Daga Sahl ɗan Hunaif - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya roki Allah shahada da gaskiya, Allah Zai kai shi matsayin shahidai, koda ya mutu akan shinfiɗarsa".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda ya nemi shahada da mutuwa a tafarkin Allah, kuma ya kasance mai gaskiya mai tsarkake niyyarsa ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -, Allah Zai ba shi darajojin shahidai saboda niyyarsa ta gaskiya koda ya mutu akan shinfiɗa ba a yaki ba.
Fa’idoji
Gaskiyar niyya tare da aikata abin da za'a iya, sababi ne na samun abin nufi na lada da sakamako, koda bai yi aikin da ake nema ba.
Kwaɗaitarwa akan jihadi da neman shahada a tafarkin Allah - Mai girma da ɗaukaka -.
Baiwar Allah - Mai girma da ɗaukaka - ga wannan al'ummar, shi (Allah) yana bada mafi ɗaukakar darajoji a cikin aljanna da kankanin aiki.
Madogara
صحيح مسلم (3/ 1517) (1909).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 123).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 87).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com