Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

TSARIN ANNABI TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBBA A GARESHI WAJEN YIN ZIKIRI

Hadisai 7

Idan mutum zai shiga gidansa, sai ya ambaci sunan Allah a yayin shigarsa da lokacin cin abincin sa , Shaidan zai ce : Babu makwanci gareku, kuma babu abincin dare

عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللهِ رضي الله عنهما أَنَّهُ سَمِعَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «إِذَا دَخَلَ الرَّجُلُ بَيْتَهُ، فَذَكَرَ اللهَ عِنْدَ دُخُولِهِ وَعِنْدَ طَعَامِهِ، قَالَ الشَّيْطَانُ: لَا مَبِيتَ لَكُمْ، وَلَا عَشَاءَ، وَإِذَا دَخَلَ، فَلَمْ يَذْكُرِ اللهَ عِنْدَ دُخُولِهِ، قَالَ الشَّيْطَانُ: أَدْرَكْتُمُ الْمَبِيتَ، وَإِذَا لَمْ يَذْكُرِ اللهَ عِنْدَ طَعَامِهِ، قَالَ: أَدْرَكْتُمُ الْمَبِيتَ وَالْعَشَاءَ».
Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Idan mutum zai shiga gidansa, sai ya ambaci sunan Allah a yayin shigarsa da lokacin cin abincin sa , Shaidan zai ce : Babu makwanci gareku, kuma babu abincin dare, idan zai shiga bai ambaci sunan Allah a yayin shigarsa ba, Shaidan zai ce: Kun sami makwanci, idan bai ambaci Allah a lokacin cin abincin sa ba, zai ce : Kun riski makwanci da abincin dare".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da ambatan Allah a yayin shiga gida da kafin cin abinci, kuma cewa shi idan ya ambaci Allah da fadinsa: (Da sunan Allah) a lokacin shigarsa da kuma lokacin fara abincinsa, Shaidan zai cewa mataimakansa: Baku da rabo na makwanci ko abincin dare a wannan gidan da mai shi ya kare kansa daga ku da ambatan Allah - Madaukakin sarki -. Amma idan zai shiga gidansa bai ambaci Allah a lokacin shigarsa ba ko lokacin cin abincinsa, sai Shaidan ya sanar da mataimaknsa cewa sun sami makwanci, da abincin dare a wannan gidan.

Fa’idoji
  1. An so ambatan Allah a lokacin shiga gida da lokacin cin abinci, domin Shaidan yana kwana a cikin gidaje, yana ci daga abincin mutanen gidan idan ba su ambaci sunan Allah - Madaukakin sarki ba -.
  2. Shaidan yana lura da Dan Adam a cikin aikinsa da jujjuyawarsa acikin al'amauransa gaba dayansu, idan ya rafkana daga zikiri zai samu abin nufinsa daga gare shi .
  3. Zikiri yana kore Shaidan.
  4. Kowanne Shaidan yana da mabiya da masoya suna albishir da maganarsa kuma suna bin umarninsa.
Madogara

صحيح مسلم (3/ 1598) (2018). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 50). تطريز رياض الصالحين، لفيصل المبارك (ص467). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (4/ 190). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 700).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ya Allah gareKa na miƙa wuya, kuma da Kai ne na yi imani, gareka ne na dogara, gareKa ne na dawo, saboda Kai ne na yi husuma, Ya Allah lallai ni ina neman tsari da buwayarKa, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai (kada) Ka ɓatar da ni, Kaine Rayayye wanda ba zai mutu ba, aljanu da mutane kuwa zasu mutu

عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضيَ اللهُ عنهما أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَقُولُ: «اللهُمَّ لَكَ أَسْلَمْتُ، وَبِكَ آمَنْتُ، وَعَلَيْكَ تَوَكَّلْتُ، وَإِلَيْكَ أَنَبْتُ، وَبِكَ خَاصَمْتُ، اللهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِعِزَّتِكَ، لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ أَنْ تُضِلَّنِي، أَنْتَ الْحَيُّ الَّذِي لَا يَمُوتُ، وَالْجِنُّ وَالْإِنْسُ يَمُوتُونَ».
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana cewa: "Ya Allah gareKa na miƙa wuya, kuma da Kai ne na yi imani, gareka ne na dogara, gareKa ne na dawo, saboda Kai ne na yi husuma, Ya Allah lallai ni ina neman tsari da buwayarKa, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai (kada) Ka ɓatar da ni, Kaine Rayayye wanda ba zai mutu ba, aljanu da mutane kuwa zasu mutu"
Bukhari da Muslim ne suka ruwaito, wannan lafazin na Muslim ne, amma Bukhari ya rawaito shi a taƙaiceDarajaIngantacce ne
Sharhi

Ya kasance daga addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance yana cewa: (Ya Allah gareKa ne na miƙa wuya) kuma na jawu, (da Kai ne na yi imani) na gasgata kuma na yi iƙrari, (kuma gareKa ne na dogara) na fawwala na kuma dogara, (gareKa ne na koma) na koma na fuskanta, (saboda Kai ne na yi husuma) na yi jayayya da maƙiyanKa, (Ya Allah ni ina neman tsarinKa) ina fakewa (da buwayarKa) da hanawarKa da kuma rinjayenKa, (babu abin bautawa da gaskiya sai Kai) kuma babu wani abin bautawa da gaskiya inba Kai ba, (da Ka ɓatar da ni) daga shiriya da dacewa da yardarKa, (Kai ne Rayayye wanda ba zai mutu ba) kuma ba zai ƙareba, (aljanu da mutane kuwa zasu mutu).

Fa’idoji
  1. Halaccin gabatar da yabo (ga Allah) a yayin roƙon kowane abin nema.
  2. Wajabcin dogara ga Allah - Maɗaukakin sarki - Shi kaɗai da neman kiyayewa daga gareShi; domin cewa Shi Mai siffantuwa ne da siffofin cika, kuma Shi kaɗaine wanda ake dogara da Shi, halittu dukkaninsu gajiyayyu ne kuma masu tiƙewa ne zuwa ga mutuwa, su basu cancanci dogara a kansu ba.
  3. Koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin addu'a da waɗannan kalmomi masu tattarowa komai ya shiga, waɗanda suke bayyanar da gaskiyar imani da kuma matuƙar sakankancewa.
  4. Sindi ya ce: Faɗinsa (Kai ne Rayayye) wato: Kai ne wanda ya kamata a nemi tsari da Shi ba waninKa ba.
Madogara

صحيح البخاري (9/ 117) (7383). صحيح مسلم (4/ 2086) (2717). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص72). فتح رب البرية بتلخيص الحموية، لابن عثيمين (ص79). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 109). مرعاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، عبيد الله المباركفوري (8/ 223).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ku kama kafa da fadin Ya Ma'abocin Girma da Daukaka

عن أنس رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رسُولُ الله صلى الله عليه وسلم : «ألِظُّوا بـ (يَاذا الجَلاَلِ والإكْرامِ)».
Daga Anas Dan Malik - Allah ya yarda da shi - ya ce Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Ku kama kafa da fadin Ya Ma'abocin Girma da Daukaka"r"
Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

- رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين، للإمام أبي زكريا النووي، تحقيق د. ماهر الفحل، دار ابن كثير، دمشق، الطبعة الأولى، 1428ه. - نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة، بيروت، الطبعة الرابعة عشر، 1407هـ. - كنوز رياض الصالحين، لحمد بن ناصر العمار، دار كنوز إشبيليا - الطبعة الأولى، 1430ه. سنن الترمذي - محمد بن عيسى الترمذي، تحقيق وتعليق: أحمد محمد شاكر ومحمد فؤاد عبد الباقي وإبراهيم عطوة عوض - شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي الحلبي - مصر، الطبعة: الثانية، 1395هـ - 1975م.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ya ku mutane, ku tuba zuwa ga Allah, lallai cewa ni ina tuba zuwa gareShi a yini sau ɗari

عن الْأَغَرِّ رضي الله عنه، وَكَانَ مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «يَا أَيُّهَا النَّاسُ تُوبُوا إِلَى اللهِ، فَإِنِّي أَتُوبُ فِي الْيَوْمِ إِلَيْهِ مِائَةَ مَرَّةٍ».
Daga Agar - Allah Ya yarda da shi -, kuma ya kasance daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce: Manzon Allah - tsiar da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ya ku mutane, ku tuba zuwa ga Allah, lallai cewa ni ina tuba zuwa gareShi a yini sau ɗari".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana umartar mutane da yawaita tuba da istigfari, kuma yana bada labari game da kansa cewa shi yana tuba zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki - kuma yana neman gafararSa a yini sama da sau ɗari, alhali haƙiƙa an gafarta masa abinda ya gabatar na zunubinsa da abinda ya jinkirta, a cikin hakan akwai cikar kankan da kai da bauta ga Allah - Maɗaukaki -.

Fa’idoji
  1. Kowane mutum duk yadda matsayinsa da darajarsa suka kai a imani, to shi yana buƙatuwa zuwa komawa ga Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka -, da cika kansa da tuba, kuma babu wanda ba ya wofinta daga kasawa a tsayuwa da haƙƙin Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka -: (Ku tuba zuwa ga Allah gaba ɗaya yaku muminai).
  2. Tuba a game daidai ne daga aikata abubuwan da aka haramta ne da zunubai ko daga kasawa ne a aikata wajibai.
  3. Ikhlasi a cikin tuba sharaɗi ne akan karbar tuban, wanda ya bar wani zunubi ba dan Allah ba to ba ya kasancewa mai tuba.
  4. AlNawawi ya ce: A kwai sharuɗɗa uku ga tuba: Ya bar aikata saɓo, kuma ya yi nadama akan aikata shi, kuma ya ƙudirci niyya a yanke cewa ba zai koma ba zuwa tamkarta ba har abada, idan saɓon yana rataye ne da ɗan Adam to yana da sharaɗi na huɗu, shi ne: Maida abinda aka zalinta zuwa ga mai shi, ko tabbatar da kuɓuta daga gare shi.
  5. Faɗakarwa akan neman gafarar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba ya lazimtar cewa ya kasance dan wasu zunuban da ya aikata su ne, sai dai hakan dan cikar ubudiyyarsa ne da kuma danfaruwa da ambatanSa - tsarki ya tabbatar maSa - da jinsa girman haƙƙin Allah - Maɗaukakin sarki - da kasawar bawa duk aikin da ya aikata a godiyar ni'imominSa, hakan yana daga babin shara'antawa ga al'umma a bayansa ne, zuwa wanin hakan daga hikimomi.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2075) (2702). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 33). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (1/ 97). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 52).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a cikin sujjadarsa: "Ya Allah Ka gafarta mini dukkan zunubaina, ƙanƙaninsa, da babbansa, na farkonsa da na ƙarshensa, na bayyanensa da na ɓoyensa

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه: أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَقُولُ فِي سُجُودِهِ: «اللهُمَّ اغْفِرْ لِي ذَنْبِي كُلَّهُ دِقَّهُ، وَجِلَّهُ، وَأَوَّلَهُ وَآخِرَهُ وَعَلَانِيَتَهُ وَسِرَّهُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a cikin sujjadarsa: "Ya Allah Ka gafarta mini dukkan zunubaina, ƙanƙaninsa, da babbansa, na farkonsa da na ƙarshensa, na bayyanensa da na ɓoyensa".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana addu'a a cikin sujjadarsa sai ya ce: (Ya Allah Ka gafarta mini zunubina) da suturta shi, kuma Ka kareni nauyinsu; sai Ka yi rangwami Ka ƙetare ka kauda kai, (dukkansa), ka taimake ni: (ƙanƙaninsa) ƙaraminsa da ƙanƙaninsa, (da babbansa) babbansa da mai yawansa, (da na farkonsa) farkon zunubi, (da na ƙarshensa), da abinda ke tsakaninsu, (na zahirinsa da na baɗininsa) daga abinda babu wani wanda ya sanshi sai Kai - tsarki ya tabbatar maKa -.

Fa’idoji
  1. Ibnul-Kayyim ya ce: Neman gafarar zunubai ƙanana da manya, ƙanƙani da mai girma, na farko da na ƙarshe, na ɓoye da na bayyane, wannan gamewar kuma wannan ƙunshin dan tuba ya zo akan abinda bawa ya san shi daga zunubansa, da abinda ma bai sanshi ba.
  2. An ce: Kawai ya gabatar da (ƙanƙani) akan (mai girma) ne; domin cewa mai tambaya yana kara matsawa ne a cikin tambayarsa wato yana hauhawa, domin cewa manyan zunubai suna faruwa a galibi ne daga nacewa akan ƙananu da kuma rashin kulawa da su, kamar cewa su hanyoyi ne zuwa manyan zunubai, kuma daga haƙƙin hanya shine a gabatar da ita a tabbatarwa da kuma ɗaukakawa.
  3. Kanƙan da kai zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -, da nemanSa gafara daga dukkan zunubai, ƙanana da manya.
  4. Nawawi ya ce: A cikinsa akwai ƙarfafa addu'a da yawaita lafazzukanta duk da sashinsu ya wadatar da sashi.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 350) (483). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 506). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص780). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 509). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (17/ 111). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 979).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ya Allah, ka gafarta min abin da na yi da wanda na jinkirta, da abin da na yi farin ciki da abin da na bayyana

عن علي بن أبي طالب رضي الله عنه قال: كان رسول الله صلى الله عليه وسلم إذا قام إلى الصلاة يكون من آخر ما يقول بين التشهد والتسليم: «اللهم اغفر لي ما قَدَّمتُ وما أخَّرْتُ، وما أسررتُ وما أعلنتُ، وما أسْرَفتُ، وما أنت أعلم به مني، أنت المُقَدِّم، وأنت المؤخر، لا إله إلا أنت».
Daga Aliyu bn Abi Talib - Allah ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana tsayuwa don yin salla, zai kasance daya daga cikin abubuwan karshe da ya fada tsakanin tashahud da tasleem din: "Ya Allah, ka gafarta min abin da na yi da wanda na jinkirta, da abin da na yi farin ciki da abin da na bayyana, da abin da na yi barna." Kuma abin da ka fi sani game da ni, kai ne na farko, kuma kai ne bayin Allah, babu wani abin bauta sai kai. ”
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana tsayuwa don sallah, daya daga cikin abubuwan karshe da ya fada tsakanin tashahud da tasleem shi ne: "Ya Allah, ka gafarta mini abin da na aikata," na sharri, da "abin da na jinkirta", na aikinsa, wato: duk abin da ya gafala daga ni, da abin da Na amince, "ma'ana: Na boye," da "abin da na bayyana, da abin da na yi barna", wato: Na wuce iyaka, ina wuce gona da iri kan neman gafara ta hanyar ambaton nau'ikan rashin biyayya, da kuma "kuma abin da kuka fi sani game da ni", wato: zunubai na wanda ban san adadi da hukunci ba, "Kai ne babba", Wato, wasu daga cikin bayin zuwa gare ku ta hanyar sasanta biyayya, "kuma ku ne baya", wato: ga wasun su ta hanyar barin cin nasara ko kuma kai ne wanda aka sallama ga wanda kake so a sahun kamala, kuma kai ne koma baya ga wanda kake so daga madaukakiyar al'amura zuwa ga masu hankali, "babu wani abin bauta sai kai."

Madogara

بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، تأليف: سليم الهلالي، دار ابن الجوزي. رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين، للإمام أبي زكريا النووي، تحقيق د. ماهر الفحل، دار ابن كثير- دمشق، الطبعة الأولى، 1428هـ. صحيح مسلم، للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبدالباقي، دار عالم الكتب، الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ. مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، تأليف ملا علي القاري، تحقيق صدقي العطار، دار الفكر، بيروت، الطبعة الأولى، 1412هـ. نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة، بيروت، الطبعة الرابعة عشر، 1407هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ka ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai Yake ba Shi da abokin tarayya, Allah ne Mafi girma Mai girma, godiya ta tabbata ga Allah mai yawa, tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, babu dabara babu karfi sai ga Allah Mabuwayi Gwani

عَنْ سَعْدٍ رضي الله عنها قَالَ: جَاءَ أَعْرَابِيٌّ إِلَى رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: عَلِّمْنِي كَلَامًا أَقُولُهُ، قَالَ: «قُلْ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، اللهُ أَكْبَرُ كَبِيرًا، وَالْحَمْدُ لِلَّهِ كَثِيرًا، سُبْحَانَ اللهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ، لَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللهِ الْعَزِيزِ الْحَكِيمِ» قَالَ: فَهَؤُلَاءِ لِرَبِّي، فَمَا لِي؟ قَالَ: «قُلْ: اللهُمَّ اغْفِرْ لِي وَارْحَمْنِي وَاهْدِنِي وَارْزُقْنِي».
Daga Sa'ad - Allah Ya yarda da su - ya ce: Wani balaraben kauye ya zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ka sanar maganar da zan fada, ya ce: "Ka ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai Yake ba Shi da abokin tarayya, Allah ne Mafi girma Mai girma, godiya ta tabbata ga Allah mai yawa, tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, babu dabara babu karfi sai ga Allah Mabuwayi Gwani" sai ya ce: Wadannan na Ubangijina ne, to ni me gareni? ya ce: "Ka ce: Ya Allah Ka gafarta mini Ka ji kaina Ka shiryar dani Ka azurtani".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Wani mutum daga mazauna kauye ya tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar da shi wani zikirin da zai fade shi, Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ka ce: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai yake ba da abokin tarayya" ya fara da shahada ta tauhidi, ma'anarta babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, "Allah ne Mafi girma Mai girma" Wato: Allah ne Mafi girma daga kowanne abu kuma Mafi girma, "Godiya ta tabbata ga Allah mai yawa" Wato: Godiya ta tabbata ga Allah mai yawa, ga siffofinSa da ayyukanSa da ni'imominSa wadanda ba'a iya lissafe su, "Tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai" Wato: Ya tsarkaka Ya tsarkaka daga tawaya, "Babu dabara babu karfi sai ga Allah Ubangiji Mabuwayi Gwani" Wato: Babu dabara ta canza wa daga wani hali zuwa wani halin sai ga Allah da taimakonSa da gamkatar dinSa, sai mutumin ya ce: Wadannan kalmomin sun tabbata ga Ubanigijina dan ambatonSa da girmamaShi, to ni meye gareni na addu'a ga kaina? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ka ce: "Ya Allah Ka gafarta mini" Da shafe munanan ayyuka da suturta su, "Ka jikaina" Ta hanyar sadar da abubuwan amfani da maslahohi na Addini da duniya gareni, "Ka shiryr da ni" ga mafi kyawun halaye kuma zuwa ga hanya mikakkiya, "Ka azirtani" Dukiya ta halal da lafiya da dukkanin alheri da lafiya.

Fa’idoji
  1. Kwadaitarwa akan anbaton Allah da hailala da kabbara da tahmidi da tasbihi.
  2. An so anbaton Allah da yabo gareShi kafin fara addu'a.
  3. Anso addu'ar mutum da mafi tsarkakan addu'o'i, da kuma abinda aka ciro wanda a cikinsa akwai tattaro alherin duniya da lahira. Kuma yana da damar addu'a da abinda ya so.
  4. Yana kamata ga bawa ya yi kwadayi akan neman ilimin abinda zai amfanar da shi a duniya da lahira.
  5. Kwadaitarwa akan neman gafara da rahama da arziki, su ne matattarar alheri.
  6. Tausayinsa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi akan ilmantar da al'ummarsa abinda zai amfanar da su.
  7. An ambaci rahama bayan gafara dan tsarkakewa ta cika, gafara ita ce suturta zunubai da shafesu da nisanta daga wuta, rahama kuwa ita ce sadar da alherai da shiga aljanna, wannan shi ne rabo mai girma.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2072) (2696). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 498). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 972). مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي القاري (4/ 1606).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com