Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Wanda ya sallaci sanyaya biyu zai shiga aljanna

عن أَبِي مُوسَى الأَشْعَرِيِّ رضي الله عنه: أَنَّ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم قَالَ: «مَنْ صَلَّى ‌الْبَرْدَيْنِ دَخَلَ الْجَنَّةَ»
Daga Abu Musa al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya sallaci sanyaya biyu zai shiga aljanna".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zaburar da kwaɗaitarwa akan sallar sanyaya biyu ; su ne sallar asuba da la'asar, kuma Ya yi wa wanda ya yi su da haƙƙinsu na lokaci da jama'a da wanin haka albishir cewa sun zama sababi na shigarsa aljanna.

Fa’idoji
  1. Falalar kulawa akan sallar asuba da la'asar; domin asuba tana kasancewa ne a lokacin daɗin bacci, la'asar kuma tana kasancewa ne lokacin shagaltuwar mutum da aikinsa, wanda ya kiyayesu ya kasance mafi cancanta ya kiyaye ragowar salloli.
  2. An ambaci sallar asuba da la'asar da sanyaya biyu; domin sallar asuba a cikinta akwai sanyin dare, sallar la'asar kuma a cikinta akwai sanyin rana, koda sun kasance a lokaci na zafin rana, saidai wannan lokacin ya fi saukin (zafi) kafin wannan lokacin, ko kuma ambatansu ya zama ta babin rinjayarwa kamar yadda ake cewa: Watanni biyu ga rana da wata.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 119) (574). صحيح مسلم (1/ 440) (635). نزهة المتقين، لمجموعة من الباحثين (1/ 159). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 187).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALAR SALLAH

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com