Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Tsarki ya tabbata ga Allah da yabonSa, za a dasa masa bishiyar dabino a cikin aljanna

عَنْ جَابِرٍ رَضيَ اللهُ عنهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنْ قَالَ: سُبْحَانَ اللهِ العَظِيمِ وَبِحَمْدِهِ، غُرِسَتْ لَهُ نَخْلَةٌ فِي الجَنَّةِ».
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Tsarki ya tabbata ga Allah da yabonSa, za a dasa masa bishiyar dabino a cikin aljanna».
Tirmizi ne ya ruwaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya ce: (Tsarki ya tabbata ga Allah) Ya tsarkakeShi (Mai girma) da zatinSa da siffofinSa da kuma ayyukanSa (da yabonSa) abin haɗawa da raɓa siffofin cika gareShi - tsarki ya tabbatar maSa -; za'a kafa kuma za'a dasa masa wani dabino a cikin ƙasar aljanna a duk lokacin da ya faɗeta.

Fa’idoji
  1. Kwaɗaitarwa akan yawaita ambatan Allah - Maɗaukakin sarki -, daga hakan (akwai): Tasbihi tare da Tahmidi.
  2. Aljanna mai yalwa ce, kuma dashenta shi ne Tasbihi da Tahmidi, wannan falala ce daga Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma ni'imominSa.
  3. An keɓanci bishiyar dabino a cikin hadisin banda waninta cikin bishoyoyi; saboda yawan anfaninta da kuma daɗin 'ya'yanta; sbaoda haka ne Allah Ya buga misalin mumini da kuma imaninsa da ita a cikin Alƙur'ani.
Madogara

سنن الترمذي (5/ 456) (3464). مرعاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، للمباركفوري (7/ 464). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 985). مشكاة المصابيح، للتبريزي (2/ 713).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FA'IDOJIN ZIKIRIN ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com