Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa: Shin ɗayanku zai iya samun kyakkyawan lada dubu a kowace rana? Sai ɗaya daga cikin mazauna a gurinsa ya ce: Ta yaya mutum zai iya samun kyakkyawan lada dubu a kowace rana cikin sauƙi? Ya ce: To ya ce: "Subhanal Lahi". sau ɗari; sai a rubuta masa kaykkyawa dubu; domin cewa kyakkyawa ɗaya da kwatankwacinsa goma ne, ko kuma a kankare masa mummuna dubu daga cikin munanan ayyukansa.
- Kwaɗaitarwa akan falaloli; domin cewa su ne tsanin ayyukan biyayya.
- Falalar tasbihi da zikiri, kuma cewa wannan aikin mai sauƙi ne wanda mutum ba zai ɗorawa kansa komai ba, da shi ne mutum zai samu wannan ladan mai girma.
- Gaggawar sahabbai zuwa aikata aikin alheri ba tare da wani jinkiri ba.
- Ninka kyawawan ayyuka zuwa kwatankwacinsu sau goma, hakan misalin faɗinSa ne - Allah Maɗaukakin sarki -: (Wanda ya zo da kyakkyawa to yana da kwatankwacinsa goma) [Al-An'am: 160], wannan shi ne mafi ƙarancin matakan ninkawa, inba haka ba ai tabbas haƙiƙa ya zo zuwa ninki ɗari bakwai.
- Ya zo a cikin wasu daga cikin ruwayoyi canjin (Au (ko)) (Wa (da)) a cikin faɗinsa: Ko a sarayar masa... Al-Ƙari ya ce: Wau takan zo da ma'anar Au, dan haka babu saɓani tsakanin ruwayoyi biyun, kamar ma'ana: Cewa wanda ya faɗeta za'a rubuta masa kyakkyawa dubu, idan bai zamo a kansa ba sai a sarayar masa da wani abu a kuma ba shi wani abu, kuma zai iya yi wuwa Au ɗin ta kasance da ma'anar Wau, ko da ma'anar kai, to a wannan lokacin sai a haɗa tsakaninsu, kuma falalar Allah ta fi yalwa daga hakan ya ƙare, cewa shi za'a rubuta masa kyawawan lada dubu kuma a sarayar masa da munanan ayyuka dubu.
صحيح مسلم (4/ 2073) (2698). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 507). مرقاة المفاتيح، لعلي القاري (4/ 1594). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 980). مرعاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعبيد الله المباركفوري (7/ 454).