Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ba da labari game da kalmomi biyu da mutum zai furta su ba tare da wahala ba, kuma akowane hali, kuma ladansu mai girma ne a ma'auni, kuma Ubangijimmu Al-Rahman - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka - Yana sonsu: Tsarki ya tabbata ga Allah Mai girma, tsarki ya tabbata ga Allah da godiya a gareshi; saboda abin da suka ƙunsa na siffanta Allah da girma da cika, da tsarkakeshi daga tawaya - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka -.
- Mafi girman zikiri shi ne a haɗa tsakanin tsarkakeshi da yabo gareshi a cikinsa.
- Bayanin yalwar rahamar Allah ga bayinsa, Yana sakayya da gwaggwaɓan lada a kan aiki kaɗan.
صحيح البخاري (8/ 86) (6406). صحيح مسلم (4/ 2072) (2694). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 480). فتح ذي الجلال والإكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (6/ 519).