Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Sa'ad ya zo sai Manzon Allah SAW ya ce: Wannan Kawu na ne kowane Mutum ya nuna mun kawunsa

عن جابر بن عبد الله رضي الله عنهما ، قال: أقبل سعد، فقال النبي صلى الله عليه وسلم : «هذا خالي فليُرِني امرؤٌ خالَه».
Daga Jabir Allah ya yarda da su ya ce: Sa'ad ya zo sai Manzon Allah SAW ya ce: Wannan Kawu na ne kowane Mutum ya nuna mun kawunsa"
Al-Tirmithi Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Sa'ad Bn Abi Waqqas -Allah ya yarda da shi- ya zo Majalisin Annabi SAW yayin da Manzon Allah SAW ya ganshi sai ya ce: Wannan Kawu na ne kuma ina Alfahari da shi, to kowane Muyum ya nuna mun Kawun sa; don ya bayyana a lokacin babu wanda yake da Kawu kamar kawuna, kuma Sa'ad ya kasance daga Qabilar Bani Zahra ne, kuma Mahaifiyar Manzon Allah SAw Amina ita daga Bani Zahra ta ke, kuma shi Xanuwanta ne, kuma 'Yan Uwan Uwa Kawunnani ne.

Madogara

سنن الترمذي، محمد بن عيسى الترمذي، تحقيق وتعليق: أحمد محمد شاكر، ومحمد فؤاد عبد الباقي، وإبراهيم عطوة عوض، شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي الحلبي، مصر، الطبعة: الثانية، 1395هـ، 1975م. صحيح الجامع الصغير وزيادته، محمد ناصر الدين الألباني، المكتب الإسلامي، بيروت، الطبعة: الثالثة 1408هـ. تحفة الأحوذي بشرح جامع الترمذي، محمد عبد الرحمن بن عبد الرحيم المباركفورى، دار الكتب العلمية، بيروت.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALAR SAHABBAI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com