عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللهِ رضي الله عنهما أَنَّهُ سَمِعَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «إِذَا دَخَلَ الرَّجُلُ بَيْتَهُ، فَذَكَرَ اللهَ عِنْدَ دُخُولِهِ وَعِنْدَ طَعَامِهِ، قَالَ الشَّيْطَانُ: لَا مَبِيتَ لَكُمْ، وَلَا عَشَاءَ، وَإِذَا دَخَلَ، فَلَمْ يَذْكُرِ اللهَ عِنْدَ دُخُولِهِ، قَالَ الشَّيْطَانُ: أَدْرَكْتُمُ الْمَبِيتَ، وَإِذَا لَمْ يَذْكُرِ اللهَ عِنْدَ طَعَامِهِ، قَالَ: أَدْرَكْتُمُ الْمَبِيتَ وَالْعَشَاءَ».
Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Idan mutum zai shiga gidansa, sai ya ambaci sunan Allah a yayin shigarsa da lokacin cin abincin sa , Shaidan zai ce : Babu makwanci gareku, kuma babu abincin dare, idan zai shiga bai ambaci sunan Allah a yayin shigarsa ba, Shaidan zai ce: Kun sami makwanci, idan bai ambaci Allah a lokacin cin abincin sa ba, zai ce : Kun riski makwanci da abincin dare".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da ambatan Allah a yayin shiga gida da kafin cin abinci, kuma cewa shi idan ya ambaci Allah da fadinsa: (Da sunan Allah) a lokacin shigarsa da kuma lokacin fara abincinsa, Shaidan zai cewa mataimakansa: Baku da rabo na makwanci ko abincin dare a wannan gidan da mai shi ya kare kansa daga ku da ambatan Allah - Madaukakin sarki -. Amma idan zai shiga gidansa bai ambaci Allah a lokacin shigarsa ba ko lokacin cin abincinsa, sai Shaidan ya sanar da mataimaknsa cewa sun sami makwanci, da abincin dare a wannan gidan.
Fa’idoji
- An so ambatan Allah a lokacin shiga gida da lokacin cin abinci, domin Shaidan yana kwana a cikin gidaje, yana ci daga abincin mutanen gidan idan ba su ambaci sunan Allah - Madaukakin sarki ba -.
- Shaidan yana lura da Dan Adam a cikin aikinsa da jujjuyawarsa acikin al'amauransa gaba dayansu, idan ya rafkana daga zikiri zai samu abin nufinsa daga gare shi .
- Zikiri yana kore Shaidan.
- Kowanne Shaidan yana da mabiya da masoya suna albishir da maganarsa kuma suna bin umarninsa.
Madogara
صحيح مسلم (3/ 1598) (2018).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 50).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل المبارك (ص467).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (4/ 190).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 700).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «يَقُولُ اللهُ عَزَّ وَجَلَّ: أَنَا عِنْدَ ظَنِّ عَبْدِي، وَأَنَا مَعَهُ حِينَ يَذْكُرُنِي، فَإِنْ ذَكَرَنِي فِي نَفْسِهِ ذَكَرْتُهُ فِي نَفْسِي، وَإِنْ ذَكَرَنِي فِي مَلَإٍ ذَكَرْتُهُ فِي مَلَإٍ خَيْرٍ مِنْهُ، وَإِنِ اقْتَرَبَ إِلَيَّ شِبْرًا، تَقَرَّبْتُ إِلَيْهِ ذِرَاعًا، وَإِنِ اقْتَرَبَ إِلَيَّ ذِرَاعًا، اقْتَرَبْتُ إِلَيْهِ بَاعًا، وَإِنْ أَتَانِي يَمْشِي أَتَيْتُهُ هَرْوَلَةً».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah - Mai girma da ɗaukaka - Yana cewa: Ni ina inda zatan bawaNa yake, kuma Ni ina tare da shi lokacin da yake ambatona, idan ya ambaceNi a cikin ransa zan ambace shi a cikin raiNa, idan ya ambaceni a cikin mutane zan ambace shi a cikin mutanen da suka fisu alheri, idan ya kusantoNi taki (ɗaya), Zan kusanto zuwa gare shi zira'i (ɗaya), idan ya kusanto zuwa gareNi zira'i (ɗaya), zan kusanto gare shi faɗin hannaye, idan ya zo miNi yana tafiya zan zo masa ina gaggawa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Yana cewa:
Ni ina inda zatan bawaNa gareNi yake, zan yi mu'amala da bawaNa gwargwadan zatansa da Ni, hakan dan ƙauna da burin rangwami, kuma Ina yi masa abinda yake tinanin afkuwarsa daga gareNi na alheri ne ko wanin hakan; kuma Ni ina tare da shi da rahama da dacewa da shiriya da kiyayewa da ƙarfafawa idan ya anbaceNi.
Idan ya anbaceNi a cikin ransa shi kaɗai a kaɗaice da tasbihi da hailala ko waninsu; zan anbace shi a cikin raiNa.
Idan ya anbaceNi a cikin jama'a; zan ambace shi a cikin jama'ar da tafisu yawa kuma ta fisu tsarki.
Wanda ya nemi kusanci zuwa ga Allah gwargwadan taki Allah Zai yi masa ƙari sai Ya kusanto zuwa gare shi da zira'i.
Idan ya nemi kusanci zuwa gare shi gwargwadan zira'i zai kusanto zuwa gare shi gwargwadan awon faɗin hannaye.
Idan ya zo zuwa ga Allah yana tafiya to Allah zai zo masa Yana sassarfa.
Bawa idan ya nemi kusanci zuwa ga Ubangijinsa da biyayya gareShi da fuskantowa gareShi, to lallai Ubangiji - Maɗaukakin sarki - Zai ƙara kusanci zuwa gareshi dan sakamako daga jinsin aikinsa.
A duk lokacin da bautar mumini ta cika ga Ubangijinsa to Allah Maɗaukakin sarki zai kusanto zuwa gare shi, kyautar Allah da sakamakonSa (ita ce ) mafi yawa daga aikin bawa da kuma wahalarsa, a taƙaice cewa sakamakon Allah mai rinjaya ne akan aiki ta hanyar kaifiyya da kuma kimmiya.
Mumini yana kyautata zato, kuma yana aiki, yana gaggawa yana ƙarawa har ya gamu da Allah.
Fa’idoji
- Wannan hadisin yana daga abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake ruwaito shi daga Ubangijinsa, ana ambatonsa da Hadisi Ƙudsi, ko Ilahi, shi ne wanda lafazinsa da ma'anarsa daga Allah ne, sai dai cewa shi babu keɓance-keɓancen AlƘur’ani a cikinsa waɗanda ya keɓanta da su daga waninSa, kamar bauta da karanta shi, da yin tsarki sabo da shi da fito na fito(ƙalubalanta) da gajiyarwa, da sauransu.
- Al-Aajurri ya ce: Lallai ma'abota gaskiya suna siffanta Allah - Mai girma da ɗaukaka - da abinda Ya siffanta kanSa - Mai girma da ɗaukaka - da shi, da kuma abinda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya siffanta shi da shi, kuma da abinda sahabbai - Allah Ya yarda da su - suka siffantaShi da shi, wannan (ita ce) mazhabar malamai daga waɗanda ya bi bai yi ƙirƙire ba, Ya ƙare. Ahlus Sunna suna tabbatarwa Allah abinda Ya tabbatarwa kanSa da shi na sunaye da siffofi ba tare da jirkitawa ko korewa ko kaifantawa ko kamantawa ba, kuma suna korewa Allah abinda Ya korewa kanSa, sunayin shiru daga abinda korewa ko tabbatarwa bai zo da shi ba, Allah - madaukakin sarki - ya ce: {Babu wani abu tamkarSa, Shi ne Mai yawan ji kuma Mai yawan gani}.
- Kyautata zato ga Allah babu makawa daga aiki a tare da shi, al-Hasanul Basri ya ce: Lallai cewa mumini ya kyautata zato ga Ubangijinsa sai ya kyautata aiki, kuma lallai cewa fajiri ya munana zato ga Ubangijinsa sai ya munana aiki.
- Al-Ƙurɗubi ya ce: An ce: Ma'anar "Zaton bawaNa gareNi" Zaton amsawa a yayin addu'a, da kuma zatan karɓa a yayin tuba, da zatan gafara a yayin istigfari, da zatan sakayya a yayin aikin ibada da sharuɗɗanta dan riƙo da gaskiyar alƙawarinsa, saboda haka yana kamata ga mutum ya yi ƙoƙari a tsayuwa da abinda ke kansa yana mai sakankancewa da cewa Allah Zai karɓe shi kuma Ya gafarta maSa; domin cewa shi ya yi alƙawari da hakan kuma Shi baYa saɓa alƙawari, idan ya ƙudirce ko ya yi zaton cewa Allah ba Zai karɓeta ba ko kuma cewa ba zata anfane shi ba to wannan shi ne yanke ƙauna daga rahamar Allah, kuma hakan yana daga manyan laifuka, wanda ya mutu akan hakan za'a wakilta shi zuwa abinda ya yi zato kamar yadda yake cikin sashin hanyoyin hadisin da aka anbata; "To bawaNa ya yi zato Na da abinda ya so", ya ce: Amma zatan gafara tare da nacewa akan sabo to hakan shi ne tsantsar jahilci da ruɗuwa.
- Kwaɗaitarwa akan yawaita anbatan Allah a cikin ranka da harshenka gaba ɗaya, yana jin tsoron Allah a cikin ransa da zuciyarsa ya dinga tuna girmanSa da haƙƙinSa ya ƙaunace Shi ya girmamaShi ya so Shi ya kyautata masa zato ya tsarkake aiki, ya furta da harshe: Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne Mafi girma, babu wata dabara babu wani ƙarfi sai ga Allah.
- Ibnu Abi Jamrah ya ce: Wanda ya anbace shi alhali shi yana mai jin tsoro zai amintar da shi, ko mai kewa zai ɗebe masa kewa.
- Taki: (shi ne) faɗin dake tsakanin ƙaramin ɗan yatsa zuwa babban ɗan yatsa a yayin miƙe tafi. Zira'i kuwa: (shi ne) faɗin dake tsakanin gefen ɗan yatsa na tsakiya har zuwa ƙashin gwiwar hannu. Ba'i kuwa: (Shi ne) tsawon zira'i biyu na mutum da kuma damattsansa da faɗin ƙirjinsa; hakan (shi ne) gwargwadan zira'i huɗu.
Madogara
صحيح البخاري (9/ 121) (7405).
صحيح مسلم (4/ 2067) (2675).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (17/ 151).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 516).
منار القاري شرح مختصر صحيح البخاري، حمزة محمد (5/ 372).
الجواب الكافي لمن سأل عن الدواء الشافي أو الداء والدواء (ص25).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 510).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 983).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «يَعْقِدُ الشَّيْطَانُ عَلَى قَافِيَةِ رَأْسِ أَحَدِكُمْ إِذَا هُوَ نَامَ ثَلاَثَ عُقَدٍ يَضْرِبُ كُلَّ عُقْدَةٍ عَلَيْكَ لَيْلٌ طَوِيلٌ، فَارْقُدْ، فَإِنِ اسْتَيْقَظَ فَذَكَرَ اللَّهَ، انْحَلَّتْ عُقْدَةٌ، فَإِنْ تَوَضَّأَ انْحَلَّتْ عُقْدَةٌ، فَإِنْ صَلَّى انْحَلَّتْ عُقْدَةٌ، فَأَصْبَحَ نَشِيطًا طَيِّبَ النَّفْسِ، وَإِلَّا أَصْبَحَ خَبِيثَ النَّفْسِ كَسْلاَنَ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shaiɗan yana ƙulli uku akan ƙarshen kan ɗayanku idan ya yi bacci, yana buga (hannunsa) akan kowane ƙulli, ka yi dare mai tsawo, sai ka yi bacci, idan ya farka sai ya ambaci Allah, sai kulli ɗaya ya warware, idan ya yi alwala sai ƙulli ɗaya ya warware, idan ya yi sallah sai ƙulli (ɗaya) ya warware, sai ya wayi gari mai yawan nishaɗi mai daɗin rai, inba haka ba sai ya wayi gari mai mummunar rai mai yawan kasala".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin halin Shaiɗan da kuma yakinsa ga mutumin da yake nufin tsayuwa dan sallar dare ko Asuba.
domin mumini idan ya tafi yin bacci shaiɗan yana ƙulli uku akan ƙyaraysa - yana nufin: Ƙarshen kansa -.
Idan mumini ya farka kuma ya ambaci Allah - Maɗaukakin sarki - bai amsa waswasin shaiɗan ba; sai ƙulli (ɗaya) ya warware.
Idan ya yi alwala sai ya warware.
Idan ya tashi ya yi sallah sai ƙulli na uku ya warware, sai ya wayi gari mai yawan nishaɗi mai daɗin rai; dan farin cikinsa da abinda Allah Ya datar da shi na aikin ɗa'a, yana mai bushara da abinda Allah Ya yi masa alƙawari na lada da gafara, tare da abinda ya gushe daga gare shi na ƙulle-ƙullen Shaiɗan da nauyayawarsa, in ba haka ba zai wayi gari mai mummunan rai, mai baƙin ciki a zuciya, mai kasala daga ayyukan alheri da biyayya; domin cewa shi abin ɗaurewa ne da marin Shaiɗan, kuma abin nisanta daga kusancin Al-Rahman.
Fa’idoji
- Shaiɗan kowane lokaci yana ƙoƙari ta kowace hanya ga mutum; dan ya tsare tsakaninsa da tsakanin biyayya ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -, kuma babu tsira ga bawa daga Shaiɗan sai da neman taimakon Allah - Mai girma da ɗaukaka -, da yin riƙo da sabubban kariya da tsari.
- Ambatan Allah - Maɗaukakin sarki - da bauta masa suna gadar da nishaɗi a rai da walwalar ƙirji, kuma suna kore kasala da nauyin jiki, kuma suna tafiyar da baƙin ciki da ƙiyayya; domin cewa su suna korar Shaiɗan wannan yana daga wasiwasinsa.
- Mumini yana farin ciki da datarwar Allah - Maɗaukakin sarki - gare shi dan tsayuwa da ɗa'arSa, kuma yana baƙin ciki dan taƙaitawarsa a matakan falala da kuma cika.
- Gafala da karkata daga ayyukan biyayya shi yana daga aikin Shaiɗan da kuma kyalkyalinsa.
- Waɗannan al'amuran guda uku - ambatan Allah, da alwala, da sallah - suna kore Shaiɗan.
- Ƙullin Shaiɗan akan ƙarshen kai a keɓance; domin nan ce cibiya ta ƙarfi, kuma fagene na jujjuayawrsu, idan ya yi ɗauri akansa sai ya samu damar da zai yi rinjaye akan ran mutum, da kuma jefa barci a kansa.
- Ibnu Hajar al-Asƙalani ya ce: Ambatan dare a cikin faɗinsa: "Na horeka da dare", zahirinsa hakan na faruwa ne a baccin dare kadai.
- Ibnu Hajar al-Asƙalani ya ce: Babu wani keɓantaccen abu na Zikiri da aka ware akan wannan, da za’a ce wani ba ya wadatarwa sai shi, kawai, dukkan abinda ambatan Allah ya gasgata akansa ya isar, karatun Alƙur'ni yana shiga ciki, da karatun hadisin Annabi, da shagaltuwa da ilimin shari'a, mafi cancantar abinda za'a tinatar da shi faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanda ya farka da daddare sai ya ce: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai yake baShi da abokin tarayya, mulki nasa ne godiya ta tabbata gareShi, Shi Mai iko ne akan dukkan komai, godiya ta tabbata ga Allah, tsarki ya tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne Mafi girma, babu dabara babu karfi sai ga Allah. Sannan ya ce: Ya Allah Ka gafarta mini, ko ya yi addu'a za'a amsa masa, idan ya yi alwala za'a karbi sallarsa). Bukharine ya ruwaito shi.
Madogara
صحيح البخاري (2/ 52) (1142).
صحيح مسلم (1/ 538) (776).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 328).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 834).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (15/ 305).
فتح الباري شرح صحيح البخاري، لأحمد العسقلاني (10/ 564).
طرح التثريب في شرح التقريب، العراقي (3/ 82).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ سَعْدِ بنِ أبي وَقَّاصٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: كُنَّا عِنْدَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: «أَيَعْجِزُ أَحَدُكُمْ أَنْ يَكْسِبَ، كُلَّ يَوْمٍ أَلْفَ حَسَنَةٍ؟» فَسَأَلَهُ سَائِلٌ مِنْ جُلَسَائِهِ: كَيْفَ يَكْسِبُ أَحَدُنَا أَلْفَ حَسَنَةٍ؟ قَالَ: «يُسَبِّحُ مِائَةَ تَسْبِيحَةٍ، فَيُكْتَبُ لَهُ أَلْفُ حَسَنَةٍ، أَوْ يُحَطُّ عَنْهُ أَلْفُ خَطِيئَةٍ».
Daga Sa'ad ɗan Abu Waƙas - Allah Ya yarda da shi - ya ce Mun kasance a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - sai ya ce: «Shin ɗayanku zai gaza wajen samun kyakykyawan aiki dubu a kowace rana?» Sai wani mai tambaya daga mazauna wajen ya tambaye shi: Ta yaya ɗayammu zai samu kyakykyawan aiki dubu? Ya ce: «Ya yi tasbihi sau ɗari, sai a rubuta masa kyakykyawa dubu, ko kuma a sarayar masa da kura-kurai dubu».
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa: Shin ɗayanku zai iya samun kyakkyawan lada dubu a kowace rana? Sai ɗaya daga cikin mazauna a gurinsa ya ce: Ta yaya mutum zai iya samun kyakkyawan lada dubu a kowace rana cikin sauƙi? Ya ce: To ya ce: "Subhanal Lahi". sau ɗari; sai a rubuta masa kaykkyawa dubu; domin cewa kyakkyawa ɗaya da kwatankwacinsa goma ne, ko kuma a kankare masa mummuna dubu daga cikin munanan ayyukansa.
Fa’idoji
- Kwaɗaitarwa akan falaloli; domin cewa su ne tsanin ayyukan biyayya.
- Falalar tasbihi da zikiri, kuma cewa wannan aikin mai sauƙi ne wanda mutum ba zai ɗorawa kansa komai ba, da shi ne mutum zai samu wannan ladan mai girma.
- Gaggawar sahabbai zuwa aikata aikin alheri ba tare da wani jinkiri ba.
- Ninka kyawawan ayyuka zuwa kwatankwacinsu sau goma, hakan misalin faɗinSa ne - Allah Maɗaukakin sarki -: (Wanda ya zo da kyakkyawa to yana da kwatankwacinsa goma) [Al-An'am: 160], wannan shi ne mafi ƙarancin matakan ninkawa, inba haka ba ai tabbas haƙiƙa ya zo zuwa ninki ɗari bakwai.
- Ya zo a cikin wasu daga cikin ruwayoyi canjin (Au (ko)) (Wa (da)) a cikin faɗinsa: Ko a sarayar masa... Al-Ƙari ya ce: Wau takan zo da ma'anar Au, dan haka babu saɓani tsakanin ruwayoyi biyun, kamar ma'ana: Cewa wanda ya faɗeta za'a rubuta masa kyakkyawa dubu, idan bai zamo a kansa ba sai a sarayar masa da wani abu a kuma ba shi wani abu, kuma zai iya yi wuwa Au ɗin ta kasance da ma'anar Wau, ko da ma'anar kai, to a wannan lokacin sai a haɗa tsakaninsu, kuma falalar Allah ta fi yalwa daga hakan ya ƙare, cewa shi za'a rubuta masa kyawawan lada dubu kuma a sarayar masa da munanan ayyuka dubu.
Madogara
صحيح مسلم (4/ 2073) (2698).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 507).
مرقاة المفاتيح، لعلي القاري (4/ 1594).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 980).
مرعاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعبيد الله المباركفوري (7/ 454).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي مُوسَى رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَثَلُ الَّذِي يَذْكُرُ رَبَّهُ وَالَّذِي لاَ يَذْكُرُ رَبَّهُ، مَثَلُ الحَيِّ وَالمَيِّتِ»، ولفظ مسلم: «مَثَلُ الْبَيْتِ الَّذِي يُذْكَرُ اللهُ فِيهِ، وَالْبَيْتِ الَّذِي لَا يُذْكَرُ اللهُ فِيهِ، مَثَلُ الْحَيِّ وَالْمَيِّتِ».
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Misalin wanda yake ambatan Ubangijinsa da wanda ba ya ambatan Ubangijinsa, kamar rayayye ne da matacce", lafazin Muslim kuma: "Misalin gidan da ake ambatan Allah a cikinsa, da gidan da ba'a ambatan Allah a cikinsa, kamar rayayye ne da matacce".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana banbanci tsakanin wanda yake ambatan Allah - Maɗaukakin sarki - da wanda ba ya ambatanSa, kuma misalin banbanci ne tsakanin rayayye da matacce a anfaninsa da kyakkyawan zahirinsa, misalin wanda yake ambatan Ubangijinsa misalin rayayye ne wanda a zahirinsa mai adone da hasken rayuwa, kuma baɗininsa da hasken ma'arifa, kuma a cikinsa akwai anfani, kuma misalin wanda ba ya ambatan Allah kwatankwacin mamaci ne wanda zahirinsa ba ya anfani, kuma baɗininsa ɓataccene, babu wani anfani acikinsa.
Haka nan gidan da ake siffanta shi da rayayye idan mazaunansa sun kasance suna ambatan Allah, inba haka ba to shi mataccen gida ne, saboda barin mazaunansa daga ambatan Allah; idan an wawaita mamaci da matacce a cikin siffanta gida kawai ana nufi da shi mazaunin gidan.
Fa’idoji
- Kwaɗaitarwa akan ambatan Allah da gargaɗarwa daga rafkana daga gare shi.
- Zikiri shi ne rayuwar rai, kamar yadda rai rayuwar jiki ne.
- Daga shiryarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - buga misali dan kusanto da ma'anoni.
- Al-Nawawi ya ce: A cikinsa akwai kwaɗaitarwa akan ambatan Allah - Maɗaukakin sarki - a cikin gida, kuma cewa kada a wofantar da shi daga zikiri.
- Al-Nawawi ya ce: Kuma a cikinsa cewa tsawon rayuwa a cikin ɗa'a falala ce koda mamacin yana cirata zuwa alheri; domin rayayye zai risku da shi kuma zai ƙaru a kansa da abinda ya aikata shi na ayyukan ɗa'a.
Madogara
صحيح البخاري (8/ 86) (6407).
صحيح مسلم (1/ 539) (779).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، (2/ 982).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 516).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ جَابِرٍ رَضيَ اللهُ عنهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنْ قَالَ: سُبْحَانَ اللهِ العَظِيمِ وَبِحَمْدِهِ، غُرِسَتْ لَهُ نَخْلَةٌ فِي الجَنَّةِ».
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Tsarki ya tabbata ga Allah da yabonSa, za a dasa masa bishiyar dabino a cikin aljanna».
Tirmizi ne ya ruwaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya ce: (Tsarki ya tabbata ga Allah) Ya tsarkakeShi (Mai girma) da zatinSa da siffofinSa da kuma ayyukanSa (da yabonSa) abin haɗawa da raɓa siffofin cika gareShi - tsarki ya tabbatar maSa -; za'a kafa kuma za'a dasa masa wani dabino a cikin ƙasar aljanna a duk lokacin da ya faɗeta.
Fa’idoji
- Kwaɗaitarwa akan yawaita ambatan Allah - Maɗaukakin sarki -, daga hakan (akwai): Tasbihi tare da Tahmidi.
- Aljanna mai yalwa ce, kuma dashenta shi ne Tasbihi da Tahmidi, wannan falala ce daga Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma ni'imominSa.
- An keɓanci bishiyar dabino a cikin hadisin banda waninta cikin bishoyoyi; saboda yawan anfaninta da kuma daɗin 'ya'yanta; sbaoda haka ne Allah Ya buga misalin mumini da kuma imaninsa da ita a cikin Alƙur'ani.
Madogara
سنن الترمذي (5/ 456) (3464).
مرعاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، للمباركفوري (7/ 464).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 985).
مشكاة المصابيح، للتبريزي (2/ 713).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ كَعْبِ بْنِ عُجْرَةَ رضي الله عنه عَنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مُعَقِّبَاتٌ لَا يَخِيبُ قَائِلُهُنَّ -أَوْ فَاعِلُهُنَّ- دُبُرَ كُلِّ صَلَاةٍ مَكْتُوبَةٍ، ثَلَاثٌ وَثَلَاثُونَ تَسْبِيحَةً، وَثَلَاثٌ وَثَلَاثُونَ تَحْمِيدَةً، وَأَرْبَعٌ وَثَلَاثُونَ تَكْبِيرَةً».
Daga Ka'ab dan Ujrah - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Masu biyewa juna mai fadinsu ba ya tabewa - ko mai aikata su - a bayan kowacce sallar farilla, Tasbihi talatin da uku, da Tahmidi talatin da uku, da Kabbara talatin da hudu".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da wasu zikiran da mai fadainsu ba ya asara kuma ba ya tabewa, kai yana da ladan wadannan kalmomin, kuma sashinsu yana zuwa bayan sashi, ana fadarsu a bayan sallolin farilla, su ne:
"Tsarki ya tabbata ga Allah" sau talatin da uku, wato tsarkakeshi - Madaukakin sarki - daga dukkanin tawaya.
"Godiya ta tabbata ga Allah" sau talatin da uku, ita ce siffanta Allah da cikakkiyar cika tare da soyayyarSa da girmamaShi.
"Allah ne Mafi girma" sau talatin da hudu, Allah ne Mafi girmamawa Mafi buwaya daga dukkan komai.
Fa’idoji
- Falalar tasbihi da tahmidi da kabbara, su ne wanzajju nagartattu.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 418) (596).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 501).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 976).
مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (2/ 766).
تيسير العلام، للبسام (ص227).
فيض القدير شرح الجامع الصغير، لزين الدين المناوي (5/ 525).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي سعيد الخدري رضي الله عنه مرفوعاً: «إنَّ الشيطانَ قال: وعِزَّتِك يا رب، لا أَبرحُ أُغوي عبادَك ما دامت أرواحُهم في أجسادهم، قال الربُّ: وعِزَّتي وجَلالي لا أزال أغفرُ لهم ما استغفروني».
Daga Abu Sa'id Al-Khudri -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Manzon Allah "Lallai shaixan ya ce: Na rantse da Girmanka Allah, ba zan gushe ba ina vatar da Bayinka, matuqar dai rayukansu suna jikinsu, Ubangiji ya ce: Na rantse da Girmana da Xaukaka ta ba zan gushe ba ina gafarta musu matuqar sun nemi gafara ta"
Ahmad ne ya rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi
“Shaidan ya ce: Kuma daukakarka, ya Ubangiji, ba zan ci gaba da yaudarar bayinka ba muddin rayukansu suna cikin jikinsu.” Wato, Shaidan ya rantse da daukakar Allah cewa zai ci gaba da batar da bayin a tsawon rayuwarsu. . "Ubangiji ya ce: Darajata da darajata duk da haka na gafarta musu in nemi gafara" zunubai., “Shaiɗan ya ce: Kuma ɗaukakarka, ya Ubangiji, ba zan yaudari bayinka ba har abada idan rayukansu suna cikin jikinsu.” Wato: Shaiɗan ya rantse da ɗaukakar Allah cewa zai ci gaba da ɓatar da bayinsa a cikin aikin yana rayuwa. "Ubangiji ya ce: Darajata da darajata har ilayau na gafarta musu idan suka nemi gafara." Wato, Ubangiji Madaukaki ya ce a cikin amsar da ya ba shi: Darajata da daukakata har yanzu suna gafarta musu muddin suka roke ni. ya gafarta musu zunubansu.
Madogara
مسند الإمام أحمد بن حنبل، تحقيق: شعيب الأرنؤوط - عادل مرشد، وآخرون، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الأولى، 1421هـ - 2001م.
مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي بن سلطان الملا الهروي القاري، الناشر: دار الفكر، بيروت – لبنان، الطبعة: الأولى، 1422هـ - 2002م.
مرعاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لأبي الحسن عبيد الله بن محمد عبد السلام بن خان محمد بن أمان الله بن حسام الدين الرحماني المباركفوري، الناشر: إدارة البحوث العلمية والدعوة والإفتاء - الجامعة السلفية - بنارس الهند، الطبعة: الثالثة - 1404 هـ، 1984 م.
التنوير شرح الجامع الصغير، لمحمد بن إسماعيل بن صلاح بن محمد الحسني، الكحلاني الأمير الصنعاني، المحقق: د. محمَّد إسحاق محمَّد إبراهيم، الناشر: مكتبة دار السلام، الرياض، الطبعة: الأولى، 1432 هـ - 2011 م.
صحيح الجامع الصغير وزياداته، للألباني، نشر: المكتب الإسلامي.
صفات الله عز وجل الواردة في الكتاب والسنة : علوي بن عبد القادر السَّقَّاف دار الهجرة الطبعة : الثالثة ، 1426 هـ - 2006 م.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com