Duk mutumin da ya halarci (yaƙin) Badar da Hudaibiyya ba zai shiga wuta ba
عن جابر رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «لن يدخلَ النارَ رجلٌ شَهِد بدرًا والحُدَيْبِيَة».
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Duk mutumin da ya halarci (yaƙin) Badar da Hudaibiyya ba zai shiga wuta ba".
Ahmad ne ya ruwaito shi kuma asalinsa yana cikin Sahih MuslimDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa duk wanda ya halarci yaƙin Badar wanda aka yi a cikin shekara ta biyu da hijira yana mai yaƙi tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, haka nan wanda ya halarci Sulhun Hudaibiyya, kuma a cikinsa ne aka yi Bai'atir Ridwan wacce aka yi a cikin shekara ta shida da hijira ba zai shiga wuta ba.
Fa’idoji
A cikinsa akwai falalar ma'abota (yaƙin) Badar da Hudaibiyya, kuma su ba zasu shiga wuta ba.
Bayanin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Zai lamunce musu abinda ake bin su, kuma Zai datar da su ga mutuwa akan imani, kuma Zai shigar da su aljanna ba tare da rigayar azabar wuta ba, wannan kuma falalar Allah ce da yake ba wa wanda Yake so, Allah Ma'abocin falala ne Mai girma.
Madogara
صحيح مسلم (4/ 1942) (2495) .
مسند أحمد (23/ 410) (15262).
المصباح المنير في غريب الشرح الكبير، لأحمد الفيومي (1/ 123).
فيض القدير شرح الجامع الصغير، للمناوي (5/ 302).
المنهاج شرح صحيح مسلم بن الحجاج، للنووي (16/ 57).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com