Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa dukkanin ayyuka ababen izina ne da niyya, wannan hukuncin mai gamewa ne a cikin dukkanin ayyuka na ibadu da mu'amaloli, wanda ya yi nufin wani abin amfani da aikinsa ba zai samu komai ba sai wannan abin amfanin, kuma babu sakamako gareshi, wanda yayi nufin neman kusanci da aikinsa zuwa ga Allah - madaukakin sarki zai samu sakamako da lada daga aikinsa ko da aikin ya kasance na al'ada ne, kamar ci da sha. Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya buga misali don bayanin tasirin niyya a ayyuka tare da daidaituwarsu a sura ta zahiri, sai ya bayyana cewa wanda ya yi nufin neman yardar Ubangigjinsa da hijirarsa, to, hijirarsa hijira ce ta shari'a abar karɓa za a yi masa sakayya a kanta don gaskiyar niyyarsa, wanda ya yi nufin wani abin amfani na duniya na dukiya, ko kasuwanci, ko mata da hijirarsa ba zai samu komai daga hijirarsa ba sai wancan abin amfanin da ya yi niyyarsu, kuma ba zai samu lada da sakamako ba.
- Kwaɗaitarwa a kan ikhlasi, domin Allah ba Ya karɓar aiki sai abin da aka nufi zatinsa da shi.
- Ayyukan da ake neman kusancin Allah - Mai girma da ɗaukaka - da su idan mukallafi ya aikata su a kan tafarkin al'ada, to, ba shi da wani lada a kansu, har sai ya yi nufin neman kusancin Allah da su.
- Niyya da ita ne ake banbancewa tsakaknin ibadu sashinsu da sashi, kuma (da itane ake banbancewa tsakanin) ibadu da al'adu.
صحيح البخاري (9/ 22) (6953)، (1/ 6) (1). صحيح مسلم (3/ 1515) (1907). التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية (ص5). شرح الأربعين النووية، لابن عثيمين (ص5). فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين، للعباد (ص8). شرح النووي على مسلم (13/ 54). تاج العروس من جواهر القاموس، للزبيدي (7/ 196).