Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Idan mutum zai shiga gidansa, sai ya ambaci sunan Allah a yayin shigarsa da lokacin cin abincin sa , Shaidan zai ce : Babu makwanci gareku, kuma babu abincin dare

عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللهِ رضي الله عنهما أَنَّهُ سَمِعَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «إِذَا دَخَلَ الرَّجُلُ بَيْتَهُ، فَذَكَرَ اللهَ عِنْدَ دُخُولِهِ وَعِنْدَ طَعَامِهِ، قَالَ الشَّيْطَانُ: لَا مَبِيتَ لَكُمْ، وَلَا عَشَاءَ، وَإِذَا دَخَلَ، فَلَمْ يَذْكُرِ اللهَ عِنْدَ دُخُولِهِ، قَالَ الشَّيْطَانُ: أَدْرَكْتُمُ الْمَبِيتَ، وَإِذَا لَمْ يَذْكُرِ اللهَ عِنْدَ طَعَامِهِ، قَالَ: أَدْرَكْتُمُ الْمَبِيتَ وَالْعَشَاءَ».
Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Idan mutum zai shiga gidansa, sai ya ambaci sunan Allah a yayin shigarsa da lokacin cin abincin sa , Shaidan zai ce : Babu makwanci gareku, kuma babu abincin dare, idan zai shiga bai ambaci sunan Allah a yayin shigarsa ba, Shaidan zai ce: Kun sami makwanci, idan bai ambaci Allah a lokacin cin abincin sa ba, zai ce : Kun riski makwanci da abincin dare".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da ambatan Allah a yayin shiga gida da kafin cin abinci, kuma cewa shi idan ya ambaci Allah da fadinsa: (Da sunan Allah) a lokacin shigarsa da kuma lokacin fara abincinsa, Shaidan zai cewa mataimakansa: Baku da rabo na makwanci ko abincin dare a wannan gidan da mai shi ya kare kansa daga ku da ambatan Allah - Madaukakin sarki -. Amma idan zai shiga gidansa bai ambaci Allah a lokacin shigarsa ba ko lokacin cin abincinsa, sai Shaidan ya sanar da mataimaknsa cewa sun sami makwanci, da abincin dare a wannan gidan.

Fa’idoji
  1. An so ambatan Allah a lokacin shiga gida da lokacin cin abinci, domin Shaidan yana kwana a cikin gidaje, yana ci daga abincin mutanen gidan idan ba su ambaci sunan Allah - Madaukakin sarki ba -.
  2. Shaidan yana lura da Dan Adam a cikin aikinsa da jujjuyawarsa acikin al'amauransa gaba dayansu, idan ya rafkana daga zikiri zai samu abin nufinsa daga gare shi .
  3. Zikiri yana kore Shaidan.
  4. Kowanne Shaidan yana da mabiya da masoya suna albishir da maganarsa kuma suna bin umarninsa.
Madogara

صحيح مسلم (3/ 1598) (2018). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 50). تطريز رياض الصالحين، لفيصل المبارك (ص467). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (4/ 190). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 700).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
TSARIN ANNABI TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBBA A GARESHI WAJEN YIN ZIKIRI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com