Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Na yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi caffa - akan shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu Manzon Allah ne, da tsaida sallah, da bada zakka, da ji da bi, da nasiha ga kowanne musulmi

عَنْ جَرِيرِِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ رضي الله عنه قَالَ: بَايَعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلَى شَهَادَةِ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ، وَإِقَامِ الصَّلاَةِ، وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ، وَالسَّمْعِ وَالطَّاعَةِ، وَالنُّصْحِ لِكُلِّ مُسْلِمٍ.
Daga Jariri Dan Abadullahi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi caffa - akan shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu Manzon Allah ne, da tsaida sallah, da bada zakka, da ji da bi, da nasiha ga kowanne musulmi.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Sahabi Jariru Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa shi ya dorawa kansa ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alkawari akan tauhidi, da yin salloli biyar a yini da dare, da sharuddansu da rukunansu da wajibansu da sunnoninsu, da kuma bada zakka ta dole, ita ce ibada ta dukiya wajiba, ana karba daga mawadata ana bada ita ga macancanta daga talakawa da wasunsu, da kuma biyayya ga shugabanni, da nasiha ga kowanne musulmi, hakan ta hanyar kwadayi akan amfanar da shi, da sadar da alheri gare shi, da tunkude sharri daga gare shi ta hanyar magana da aikatawa.

Fa’idoji
  1. Muhimmancin sallah da zakka, su biyun suna daga rukunan Musulunci.
  2. Muhimmancin nasiha da yin nasiha tsakanin musulmai, har Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa sahabbai - Allah Ya yarda dasu - caffa akanta.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 111) (524)، (3/ 72) (2157). صحيح مسلم (1/ 75) (56). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 272). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص145). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 398). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 206).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALAR SALLAH

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com