عَنْ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: أَنَّهُ جَاءَ إِلَى الحَجَرِ الأَسْوَدِ فَقَبَّلَهُ، فَقَالَ: إِنِّي أَعْلَمُ أَنَّكَ حَجَرٌ، لاَ تَضُرُّ وَلاَ تَنْفَعُ، وَلَوْلاَ أَنِّي رَأَيْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُقَبِّلُكَ مَا قَبَّلْتُكَ.
Daga Umar - Allah ya yarda da shi -: Cewa shi ya zo wurin Hajarul Aswad (Baƙin dutse) sai ya sumbace shi, sai ya ce: Lallai ni nasan cewa kai dutse ne, baka cutarwa kuma baka anfanarwa, da badan cewa ni naga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana sunbatarka ba da ban sunbaceka ba.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Sarkin muminai Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya zo wajen Hajarul Aswad a kusurwar Ka'aba sai ya sunbace shi, sai ya ce: Lallai ni nasan cewa kai dutse ne, baka cutarwa kuma baka anfanarwa, da badan cewa ni na ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana sunbatarka ba da ban sunbaceka ba.
Fa’idoji
- Halaccin sunbatar Hajarul Aswad ga masu ɗawafi lokacin da suka yi daura da shi, idan zai yi wu kuma cikin sauƙi.
- Abin nufi daga sunbatar Hajaraul Aswad, shi ne bin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Nawawi ya ce: Ma'anarsa cewa babu wani iko gare shi akan anfanarwa ko cutarwa, kuma cewa shi dutse ne abin halitta kamar ragowar halittun da basa cutarwa kuma basa anfanarwa, kuma (sayyadina) Umar ya yaɗa wannan ne a lokacin Mausim (Hajji); dan ya shaida waa kasashe, kuma ma'abota Mausim (Hajji) mabanbantan ƙasashe su kiyaye.
- Ibadu a tsaye suke (ababen shara'antawa ne daga Allah da ManzonSa kadai); ba'a shara'anta wani abu na ibada sai abinda Allah da ManzonSa suka shara'anta.
- Idan ibada ta inganta za’a yi aiki da ita koda ba'asan hikimarta ba; domin cewa rikon da mutane suka yi da umarni da kuma biyayyarsu a kan tsayuwa da ita yana daga hikimomi ababen nufi.
- Hani daga sunbatar abinda shari'a ba ta zo da sunbatarsa ba ta hanyar bauta na duwatsu da wasunsu.
Madogara
صحيح البخاري (2/ 149) (1597).
صحيح مسلم (2/ 925) (1270).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص394).
تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (3/ 527).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عبد الله بن عباس رضي الله عنهما قال: قَدِم عُيَينَة بن حِصنٍ، فَنزَل على ابنِ أَخِيه الحُرِّ بن قَيسٍ، وكان من النَّفَر الذين يُدنِيهِم عمر رضي الله عنه ، وكان القُرَّاء أصحاب مَجلِس عُمر رضي الله عنه ومُشاوَرَتِه كُهُولا كانوا أو شُبَّانًا، فقال عيينة لابن أَخِيه: يَا ابن أخي، لك وَجْه عند هذا الأمير فَاسْتَأذِن لِي عليه، فَاسْتَأذَن فَأَذِن لَه عُمر، فَلَمَّا دَخَل قال: هي يا ابن الخطَّاب، فَوالله مَا تُعطِينَا الجَزْلَ ولا تَحكُمُ فِينَا بِالعَدلِ، فغضب عمر رضي الله عنه حَتَّى هَمَّ أَنْ يُوقِعَ بِه، فقال له الحُرُّ: يا أمير المؤمنين، إنَّ الله تعالى قال لِنَبِيِّه صلى الله عليه وسلم : {خذ العفو وأمر بالعرف وأعرض عن الجاهلين}، وإِنَّ هذا مِن الجَاهِلِين، والله مَا جَاوَزَها عُمر حِين تَلاَهَا، وكان وَقَّافًا عند كِتَاب الله تعالى .
Daga Abdullah bn Abbas - Allah ya yarda da shi - wanda ya ce: Ya zo wurin Ayaynah bn Husn, sai ya sauka a kan dan dan uwansa al-Hurri bn Qais, kuma yana daga cikin wadanda Umar ya yi Allah wadai da su, kuma masu karanta shi sahabban majalisar Umar ne - Allah ya yarda da shi - kuma an so su Ko kuma wani saurayi, sa'annan Ayina ya ce da dan dan uwansa: Haba, dan dan uwana, kana da fuska da wannan basaraken, don haka ka nemi izini a kansa, don haka na ba shi izini. - Har sai da suka so sa hannu, sai mai 'yanci ya ce masa: Ya Amirul Muminina, Allah Madaukaki ya ce wa Annabinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: {Ka yi afuwa ka yi umarni da al'ada kuma ka kau da kai daga jahilai. Kuma wannan daga jahilai ne, kuma Allah bai ba shi izini ba, kuma ya kasance tsawon rayuwa. Kuma tsayuwa a kan littafin Allah madaukaki.
Buhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Babban sahabi Abdullah bin Abbas - Allah ya yarda da shi - ya ba mu labarin abin da ya faru da Amirul Muminina, Umar bin al-Khattab - yardar Allah ta tabbata a gare shi - lokacin da Uyaynah bn Husn - Allah ya yarda da shi - ya gabatar da shi gareshi, kuma yana daya daga cikin manyan mutanensa, don haka kalaman nasa suka fara watsewa ta hanyar kai hare-hare da tofin Allah tsine, sannan kuma suka hukunta shi. Zarginsa, yana cewa: Ba ku ba mu lu'ulu'u, ko ku yanke mana hukunci da adalci, don haka Umar - Allah ya yarda da shi - ya yi fushi har ya kusan buge shi, amma wasu daga cikin masu karatu, ciki har da dan uwan Ayina, Al-Hur Bin Qais, sun yi magana da Halifa Rashidun, Allah ya yarda da shi: Ya Amirul Muminina, Allah madaukaki ya ce wa annabinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: “Ka yi afuwa, ka umarci al’ada, kuma ka kau da kai daga jahilai.” Kuma wannan daga jahilai ne. Saboda yana tsaye a littafin Allah - yardar Allah ta tabbata a gare shi - kuma ya yarda da shi - kuma ya tsaya bai buge mutumin ba. Ga ayar da aka karanta masa. Wannan ita ce adabin Sahabbai - Allah ya yarda da su - da littafin Allah Karka wuce shi, idan akace musu wannan maganar Allah ce, Ku Tashi tsaye, koma dai menene.
Madogara
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي، ط1، دار ابن الجوزي، الدمام، 1415هـ.
تطريز رياض الصالحين، للشيخ فيصل المبارك، ط1، تحقيق: عبد العزيز بن عبد الله آل حمد، دار العاصمة، الرياض، 1423هـ.
رياض الصالحين للنووي، ط1، تحقيق: ماهر ياسين الفحل، دار ابن كثير، دمشق، بيروت، 1428هـ.
رياض الصالحين، ط4، تحقيق: عصام هادي، وزارة الأوقاف والشؤون الإسلامية القطرية، دار الريان، بيروت، 1428هـ.
كنوز رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين برئاسة حمد بن ناصر العمار، ط1، كنوز إشبيليا، الرياض، 1430هـ.
شرح رياض الصالحين، للشيخ ابن عثيمين، دار الوطن للنشر، الرياض، 1426هـ.
صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422هـ.
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين لمجموعة من الباحثين، ط14، مؤسسة الرسالة، 1407هـ.
تاج العروس من جواهر القاموس، لمحمّد بن محمّد بن عبد الرزّاق الحسيني، الملقّب بمرتضى، الزَّبيدي، تحقيق مجموعة من المحققين، دار الهداية.
الدلائل في غريب الحديث، لقاسم بن ثابت بن حزم العوفي السرقسطي، تحقيق: د. محمد بن عبد الله القناص، الناشر: مكتبة العبيكان، الرياض، الطبعة: الأولى، 1422هـ - 2001م.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن جندب رضي الله عنه قال: سَمِعْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَبْلَ أَنْ يَمُوتَ بِخَمْسٍ وَهُوَ يَقُولُ «إِنِّي أَبْرَأُ إِلَى اللهِ أَنْ يَكُونَ لِي مِنْكُمْ خَلِيلٌ فَإِنَّ اللهَ تَعَالَى قَدِ اتَّخَذَنِي خَلِيلًا كَمَا اتَّخَذَ إِبْرَاهِيمَ خَلِيلًا، وَلَوْ كُنْتُ مُتَّخِذًا مِنْ أُمَّتِي خَلِيلًا لَاتَّخَذْتُ أَبَا بَكْرٍ خَلِيلًا! أَلَا وَإِنَّ مَنْ كَانَ قَبْلَكُمْ كَانُوا يَتَّخِذُونَ قُبُورَ أَنْبِيَائِهِمْ وَصَالِحِيهِمْ مَسَاجِدَ، أَلَا فَلَا تَتَّخِذُوا الْقُبُورَ مَسَاجِدَ! إِنِّي أَنْهَاكُمْ عَنْ ذَلِكَ».
Daga Jundub - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Naji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kafin mutuwarsa da (darare) biyar alhali shi yana cewa: "Lallai ni ina barranta zuwa ga Allah da ya zama ina da badadi daga cikinku, to lallai cewa Allah - Madaukakin sarki - hakika Ya rike ni badadi, kamar yadda Ya riki (Annabi) Ibrahim badadi, da na kasance mai rikon badadi daga al'ummata da na riki Abubakar badadi, ku saurara lallai wadanda suka gabace ku sun kasance suna maida kaburburan Annabawansu da salihansu masallatai, ku saurara kada ku maida kaburbura masallatai, lallai ni ina hanaku hakan".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincinAllah su tabbata a gare shi - ya sanar game da darajarsa a wurin Allah - Madaukain sarki -, kuma cewa ita takai mafi kololuwar darajojin soyayya, kamar yadda (Annabi ) Ibrahim - amincin Allah ya tabbata a gare shi - ya sameta, saboda haka ne ya kore ya zama cewa yana da wani badadi wanin Allah; domin cewa zuciyarsa ta cika da soyayyar Allah - Madaukakin sarki - da girmama Shi da saninsa, to ba ta yalwatuwa ga wani koma bayan Allah. Da a ce yana da wani badadi daga halitta da ya zama sayyidin Abubakar - Allah Ya yarda da shi -. Sannan ya yi gargadi daga ketare iyakar da ta halatta a cikin soyayya kamar yadda Yahudawa da Nasara suka aikata a kaburburan Annabawansu da salihansu har suka maida su alloli na shirka ana bauta musu koma bayan Allah, kuma suka sanya siminti da kayan alatu a kaburburan dake masallatai da guraren ibada, kuma tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana al'ummarsa da su aikata irin aikinsu.
Fa’idoji
- Falalar Sayyidina Abubakar Siddik - Allah ya yarda da shi -, kuma cewa shi ne mafificin sahabbai kuma mafi cancantar mutane da Halifancin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bayan mutuwarsa.
- Lallai cewa gina masallatai akan kaburbura yana daga abubuwanki daga al'ummata da suka gabata.
- Hana maida kaburbura guraren ibada da za'a dinga sallah a wurinsu ko zuwa gare su, kuma ana gina masallatai ko kubbobi akansu, dan gujewa afkawa a cikin shirka saboda hakan.
- Gargadi daga zurfafawa a salihai bayi, domin hakan na kaiwa zuwa shirka.
- Hadarin abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi gargadi yayin da ya karfafa hakan kafin mutuwarsa da darare biyar.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 377) (532).
شرح النووي على مسلم (5/ 13).
الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص188).
الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص172).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنِ الْبَرَاءِ رضي الله عنه: عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُ قَالَ فِي الْأَنْصَارِ: «لَا يُحِبُّهُمْ إِلَّا مُؤْمِنٌ، وَلَا يُبْغِضُهُمْ إِلَّا مُنَافِقٌ، مَنْ أَحَبَّهُمْ أَحَبَّهُ اللهُ وَمَنْ أَبْغَضَهُمْ أَبْغَضَهُ اللهُ».
Daga Al-Barra - Allah Ya yarda da shi -: Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi cewa shi ya fada a sha'anin mutane Madina: "Ba mai sonsu sai mumini, kuma babu mai kinsu sai munafiki, wanda ya so su Allah zai so shi, wanda ya ki su Allah Zai ki shi".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa son mutanen Ansar daga mutanen Madina, alama ce akan cikar imani; wannan dan rigayarsu a taimakon Musulunci da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da kokari akan tarbar musulmai, da bada dukiyoyinsu da rayukansu a tafarkin Allah, kuma cewa kinsu alama ce ta munafunci. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana cewa wanda ya so mutanen Madina Allah Zai so shi, wanda ya ki su Allah Zai ki shi.
Fa’idoji
- A cikinsa akwai daraja mai girma ga mutanen Madina, son su alamce akan imani da kubuta daga munafunci.
- Son masoya Allah da taimakonsu sababine na samun son Allah ga bawa.
- Falalar wadanda suka rigaya na farko a cikin Musulunci.
Madogara
صحيح البخاري (5/ 32) (3783).
صحيح مسلم (1/ 85) (75).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 447).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص257).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (6/ 258).
شرح النووي على مسلم (2/ 63).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين (1/ 350).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ يَوْمَ خَيْبَرَ: «لَأُعْطِيَنَّ هَذِهِ الرَّايَةَ رَجُلًا يُحِبُّ اللهَ وَرَسُولَهُ، يَفْتَحُ اللهُ عَلَى يَدَيْهِ» قَالَ عُمَرُ بْنُ الْخَطَّابِ: مَا أَحْبَبْتُ الْإِمَارَةَ إِلَّا يَوْمَئِذٍ، قَالَ فَتَسَاوَرْتُ لَهَا رَجَاءَ أَنْ أُدْعَى لَهَا، قَالَ فَدَعَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلِيَّ بْنَ أَبِي طَالِبٍ، فَأَعْطَاهُ إِيَّاهَا، وَقَالَ: «امْشِ، وَلَا تَلْتَفِتْ، حَتَّى يَفْتَحَ اللهُ عَلَيْكَ» قَالَ فَسَارَ عَلِيٌّ شَيْئًا ثُمَّ وَقَفَ وَلَمْ يَلْتَفِتْ، فَصَرَخَ: يَا رَسُولَ اللهِ، عَلَى مَاذَا أُقَاتِلُ النَّاسَ؟ قَالَ: «قَاتِلْهُمْ حَتَّى يَشْهَدُوا أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ، فَإِذَا فَعَلُوا ذَلِكَ فَقَدْ مَنَعُوا مِنْكَ دِمَاءَهُمْ وَأَمْوَالَهُمْ، إِلَّا بِحَقِّهَا وَحِسَابُهُمْ عَلَى اللهِ».
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya faɗa a ranar Khaibara: "Zan bada wannan tutar ga wani mutum mai ƙaunar Allah da ManzonSa, Allah zai yi buɗi ta hannayensa" Umar ɗan Khaɗɗab ya ce: Ban so shugabanci ba sai wannan ranar, ya ce sai na yi ɗigirgire saboda ita dan kwaɗayin a kirawoni gareta, ya ce: Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kira Aliyu bin Abi Ɗalib - Allah Ya yarda da shi -, sai ya ba shi ita, ya ce: "Ka tafi, kada ka juya, har sai Allah Ya buɗe maka." Ya ce sai Aliyu ya tafi ɗan wani taku, sannan ya tsaya bai juya ba, sai ya yi magana: Ya Manzon Allah, akan me zan yaƙi mutane? Ya ce: "Ka yaƙesu har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammad manzon Allah ne, idan suka aikta hakan to hakika sun hana jinanensu da dukiyoyinsu daga gareni sai da hakkinsu kuma hisabinsu yana ga Allah".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bada labarin samun nasarar musulmai a gobe akan Yahudawan Khaibara wani gari ne kusa da Madina, hakan ta hannun wani mutum da zai ba shi tuta, shi ne wata alama wacce runduna suke riƙonta dan alama gareta, wannan mutumin daga siffofinsa cewa shi yana son Allah da ManzonSa, kuma Allah da ManzonSa suna sonsa.
Hakika Uamr ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ambaci cewa shi bai taɓa son shugabanci ba kuma ya zama shi ne abin nufi sai a wannan ranar; dan kwaɗayin abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗe shi na son Allah da ManzonSa ya same shi , kuma Umar - Allah Ya yarda da shi ya daga kansa dan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gan shi dan kwaɗayin a kira shi gareta, da kuma kwaɗayi a karɓar waccan tutar.
Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kira Ali ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - sai ya bashi tutar, kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarce shi ya tafi da rundunar, kuma kada ya juya baya a yaƙi bayan haɗuwa da maƙiya dan hutu ko tsayawa ko sulhu har sai Allah Ya buɗe masa waɗannan katangun da nasara da kuma rinjaye.
Sai Aliyu - Allah Ya yarda da shi - ya tafi, sannan ya tsaya sai dai bai juya ba; dan kada ya saɓa umarnin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai Ali - Allah Ya yarda da shi - ya ɗaga muryarsa: Ya Manzon Allah, akan me zan yaki mutane?
Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ka yaƙesu har sai sun shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, idan sun amsa, sun shiga Musulunci; to haƙiƙa sun hana jinanensu da dukiyoyinsu daga gareka kuma sun haramta daga gareka, sai dai da haƙƙinsu, yana nufin sai dai idan sun aikata laifi ko jinayar da zasu cancanci kisa akansu da wajabcin hukunce-hukuncen Musulunci, kuma hisabinsu yana ga Allah.
Fa’idoji
- Sahabbai sun kasance suna ƙin shugabanci dan abinda ke cikinsa na nauyi mai girman gaske.
- Halaccin mike wuya da dagowa dan wani al'amarin da alherinsa yake da ƙarfi.
- Fadakarwar shugaba ga jagoran runduna a yanayin tasarrufi a fagen yaƙi.
- Lazimtuwar sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga wasiyyoyinsa da kuma gaggawa ga zartar da su.
- Wanda wani abu ya rikitar da shi a cikin abinda aka neme shi da shi to ya yi tambaya game da shi.
- Daga dalilan Annabcinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bada labarinsa da nasara akan Yahudawa, inda ya bada labari game da buɗe Khaibara sai ya zama kamar yanda ya bada labarin.
- Kwaɗaitarwa akan fuskanta da gaggawa zuwa abinda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da shi.
- Ba ya halatta kashe wanda ya furta kalmar shahada biyu sai dai idan abinda yake wajabta kisa ya bayyana daga gare shi.
- Hukunce-hukuncen Musulunci suna gudana ne akan abinda yake bayyana daga mutane Allah kuma Yana jiɓintar abinda suka ɓoye.
- Abin nufi mafi girma daga yaƙi shi ne shigar mutane cikin Musulunci.
Madogara
صحيح مسلم (4/ 1871) (2405).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 127).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 45).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 174).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي سليمان خالد بن الوليد رضي الله عنه قال: لقد انقطعت في يدي يوم مُؤْتَةَ تسعة أسياف، فما بقي في يدي إلا صَفِيحَةٌ يمانية.
Daga Abu Sulaiman Bn Khalid Bn Walid -Allah ya yarda da sh- ya ce:Haqiqa a Hannuna Takubba Tara sun karye a ranar yaqin Mu'ata, babu abunda ya ragu a Hannuna sai Takobin Yamani
Buhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
صحيح البخاري، أبو عبد الله محمد بن إسماعيل بن إبراهيم بن المغيرة الجعفي البخاري، تحقيق محمد زهير بن ناصر الناصر -الناشر : دار طوق النجاة -الطبعة : الأولى 1422هـ.
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، تأليف سليم بن عيد الهلالي، دار ابن الجوزي.
رياض الصالحين، تأليف محيي الدين النووي، تحقيق عصام موسى هادي، ط: وزارة الأوقاف والشؤون الإسلامية بدولة قطر.
شرح رياض الصالحين، المؤلف : محمد بن صالح بن محمد العثيمين.
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، تأليف د/ مصطفى الخن، د/ مصطفى البغا، محيي الدين مستو، علي الشربجي، محمد أمين لطفي، مؤسسة الرسالة، ط:الرابعة عشر1407.
دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين، تأليف محمد علي بن محمد علان.
كنوز رياض الصالحين، تأليف حمد بن ناصر العمار، دار كنوز إشبيليا، ط1-1430ه.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عائشة قالت: كان رسولُ الله صلى الله عليه وسلم مُضْطجِعًا في بيتي، كاشفًا عن فَخِذَيْه، أو ساقَيْه، فاسْتأذَن أبو بكر فأذِنَ له، وهو على تلك الحال، فتحدَّثَ، ثم اسْتأذَن عُمر، فأذِن له، وهو كذلك، فتحدَّث، ثم اسْتأذَن عثمان، فجلس رسول الله صلى الله عليه وسلم ، وسوَّى ثِيابه -قال محمد: ولا أقول ذلك في يوم واحد- فَدَخَل فتحدَّث، فلمَّا خرج قالت عائشة: دخل أبو بكر فلم تَهْتَشَّ له ولم تُبَالِه، ثم دخل عمر فلم تَهْتَشَّ له ولم تُبَالِه، ثم دخل عثمان فجلستَ وسوَّيتَ ثيابك فقال: «ألا أسْتَحِي من رجل تَسْتَحِي منه الملائكةُ».
A kan A’isha ta ce: Manzon Allah - SAW- yana kwance a cikin gidana, yana bayyana cinyarsa ko kafafunsa, don haka Abubakar ya ba da izininsa kuma ya ba shi izini, kuma yana kamar wannan, sannan ya yi magana, sannan Umar ya tambaya, don haka ya ba shi izini, kuma haka ne, sannan ya yi magana.Uthman ya nemi izini, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya zauna ya daidaita tufafinsa - Muhammad ya ce: Ba na ce haka a rana daya ba - don haka ya shiga ya yi magana, kuma a lokacin da zai tafi, sai A'isha ta ce: Abubakar ya shiga kuma ba ta kula shi ba, kai kuma ba ka damu ba, to Umar ya shiga kuma bai ji ba tsoratar da shi kuma ba ta kula shi ba, sannan Uthman ya shiga, sai ka zauna ka daidaita tufafinka. Ya ce: "Shin ba zan jin kunyar wani mutum da mala'iku za su ji kunya daga gare shi ba".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
A’isha - Allah ya yarda da ita - ta ruwaito cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana kwance a gidanta, yana bayyana cinyarsa ko kafafunsa, don haka Abubakar ya nemi izinin shiga sai ya ba shi izini, alhali yana cikin wannan yanayin kwance da cinyoyinsa ko kafafuwansa a bayyane - Allah ya kara tsira da aminci a gare shi - Don haka Abubakar ya yi magana da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai Omar ya nemi izininsa , don haka ya bashi izini, sai ya kasance haka, to ya yi magana, sai Uthman ya nemi izinin shiga, don haka Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya mike a zaune, ya gyara tufafinsa ya rufe cinyoyinsa ko Kafafuwansa, sannan ya bashi izinin shiga, sai ya shiga yayi magana, kuma lokacin da zai fita, sai A'isha ta ce: Abubakar ya shiga, kuma ba ta ji dadi ba kuma ta damu da shigarta, sai Omar ya shigo, amma ku ba farin ciki da sha'awar shigarsa, sai Uthman ya shiga, don haka sai ku daidaita a cikin zamanku kuma ku daidaita tufafinku kuma ku rufe cinyoyinku ko ƙafafunku? Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Shin ba zan ji kunyar mutumin da mala'iku ke jin kunyar sa ba" ma'ana: Mala'ikun masu rahama suna jin kunyar Usman, to yaya ba zan iya ba kunyar shi? Wannan hadisin baya gamsuwa cewa cinya ba 'awrah bane. Saboda bangaren da babu shi a cikin hadisin akwai shakku shin kafafu ne ko cinyoyinta, ba lallai ba ne ya tabbata cewa cinyar ta halatta a bayyana. Kuma saboda hadisan da aka bankado cinya a ciki sun fito ne daga aikin Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ba daga maganganun sa ba, kuma samari sahabbai ne suka rawaito shi .. Amma hadisan da aka bankado cinya a cikinsu. , ya fi hankali, kuma manyan sahabbai ne suka rawaito shi, kuma daga maganarsa ne, kuma lafazin yana fifita aiki, kuma aikin yana da damar Kuma saboda tona asiri ya zo da sirrin mutum ba janar a kowane wuri ba, kuma fadin cewa cinya 'awrah fatawa ce daga Kwamitin din din.
Madogara
- صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، نشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.
- إكمال المعلم بفوائد مسلم لعياض بن موسى بن عياض اليحصبي السبتي، المحقق: الدكتور يحيى إسماعيل، الناشر: دار الوفاء للطباعة والنشر والتوزيع، مصر، الطبعة: الأولى، 1419 هـ - 1998 م.
- المنهاج شرح صحيح مسلم بن الحجاج، للنووي، نشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت، الطبعة: الثانية، 1392ه.
- الصحاح تاج اللغة وصحاح العربية, أبو نصر إسماعيل بن حماد الجوهري الفارابي, تحقيق: أحمد عبد الغفور عطار, دار العلم للملايين – بيروت, الطبعة: الرابعة 1407 هـ - 1987 م.
- عمدة القاري شرح صحيح البخاري، لمحمود بن أحمد الحنفى بدر الدين العينى، الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.
- التوضيح لشرح الجامع الصحيح, ابن الملقن سراج الدين أبو حفص عمر بن علي الشافعي, ت: دار الفلاح للبحث العلمي وتحقيق التراث, دار النوادر، دمشق – سوريا, الطبعة: الأولى، 1429 هـ - 2008 م.
- فتاوى اللجنة الدائمة - المجموعة الأولى, اللجنة الدائمة للبحوث العلمية والإفتاء, جمع وترتيب: أحمد بن عبد الرزاق الدويش, الناشر: رئاسة إدارة البحوث العلمية والإفتاء - الإدارة العامة للطبع – الرياض.
- فيض القدير شرح الجامع الصغير, زين الدين محمد المدعو بعبد الرؤوف بن تاج العارفين المناوي القاهري، الناشر: المكتبة التجارية الكبرى - مصر, الطبعة: الأولى، 1356.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن ابن عمر رضي الله عنهما ، عن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «هذا الذي تحرَّكَ له العرشُ، وفُتِحَتْ له أبوابُ السماءِ، وشَهِدَه سبعون ألفًا من الملائكة، لقد ضُمَّ ضَمَّةً، ثم فُرِّجَ عنه».
Wannan ne wanda Al'arshi ya girgiza saboda shi, kuma aka buxe masa kofofin Sama, kuma Mala'iku Dubu Saba'in suka raka shi, haqiqa an mastse Matsewa, sannan aka sake shi
Al-Nasa'i Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
- السنن الصغرى للنسائي "المجتبى"، تحقيق: عبد الفتاح أبو غدة، نشر: مكتب المطبوعات الإسلامية – حلب، الطبعة: الثانية، 1406ه – 1986م.
- مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي بن سلطان الملا الهروي القاري، الناشر: دار الفكر، بيروت – لبنان، الطبعة: الأولى، 1422هـ - 2002م.
- صحيح الجامع الصغير وزياداته، للألباني، نشر: المكتب الإسلامي.
- شرح سنن النسائي المسمى «ذخيرة العقبى في شرح المجتبى»، المؤلف: محمد بن علي بن آدم بن موسى الإثيوبي الوَلَّوِي، الناشر: دار المعراج الدولية للنشر - دار آل بروم للنشر والتوزيع, الطبعة الأولى, 1416- 1424.
- حاشية السندي على سنن النسائي (مطبوع مع السنن), محمد بن عبد الهادي التتوي، أبو الحسن، نور الدين السندي, مكتب المطبوعات الإسلامية – حلب, الطبعة: الثانية، 1406 – 1986م.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com