Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Allah ba Ya duba zuwa surorinku da dukiyoyinku, sai dai Yana duba zuwa zukatanku da ayyukanku

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «إِنَّ اللهَ لَا يَنْظُرُ إِلَى صُوَرِكُمْ وَأَمْوَالِكُمْ، وَلَكِنْ يَنْظُرُ إِلَى قُلُوبِكُمْ وَأَعْمَالِكُمْ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah ba Ya duba zuwa surorinku da dukiyoyinku, sai dai Yana duba zuwa zukatanku da ayyukanku".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa Allah - Tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka - ba Ya duba zuwa surorin bayi da jikkunasu, shin su kyawawa ne ko munana ne? shin su manya ne ko kananu ne? lafiyayyu ne ko marasa lafiya ne? Kuma ba Ya duba zuwa dukiyoyinsu, shin masu yawa ne ko kaɗan ne? Allah - Mai girma da daukaka - ba Ya kama bayinsa kuma ba Ya yi musu hisabi a kan waɗannan al'amuran da fifikon da ya ke cikinsu, sai dai Yana duba zuwa zukatansu da abin da ke cikinsu na tsoron Allah da sakankancewa, da gaskiya da ikhlasi, ko nufin riya da jiyarwa, yana duba zuwa ayyukansu ta bangaren gyaransu da ɓacinsu; sai Ya bayar da lada, kuma Ya yi sakayya a kansu.

Fa’idoji
  1. Kulawa da gyara zuciya, da tsarkaketa daga dukkanin wata siffa abar zargi.
  2. Gyaran zuciya ta hanyar ikhlasi ne, gyaran aiki kuma ta hanyar bin Annabi ne - tsira da aminci su tabbata a gare shi -, su ne abin dubawa da lura a wurin Allah - Maɗaukakin sarki -.
  3. Kada mutum ya ruɗu da dukiyarsa ko kyawunsa ko jikinsa ko wani abu daga abubuwan wannan duniyar.
  4. Gargaɗi daga karkata zuwa zahiri ba tare da gyara baɗini ba.
Madogara

صحيح مسلم (2564) (4/ 1986). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 40). تطريز رياض الصالحين، لفيصل المبارك (ص14). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 25).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
Kaɗaita Allah cikin sunayenSa da siffofinSa

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com