Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Wasu mutane basu zauna a wani wurin zama ba basu ambaci Allah a cikinsa ba kuma ba su yi salati ga Annabinsu ba sai hasara ta kasance a kansu, idan (Allah) Ya so Ya azabtar da su idan kuma Ya so Ya gafarta musu

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَا جَلَسَ قَوْمٌ مَجْلِسًا لَمْ يَذْكُرُوا اللَّهَ فِيهِ وَلَمْ يُصَلُّوا عَلَى نَبِيِّهِمْ إِلاَّ كَانَ عَلَيْهِمْ تِرَةً، فَإِنْ شَاءَ عَذَّبَهُمْ وَإِنْ شَاءَ غَفَرَ لَهُمْ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wasu mutane basu zauna a wani wurin zama ba basu ambaci Allah a cikinsa ba kuma ba su yi salati ga Annabinsu ba sai hasara ta kasance a kansu, idan (Allah) Ya so Ya azabtar da su idan kuma Ya so Ya gafarta musu".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shi a cikin AlkubraDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗar daga rafkana daga ambatan Allah, kuma cewa wasu mutane basu zauna a wani wurin zama ba kuma basu ambaci Allah - Maɗaukakin sarki - a cikinsa ba, kuma ba su yi salati ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba sai wannan mazaunin ya zama hasara a kansu da nadama da taɓewa da tawaya a ranar alƙiyama, idan Ya so Ya azabtar da su saboda zunubinsu da ya gabata da kuma kasawarsu mai zuwa, idan kuma Ya so Ya gafarta musu dan falala da rahama daga gare shi.

Fa’idoji
  1. Kwaɗaitarwa akan zikiri da kuma falalarsa.
  2. Falalar wuraran zama da a cikinsu akwai ambatan Allah - Maɗaukakin sarki -, da ambatan ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma cewa majalisan da a cikinsu babu hakan to sune majalisan zargi ga ma'abotansu a ranar alƙiyama.
  3. Abinda aka ambata na gargaɗi daga rafkana daga ambatan Allah ba mai taƙaituwa ba ne akan wuraren zama kawai ba, kai yana game wasunsu, alNawawi ya ce: An karhanta ga wanda ya zauna a wani wuri ya bar wurin ba tare da ya ambaci Allah - Maɗaukakin sarki - a cikinsa.
  4. Hasara mai faruwa ce garesu a ranar Alkiyama: Ko dai da kufcewar lada da sakamako saboda rashin fa'idantuwa daga lokaci a cikin biyayya ga Allah, kodai da zunubi da uƙuba saboda shagaltuwar lokacin a saɓon Allah.
  5. Wannan gargaɗin idan wannan rafkanar da abubuwan da aka halatta ne, to ta yaya da wuraren zaman da aka haramta waɗanda a cikinsu akwai giba da annamimanci da wasunsu?!
Madogara

سنن أبي داود (7/ 221) (4855). سنن الترمذي (5/ 391) (3380). السنن الكبرى للنسائي (9/ 155) (10163). توضيح الأحكام من بلوغ المرام، لعبد الله البسام (7/ 524). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 396). فتح ذي الجلال والإكرام، لابن عثيمين (6/ 464).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SAKAKKUN ZIKIRAI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com