata?" Ya ce: Babu komai, sai dai ni ina son Allah da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce; "Kai kana tare da wanda ka so" Anas ya ce: Bamu taba farin ciki da wani abu ba, irin farin cikinmu da faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Kai kana tare da wanda ka so" Anas ya ce: Ni ina son Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da Abubakar, da Umar, kuma ina kaunar in kasance tare da su dan son da nake musu, koda ban yi aiki irin aikinsu ba.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Wani mutumin karkara irin waɗanda suke zama a sahara ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: game da lokacin tashin alkiyama?
Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi Ya ce masa: Meka tanadar mata na aiki na gari?
Sai mai tambayar ya ce: Ban tanadi wani aiki mai yawa ba sai dai ni ina son Allah da ManzonSa, bai ambaci wanin hakan ba daga ayyuaka na zuciya da jiki da dukiya; domin su dukkaninsu rassa ne ga soyayya masu jerantuwa ne akanta, kuma domin soyayya ta gaskiya tana zaburar da kokarin yin aiki na gari.
Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi Ya ce masa: Lallai kai kana tare da wanda ka so a aljanna.
Sai sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suka yi farin ciki mai girma da wannan busharar.
Sannan Anas ya bada labarin cewa shi yana son Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da Abubakar, da Umar, kuma yana kaunar ya kasance tare da su, koda aikinsa bai zama irin aikinsu ba.
Fa’idoji
- Hikimar Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - a amsawa mai tambaya, yayin da ya nunar da shi akan abinda zai himmatu akansa kuma zai tseratar da shi, shi ne: Yin tanadi dan lahira da abinda zai anfanar da kuma aiki na gari.
- Allah Ya boye sanin alkiyama ga bayi dan mutum ya kasance mai tanadi mai shirin haɗuwa da Allah.
- Falalar son Allah da ManzonSa da mutanen kirki cikin muminai, da gargaɗarwa daga son mushrikai.
- Faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Kai kana tare da wanda ka so. Ba ana nufin daidaituwa a daraja da matsayi ba, a'a abin nufi kasancewarsu a aljanna ta inda kowane ɗaya daga cikinsu zai samu damar ganin ɗayan koda guri ya nisanta.
- Fadakar da musulmi dan shagaltuwa da mafi maslaha da kuma mafi anfani gare shi, da barin tambaya daga abinda ba zai anfanar da shi ba.
Madogara
صحيح البخاري (5/ 12) (3688).
صحيح مسلم (4/ 2032) (2639).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 435).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (6/ 177).
المعجم الأوسط، للطبراني (1/ 131).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 342).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه مرفوعًا: «أن رجلا زَارَ أخًا له في قرية أخرى، فأَرْصَدَ الله تعالى على مَدْرَجَتِهِ مَلَكًا، فلما أتى عليه، قال: أين تريد؟ قال: أريد أخًا لي في هذه القرية، قال: هل لك عليه من نعمةٍ تَرُبُّهَا عليه؟ قال: لا، غيرَ أني أَحْبَبْتُهُ في الله تعالى ، قال: فإني رسولُ الله إليك بأنَّ الله قد أَحَبَّكَ كما أَحْبَبْتَهُ فيه».
Daga Abu Hurairah - Allah ya yarda da shi - da isnadi: “Wani mutum ya ziyarci dan’uwansa a wani kauye, sai Allah Madaukaki Ya sanya mala’ika a sikeli nasa, don haka lokacin da ya je masa, sai ya ce: Ina kake so? Ya ce: Ina son dan uwa a gare ni a wannan kauye, sai ya ce: Shin kuna da wata falala da za a tashe shi a kansa? Sai ya ce: A'a, face dai na so shi a cikin Allah - Madaukaki - ya ce: Ni Manzon Allah ne zuwa gare ku cewa Allah ya so ku kamar yadda kuka so shi a cikinsa
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، سليم بن عيد الهلالي، الدمام، دار ابن الجوزي، الطبعة: الأولى، 1415هـ.
تطريز رياض الصالحين، فيصل بن عبد العزيز المبارك، المحقق: عبد العزيز بن عبد الله آل حمد، دار العاصمة للنشر والتوزيع، الرياض، الطبعة: الأولى، 1423هـ - 2002م.
رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين، أبو زكريا محيي الدين النووي، تحقيق ماهر الفحل، دار ابن كثير، دمشق، بيروت، الطبعة: الأولى، 1428هـ.
رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين، أبو زكريا محيي الدين النووي، تحقيق: عصام هادي، وزارة الأوقاف والشؤون الإسلامية القطرية، دار الريان، بيروت، الطبعة: الرابعة، 1428هـ.
شرح رياض الصالحين، محمد بن صالح العثيمين، دار الوطن، الرياض، 1426هـ.
صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَنَسٍ رضي الله عنه قَالَ: كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُكْثِرُ أَنْ يَقُولَ: «يَا مُقَلِّبَ القُلُوبِ ثَبِّتْ قَلْبِي عَلَى دِينِكَ»، فَقُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ، آمَنَّا بِكَ وَبِمَا جِئْتَ بِهِ فَهَلْ تَخَافُ عَلَيْنَا؟ قَالَ: «نَعَمْ، إِنَّ القُلُوبَ بَيْنَ أُصْبُعَيْنِ مِنْ أَصَابِعِ اللهِ يُقَلِّبُهَا كَيْفَ يَشَاءُ».
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yawaita faɗin: "Ya mai jujjuya zukata Ka tabbatar da zuciyata akan addininKa" sai na ce: Ya Manzon Allah, mun yi imani da kai da kuma abinda ka zo da shi, shin kana jin tsoro akanmu ne? ya ce: "Eh, lallai zukata suna tsakanin yatsu biyu daga yatsun Allah Yana jujjuyasu yadda Ya ga dama".
Tirmizi da Ahmad sun rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Mafi yawan addu'ar Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance rokon Allah ne tabbata akan addini da biyayya, da nisanta daga karkata da kuma bata, Sai Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya yi mamakin yawaitawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan wannan addu'ar, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ba shi labarin cewa zukata suna tsakanin yatsu biyu daga yatsun Allah Yana juyasu yadda Ya ga dama, Zuciya ita ce gurin imani da kafirci, hakika an anbaci zuciya (Kalbu) saboda yawan jujjuawarta; ita ce mafi tsananin jujjuyawa daga tukunya idan ta tafarfasa, wanda Allah Ya so Zai tsaida zuciyarsa akan shiriya, ya tabbatar da shi akan addini, wanda Allah Ya ga dama kuma Zai juyar da zuciyarsa daga shiriya zuwa karkata da bata.
Fa’idoji
- Kankan da kan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga Ubangijinsa da kankar dakai gareShi, da nunawa al'umma rokon hakan.
- Muhimmancin tsayuwa akan gaskiya da tabbata akan addini, kuma izina da karshe ne.
- Bawa ba ya wadatuwa daga Allah Ya tabbatarwa shi akan musulunci koda kiftawar ido.
- Kwadaitarwa akan yawaita wannan addu'ar dan koyi da Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi -.
- Tabbata akan musulunci shi ne ni'ima mafi girma wacce yake kamata ga bawa ya yi kokari gareta kuma ya godewa Ubangijinsa akanta.
Madogara
سنن الترمذي (4/ 19) (2140).
مسند أحمد (19/ 160) (12107).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (17/ 476).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 567).
نزهة المتقين، لمجموعة من الباحثين (2/ 1014).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص808).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (6/ 41).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَن سَهْلِ بْنِ حُنَيْفٍ رضي الله عنه أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنْ سَأَلَ اللهَ الشَّهَادَةَ بِصِدْقٍ بَلَّغَهُ اللهُ مَنَازِلَ الشُّهَدَاءِ، وَإِنْ مَاتَ عَلَى فِرَاشِهِ».
Daga Sahl ɗan Hunaif - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya roki Allah shahada da gaskiya, Allah Zai kai shi matsayin shahidai, koda ya mutu akan shinfiɗarsa".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda ya nemi shahada da mutuwa a tafarkin Allah, kuma ya kasance mai gaskiya mai tsarkake niyyarsa ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -, Allah Zai ba shi darajojin shahidai saboda niyyarsa ta gaskiya koda ya mutu akan shinfiɗa ba a yaki ba.
Fa’idoji
- Gaskiyar niyya tare da aikata abin da za'a iya, sababi ne na samun abin nufi na lada da sakamako, koda bai yi aikin da ake nema ba.
- Kwaɗaitarwa akan jihadi da neman shahada a tafarkin Allah - Mai girma da ɗaukaka -.
- Baiwar Allah - Mai girma da ɗaukaka - ga wannan al'ummar, shi (Allah) yana bada mafi ɗaukakar darajoji a cikin aljanna da kankanin aiki.
Madogara
صحيح مسلم (3/ 1517) (1909).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 123).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 87).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «قَالَ اللهُ تَبَارَكَ وَتَعَالَى: أَنَا أَغْنَى الشُّرَكَاءِ عَنِ الشِّرْكِ، مَنْ عَمِلَ عَمَلًا أَشْرَكَ فِيهِ مَعِي غَيْرِي تَرَكْتُهُ وَشِرْكَهُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah - alherinSa ya yawaita Ya girmama - Ya ce: Ni ne mafi wadatar abokanan tarayya daga shirka, duk wanda ya aikata wani aiki ya hada ni da wani a aikin to Zan bar shi da shirkarsa".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana sanar da cewa Allah - alherinSa ya yawaita Ya girmama - Ya ce: Lallai cewa Shi ne mafi wadatar abokanan tarayya game da shirka, to Shi ne Mawadaci daga dukkanin komai, kuma cewa mutum idan ya aikata wani aiki na biyayya kuma ya sanya shi ga Allah da kuma wanin Allah; to Zai bar shi ba zai karba daga gare shi ba, kuma Ya miyarwa da mai shi; To tsarkake aiki yana wajaba ga Allah - Madaukakin sarki -; domin cewa shi Allah tsarki ya tabbatar maSa ba ya karba sai abinda ya zama tsarkakakke ga zatinsa Mai girma.
Fa’idoji
- Gargadi daga shirka da dukkanin ire-irenta; kuma cewa ita tana hana karbar aiki.
- Jin wadatar Allah da Girmansa yana daga abinda yake taimakawa ga ikhlasi a cikin ayyuka.
Madogara
صحيح مسلم (4/ 2289) (2985).
شرح النووي على مسلم (18/ 115).
الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص287).
الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص325).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لاَ عَدْوَى وَلاَ طِيَرَةَ، وَلاَ هَامَةَ وَلاَ صَفَرَ، وَفِرَّ مِنَ المَجْذُومِ كَمَا تَفِرُّ مِنَ الأَسَدِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Babu cuta mai yaɗuwa zuwa ga wani (da karantanta) babu canfi, ko mujiya, ko Safar, kuma ka guje wa kuturu kamar yadda kake guje wa zaki".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana sashin al'amuran Jahiliyya (maguzawa) dan gargaɗi daga gare su, da kuma bayanin al'amari yana hannun Allah, kuma wani abu ba ya kasancewa sai da umarninSa da ƙaddarawarSa, su ne:
Na farko: Mutanen Jahiliyya sun kasance suna zatan cewa cuta tana yaɗuwa da kanta; sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi hani daga ƙudirce tashin cuta daga mara lafiya zuwa ga mai lafiya da ɗabi'arta; Allah Shi ne Mai tasarrufi a cikin kasantattu; kuma Shi ne wanda Yake saukar da cuta kuma Yake ɗauketa, hakan ba ya faruwa saida nufinSa da ƙaddarawarSa.
Na biyu: Mutanen Jahiliyya sun kasance idan sun fita dan wata tafiya ko kasuwanci, sai su yi wa tsuntsu tsawa, idan ya tashi ɓangaren dama sai su yi murna, idan ya tashi ɓangaren hagu sai su canfa su dawo, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi hani daga wannan canfin da tsuntsu, ya kuma bayyana cewa hakan akida ce ɓatacciya.
Na uku: Mutanen Jahiliyya sun kasance suna cewa: Idan mujiya ta faɗo a kan wani gida sai musiba ta samu mutanen wannan gidan; sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi hani game da canfa hakan.
Na huɗu: Ya yi hani daga canfa watan Safar, shi ne wata na biyu daga watannin ƙamariyya. (Wasu kuma) suka ce Safar shi ne: Wata micijiya ce da take a ciki tana samun dabbobi da mutane, suna riya cewa ita ce mafi tsananin yaɗuwa daga cutar kirci; sai ya kore wannan akidar.
Na biyar: Ya yi umarni da nisantar wanda aka shafa da cutar kuturta kamar yadda zaka nisanci zaki, hakan dan bai wa kai kariya da kuma nema masa kuɓuta da kuma aikata sabubban da Allah ya yi umarni da su. Kuturta: Wata cuta ce da gaɓɓan mutum suke cin juna daga gareta.
Fa’idoji
- Wajabcin tawakkali ga Allah da dogaro gareShi, da aikata sabubban da aka shara'anta.
- Wajabcin imani da hukuncin Allah da ƙaddararSa, kuma sabubba suna hannun Allah, Shi ne wanda Yake gudanar da su ko yake zare tasirinsu.
- Bata abinda sashin mutane suke aikatawa na canfi da launuka, kamar baƙaƙe da jajaye, ko sashin lambobi da sunaye da mutane da masu larura.
- Akan hani daga kusantar kuturu da makamancinsa masu cututtuka da suke yaɗuwa (da izinin Allah): Hakan yana daga sabubban da Allah Ya gudanar da al'ada cewa su suna kaiwa zuwa ga abinda ya sabbabasu; sabubba ba sa tsayuwa da kansu, kadai Allah Shi ne wanda idan Ya so zai zaresu ba za su tasirantar da komai ba, idan kuma Ya so sai Ya wanzar da su sai su yi tasiri.
Madogara
صحيح البخاري (7/ 126) (5707).
صحيح مسلم (4/ 1742) (2220).
فتح المجيد شرح كتاب التوحيد، لعبد الرحمن التميمي (ص307).
القول المفيد على كتاب التوحيد، لابن عثيمين (1/ 565).
الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص228).
الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص253).
التمهيد لشرح كتاب التوحيد، لصالح آل الشيخ (ص77).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عَمْرُو بن تَغْلِبَ ـ رضي الله عنه ـ أن رسول الله صلى الله عليه وسلم أُتِيَ بمالٍ أو سَبْيٍ فَقَسَّمه، فأعطى رجالا، وترك رجالًا، فبَلغَه أن الَّذِين تَرَك عَتَبُوا، فحمد الله، ثم أثنى عليه، ثم قال: «أما بعد، فوالله إني لأُعطي الرجل وأدَعُ الرجلَ، والذي أدعُ أحبُّ إلي من الذي أُعطي، ولكني إنما أُعطي أقوامًا لما أرى في قلوبهم من الجَزَع والهَلَع، وَأَكِلُ أقواما إلى ما جَعَلَ الله في قُلُوبِهم من الغِنَى والخَيْر، منهم عَمْرُو بن تَغْلِبَ» قال عمرو بن تغلب: فوالله ما أُحبُّ أن لي بكلمة رسول الله صلى الله عليه وسلم حُمْرَ النَّعَم.
A kan Amr bn Thalib - yardar Allah ta tabbata a gare shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kawo kudi ko kamammu ya raba su.Ya ba maza ya bar maza. Na rantse da Allah na bawa mutumin kuma na gayyaci mutumin, kuma wanda na kira yafi soyuwa akan wanda aka bashi. Abin da nake so shi ne cewa da maganar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ina da jan wardi.
Buhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
كنوز رياض الصالحين، تأليف: حمد بن ناصر العمار، الناشر: دار كنوز أشبيليا، الطبعة الأولى: 1430 هـ
بهجة الناظرين، تأليف: سليم بن عيد الهلالي، نسخة الكترونية، لا يوجد بها بيانات نشر
نزهة المتقين، تأليف: جمعٌ من المشايخ، الناشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة الأولى: 1397 هـ الطبعة الرابعة عشرة 1407 هـ
صحيح البخاري، تأليف: محمد بن إسماعيل البخاري، تحقيق: محمد زهير الناصر، الناشر: دار طوق النجاة الطبعة: الأولى، 1422هـ
رياض الصالحين، تأليف: محيي الدين يحيى بن شرف النووي ، تحقيق: د. ماهر بن ياسين الفحل، الطبعة: الأولى، 1428 هـ
منار القاري، تأليف: حمزة محمد قاسم ، الناشر: مكتبة دار البيان، عام النشر: 1410 هـ
المنهاج شرح صحيح مسلم بن الحجاج، تأليف: محيي الدين يحيى النووي، الناشر: دار إحياء التراث العربي، الطبعة: الثانية 1392 هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن ابن عباس رضي الله عنهما مرفوعاً: «عَيْنَانِ لاَ تَمسُّهُمَا النَّار: عَيْنٌ بَكَتْ من خَشْيَة الله، وعَيْنٌ بَاتَت تَحْرُسُ في سَبِيل الله».
A kan Ibn Abbas - Allah ya yarda da shi - tare da dagawa: "Idanun da wuta ba za ta iya taba su ba: ido mai kuka saboda tsoron Allah, da kuma ido mai kiyaye hanyar Allah."
Al-Tirmithi Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Ma'anar hadisin: Wuta ba ta taba ido mai kuka saboda tsoron Allah Madaukaki, yayin da mutum ya tuna girman Allah da ikonsa na bautar da bayinsa da tuna halin da yake ciki da kuma gazawarsa cikin gaskiyar Allah Madaukaki. Yana kuka da begen rahamar sa da kuma tsoron azabarsa da fushin sa, saboda wannan anyi alkawarin samun kubuta daga wuta. Da kuma wani ido wanda wuta bata taba shi ba, wanda shine: Duk wanda ya kiyaye saboda Allah Madaukakin Sarki a bude da wuraren fada domin kiyaye rayukan musulmai. Da kuma fadinsa: "Wuta ba ta taba su ba." Wannan daga furucin sashi ne da nufin duka, kuma abin da ake nufi shi ne cewa duk wanda ya yi kuka saboda tsoron Allah Madaukaki da wanda ya kiyaye a tafarkin Allah, Allah Madaukaki ya hana jikinsu zuwa wuta.
Madogara
- رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين؛ للإمام أبي زكريا النووي، تحقيق د. ماهر الفحل، دار ابن كثير-دمشق، الطبعة الأولى، 1428ه .
- بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين؛ تأليف سليم الهلالي، دار ابن الجوزي- الطبعة الأولى1418ه
- نزهة المتقين شرح رياض الصالحين؛ تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة-بيروت، الطبعة الرابعة عشر، 1407هـ.
سنن الترمذي، لمحمد بن عيسى الترمذي، تحقيق وتعليق: أحمد محمد شاكر ومحمد فؤاد عبد الباقي وإبراهيم عطوة عوض -شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي الحلبي - مصر
الطبعة: الثانية، 1395 هـ - 1975 م
مشكاة المصابيح، لمحمد بن عبد الله الخطيب العمري أبو عبد الله ولي الدين التبريزي، المحقق: محمد ناصر الدين الألباني المكتب الإسلامي – بيروت- الطبعة: الثالثة، 1985.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com