Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

SAKAKKUN ZIKIRAI

Hadisai 7

Mafificin zikiri: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma mafificiyar addu'a: Godiya ta tabbata ga Allah

عن جابر رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «أَفْضَلُ الذِّكْرِ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَأَفْضَلُ الدُّعَاءِ: الْحَمْدُ لِلهِ».
Daga Jabir -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Naji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: "Mafificin zikiri: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma mafificiyar addu'a: Godiya ta tabbata ga Allah".
Tirmizi da Nasa'i a cikin Al-kubra da Ibnu Majah ne Suka rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi

Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana sanar da cewa mafificin zikiri: "La ilaha illal lahu" Ma'anarta babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma cewa mafificiyar addu'a godiya ta tabbata ga Allah; shi ne ikirari da cewa mai ni'imtarwa Shi ne Allah - tsarki ya tabbatar maSa -, wanda ya cancanci cikakkiyar siffa mai kyau.

Fa’idoji
  1. Kwadaitarwa ga yawaita ambaton Allah da kalmar Tauhidi, da addu'a da godiya.
Madogara

سنن الترمذي (5/ 393) (3383). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخِن وغيره (2/ 984). زاد المعاد في هدي خير العباد، ابن قيم الجوزية (1/ 36).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Mafi soyuwar zance ga Allah huɗu ne: Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne mafi girma, da kowanne ka fara daga cikinsu ba ya cutar da kai

عن سَمُرَة بن جندبٍ رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «أَحَبُّ الْكَلَامِ إِلَى اللهِ أَرْبَعٌ: سُبْحَانَ اللهِ، وَالْحَمْدُ لِلهِ، وَلَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَاللهُ أَكْبَرُ، لَا يَضُرُّكَ بِأَيِّهِنَّ بَدَأْتَ».
Daga Samura ɗan Jundub - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gagreshi - ya ce: "Mafi soyuwar zance ga Allah huɗu ne: Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne mafi girma, da kowanne ka fara daga cikinsu ba ya cutar da kai".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa mafi soyuwar zance a wurin Allah huɗu ne: Tsarki ya tabbata ga Allah; Tana nufin tsarkake Allah - Maɗaukakin sarki - daga kowace tawaya. Godiya ta tabbata ga Allah: Siffanta Allah ne da cikakkiyar cika tare da soyayyarSa da girmamashi. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah: Wato; Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Allah ne mafi girma: Wato; Mafi girma kuma Mafi buwaya daga dukkan komai. Kuma cewa falalarta da samun ladanta ba ya nufin sai lallai an jeranta su a yayin furuci da su.

Fa’idoji
  1. Sauƙin shari'a, ta inda ba ya cutarwa da kowaccen waɗannan kalmomin ka fara.
Madogara

صحيح مسلم (3/ 1685) (2137)، (4/ 2093) (2731)، (4/ 2072) (2695). توضيح الأحكام من بلوغ المرام، للبسام (7/ 540). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 411). فتح ذي الجلال والإكرام، لابن عثيمين (6/ 477). سبل السلام بشرح بلوغ المرام، للصنعاني (2/ 706).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Sauran mutanen kirki babu abin bauta sai Allah kuma tsarki ya tabbata ga Allah, Allah ya fi girma kuma godiya ta tabbata ga Allah kuma babu wani karfi a kusa kuma babu wani karfi sai Allah

عن أبي سعيد الخدري رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : "الْبَاقِيَاتُ الصَّالِحَاتُ، لَا إلَهَ إلَّا اللَّهُ، وَسُبْحَانَ اللَّهِ، وَاَللَّهُ أَكْبَرُ، وَالْحَمْدُ لِلَّهِ، وَلَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إلَّا بِاَللَّهِ".
Daga Abu Sa`id al-Khudri, yardar Allah ta tabbata a gare shi, wanda ya ce: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Ragowar na kirki ne, babu wani Allah sai Allah, tsarki ya tabbata ga Allah, kuma Allah ya fi girma, kuma Allah ya fi girma”
Ibnu Hibban ne ya Rawaito shi - Al-Hakim Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne a baki dayan Riwayoyin sa
Sharhi

A cikin wannan hadisin akwai shaidar cancantar wannan ambaton a cikin wannan sigar, domin kuwa ya qunshi ma’anonin yabo, tsarkakewa da tasbihi ga Allah mai girma da daukaka, kuma saboda yabon Allah ga ayyukansa. Samun alheri, sai dai tare da Allah Madaukaki. Waɗannan kalmomi tare da waɗannan ma'anoni masu girma sune abin da ya rage na mumini da fa'idar shi bayan mutuwarsa.

Madogara

الإحسان في تقريب صحيح ابن حبان، لمحمد بن حبان بن أحمد بن حبان بن معاذ، التميمي، أبو حاتم، الدارمي، البُستي، ترتيب: الأمير علاء الدين علي بن بلبان الفارسي، حققه وخرج أحاديثه وعلق عليه: شعيب الأرنؤوط، ط مؤسسة الرسالة، بيروت. المستدرك على الصحيحين، لأبي عبد الله الحاكم محمد بن عبد الله بن محمد بن حمدويه النيسابوري المعروف بابن البيع، تحقيق: مصطفى عبد القادر عطا، ط دار الكتب العلمية – بيروت. السنن الكبرى، لأبي عبد الرحمن أحمد بن شعيب بن علي الخراساني، النسائي، تحقق: حسن عبد المنعم شلبي، ط مؤسسة الرسالة – بيروت. سلسلة الأحاديث الصحيحة وشيء من فقهها وفوائدها، لأبي عبد الرحمن محمد ناصر الدين، بن الحاج نوح بن نجاتي بن آدم الألباني، ط مكتبة المعارف للنشر والتوزيع، الرياض. توضيح الأحكام من بلوغ المرام، الشيخ عبد الله بن عبد الرحمن البسام، ط مكتبة الأسد الإسلامية، الطبعة الخامسة. منحة العلام في شرح بلوغ المرام، الشيخ عبد الله بن صالح الفوزان، ط دار ابن الجوزي، الطبعة الأولى. تسهيل الإلمام بفقه الأحاديث من بلوغ المرام، الشيخ صالح الفوزان بن عبد الله الفوزان، اعتنى بها عبد السلام بن عبد الله السليمان، الطبعة الأولى. فتح ذي الجلال والإكرام، الشيخ محمد بن صالح العثيمين، ط المكتبة الإسلامية، الطبعة الأولى. سبل السلام بشرح بلوغ المرام، للإمام محمد بن إسماعيل الصنعاني، ط دار الحديث.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kalmomi guda biyu masu sauƙi a harshe, masu nauyi a ma'auni, masu soyuwa ga Ubangiji Al-Rahman

عن أبي هريرة رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «كَلِمَتَانِ خَفِيفَتَانِ عَلَى اللِّسَانِ، ثَقِيلَتَانِ فِي الْمِيزَانِ، حَبِيبَتَانِ إِلَى الرَّحْمَنِ: سُبْحَانَ اللهِ الْعَظِيمِ، سُبْحَانَ اللهِ وَبِحَمْدِهِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Kalmomi guda biyu masu sauƙi a harshe, masu nauyi a ma'auni, masu soyuwa ga Ubangiji Al-Rahman: Tsarki ya tabbata ga Allah Mai girma, tsarki ya tabbata ga Allah da godiya a gareshi".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ba da labari game da kalmomi biyu da mutum zai furta su ba tare da wahala ba, kuma akowane hali, kuma ladansu mai girma ne a ma'auni, kuma Ubangijimmu Al-Rahman - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka - Yana sonsu: Tsarki ya tabbata ga Allah Mai girma, tsarki ya tabbata ga Allah da godiya a gareshi; saboda abin da suka ƙunsa na siffanta Allah da girma da cika, da tsarkakeshi daga tawaya - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka -.

Fa’idoji
  1. Mafi girman zikiri shi ne a haɗa tsakanin tsarkakeshi da yabo gareshi a cikinsa.
  2. Bayanin yalwar rahamar Allah ga bayinsa, Yana sakayya da gwaggwaɓan lada a kan aiki kaɗan.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 86) (6406). صحيح مسلم (4/ 2072) (2694). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 480). فتح ذي الجلال والإكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (6/ 519).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Wasu mutane basu zauna a wani wurin zama ba basu ambaci Allah a cikinsa ba kuma ba su yi salati ga Annabinsu ba sai hasara ta kasance a kansu, idan (Allah) Ya so Ya azabtar da su idan kuma Ya so Ya gafarta musu

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَا جَلَسَ قَوْمٌ مَجْلِسًا لَمْ يَذْكُرُوا اللَّهَ فِيهِ وَلَمْ يُصَلُّوا عَلَى نَبِيِّهِمْ إِلاَّ كَانَ عَلَيْهِمْ تِرَةً، فَإِنْ شَاءَ عَذَّبَهُمْ وَإِنْ شَاءَ غَفَرَ لَهُمْ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wasu mutane basu zauna a wani wurin zama ba basu ambaci Allah a cikinsa ba kuma ba su yi salati ga Annabinsu ba sai hasara ta kasance a kansu, idan (Allah) Ya so Ya azabtar da su idan kuma Ya so Ya gafarta musu".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shi a cikin AlkubraDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗar daga rafkana daga ambatan Allah, kuma cewa wasu mutane basu zauna a wani wurin zama ba kuma basu ambaci Allah - Maɗaukakin sarki - a cikinsa ba, kuma ba su yi salati ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba sai wannan mazaunin ya zama hasara a kansu da nadama da taɓewa da tawaya a ranar alƙiyama, idan Ya so Ya azabtar da su saboda zunubinsu da ya gabata da kuma kasawarsu mai zuwa, idan kuma Ya so Ya gafarta musu dan falala da rahama daga gare shi.

Fa’idoji
  1. Kwaɗaitarwa akan zikiri da kuma falalarsa.
  2. Falalar wuraran zama da a cikinsu akwai ambatan Allah - Maɗaukakin sarki -, da ambatan ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma cewa majalisan da a cikinsu babu hakan to sune majalisan zargi ga ma'abotansu a ranar alƙiyama.
  3. Abinda aka ambata na gargaɗi daga rafkana daga ambatan Allah ba mai taƙaituwa ba ne akan wuraren zama kawai ba, kai yana game wasunsu, alNawawi ya ce: An karhanta ga wanda ya zauna a wani wuri ya bar wurin ba tare da ya ambaci Allah - Maɗaukakin sarki - a cikinsa.
  4. Hasara mai faruwa ce garesu a ranar Alkiyama: Ko dai da kufcewar lada da sakamako saboda rashin fa'idantuwa daga lokaci a cikin biyayya ga Allah, kodai da zunubi da uƙuba saboda shagaltuwar lokacin a saɓon Allah.
  5. Wannan gargaɗin idan wannan rafkanar da abubuwan da aka halatta ne, to ta yaya da wuraren zaman da aka haramta waɗanda a cikinsu akwai giba da annamimanci da wasunsu?!
Madogara

سنن أبي داود (7/ 221) (4855). سنن الترمذي (5/ 391) (3380). السنن الكبرى للنسائي (9/ 155) (10163). توضيح الأحكام من بلوغ المرام، لعبد الله البسام (7/ 524). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 396). فتح ذي الجلال والإكرام، لابن عثيمين (6/ 464).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

In ce: Tsarki ya tabbata ga Allah, Godiya ta tabbata ga Allah, Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, Allah ne mafi girma. Fadin haka ya fi min duk abin da rana ta fito a kansa

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «لَأَنْ أَقُولَ: سُبْحَانَ اللهِ، وَالْحَمْدُ لِلهِ، وَلَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَاللهُ أَكْبَرُ، أَحَبُّ إِلَيَّ مِمَّا طَلَعَتْ عَلَيْهِ الشَّمْسُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: In ce: Tsarki ya tabbata ga Allah, Godiya ta tabbata ga Allah, Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, Allah ne mafi girma. Fadin haka ya fi min duk abin da rana ta fito a kansa.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labari cewa anbaton Allah (Zikiri) da waɗannan kalmomi masu girma, shi ya fi duniya da abin da yake cikinta, su ne: "Tsarki ya tabbata ga Allah": Tsarke Allah ne daga dukkan tawaya. "Godiya ta tabbata ga Allah": Yabon Allah ne da siffofinSa na Kamala tare da sonSa da kuma girmamaShi. "Babu abin bautawa sai Allah": Wato babu abin bauta da gaskiya sai Allah. Allah ne mafi girma; Mafi girma da ɗaukaka a kan komai.

Fa’idoji
  1. Kwaɗaitarwa a kan anbaton Allah. Kuma Shi ne mafi soyuwa sama da duk wani abu da rana ta fito a kansa.
  2. Zaburarwa a kan yawaita anbaton Allah, saboda ladan da yake da shi da kuma falala.
  3. Jin daɗin duniya kaɗan ne, kuma sha’awar da ke cikinta mai gushewa ce
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2072) (2695). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 496). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 485). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخِن وغيره (2/ 970). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل المبارك (ص772).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayinAddini, kuma da Muhammad a matsayin Manzo, Aljanna ta wajaba a gare shi

عَن أَبي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنْ قَالَ: رَضِيتُ بِاللَّهِ رَبًّا، وَبِالْإِسْلَامِ دِينًا، وَبِمُحَمَّدٍ رَسُولًا، وَجَبَتْ لَهُ الْجَنَّةُ».
Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayinAddini, kuma da Muhammad a matsayin Manzo, Aljanna ta wajaba a gare shi».
Abu Dawud ne Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya ce: (Na yarda da Allah a matsayin Ubangiji) kuma abin bautawa da gaskiya mai reno kuma mamallaki shugaba kuma mai gyarawa. (Da Musulunci) da dukkanin hukunce-hukuncensa na umarni da hani (Addini) kuma tafarki da shari'a da miƙa wuya. (Da Annabi Muhammad a matsayin manzo) da Annabi; da dukkanin abinda aka aiko shi da shi kuma ya isar da shi garemu, sai aljanna ta wajaba gare shi.

Fa’idoji
  1. Kwaɗaitarwa a kan faɗar wannan addu'ar, da bayanin ladan da ya jerantu a kanta.
  2. Yarda da Allah a matsayin Ubangiji ta ƙunshi kada mutum ya bautawa waninSa - tsarki ya tabbatar maSa -.
  3. Yarda da (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a matsayin Annabi da Manzo ya ƙunshi yi masa biyayya - aminci ya tabbata agare shi - da jawuwa ga sunnarsa.
  4. Yarda da Musulunci a matsayin Addini shi ne yarda da abinda Allah Ya zaɓe shi ga bayinSa.
  5. An so faɗin wannan addu'ar a yayin shahada biyu daga jin kiran sallah kamar yanda yake a cikin wasu riwayoyin daban.
  6. Kuma ya zo a cikin wani hadisin daban cewa an so wannan addu'ar a safiya da maraice.
Madogara

سنن أبي داود (2/ 635) (1529). شرح أبي داود للعيني (5/ 439). شرح سنن أبي داود لابن رسلان (7/ 348). المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (3/ 710).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com