Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

In ce: Tsarki ya tabbata ga Allah, Godiya ta tabbata ga Allah, Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, Allah ne mafi girma. Fadin haka ya fi min duk abin da rana ta fito a kansa

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «لَأَنْ أَقُولَ: سُبْحَانَ اللهِ، وَالْحَمْدُ لِلهِ، وَلَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَاللهُ أَكْبَرُ، أَحَبُّ إِلَيَّ مِمَّا طَلَعَتْ عَلَيْهِ الشَّمْسُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: In ce: Tsarki ya tabbata ga Allah, Godiya ta tabbata ga Allah, Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, Allah ne mafi girma. Fadin haka ya fi min duk abin da rana ta fito a kansa.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labari cewa anbaton Allah (Zikiri) da waɗannan kalmomi masu girma, shi ya fi duniya da abin da yake cikinta, su ne: "Tsarki ya tabbata ga Allah": Tsarke Allah ne daga dukkan tawaya. "Godiya ta tabbata ga Allah": Yabon Allah ne da siffofinSa na Kamala tare da sonSa da kuma girmamaShi. "Babu abin bautawa sai Allah": Wato babu abin bauta da gaskiya sai Allah. Allah ne mafi girma; Mafi girma da ɗaukaka a kan komai.

Fa’idoji
  1. Kwaɗaitarwa a kan anbaton Allah. Kuma Shi ne mafi soyuwa sama da duk wani abu da rana ta fito a kansa.
  2. Zaburarwa a kan yawaita anbaton Allah, saboda ladan da yake da shi da kuma falala.
  3. Jin daɗin duniya kaɗan ne, kuma sha’awar da ke cikinta mai gushewa ce
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2072) (2695). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 496). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 485). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخِن وغيره (2/ 970). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل المبارك (ص772).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SAKAKKUN ZIKIRAI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com