Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayinAddini, kuma da Muhammad a matsayin Manzo, Aljanna ta wajaba a gare shi».
Abu Dawud ne Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya ce: (Na yarda da Allah a matsayin Ubangiji) kuma abin bautawa da gaskiya mai reno kuma mamallaki shugaba kuma mai gyarawa.
(Da Musulunci) da dukkanin hukunce-hukuncensa na umarni da hani (Addini) kuma tafarki da shari'a da miƙa wuya.
(Da Annabi Muhammad a matsayin manzo) da Annabi; da dukkanin abinda aka aiko shi da shi kuma ya isar da shi garemu, sai aljanna ta wajaba gare shi.
Fa’idoji
Kwaɗaitarwa a kan faɗar wannan addu'ar, da bayanin ladan da ya jerantu a kanta.
Yarda da Allah a matsayin Ubangiji ta ƙunshi kada mutum ya bautawa waninSa - tsarki ya tabbatar maSa -.
Yarda da (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a matsayin Annabi da Manzo ya ƙunshi yi masa biyayya - aminci ya tabbata agare shi - da jawuwa ga sunnarsa.
Yarda da Musulunci a matsayin Addini shi ne yarda da abinda Allah Ya zaɓe shi ga bayinSa.
An so faɗin wannan addu'ar a yayin shahada biyu daga jin kiran sallah kamar yanda yake a cikin wasu riwayoyin daban.
Kuma ya zo a cikin wani hadisin daban cewa an so wannan addu'ar a safiya da maraice.
Madogara
سنن أبي داود (2/ 635) (1529).
شرح أبي داود للعيني (5/ 439).
شرح سنن أبي داود لابن رسلان (7/ 348).
المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (3/ 710).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com