Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lallai ni nasan cewa kai dutse ne, baka cutarwa kuma baka anfanarwa, da badan cewa ni naga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana sunbatarka ba da ban sunbaceka ba

عَنْ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: أَنَّهُ جَاءَ إِلَى الحَجَرِ الأَسْوَدِ فَقَبَّلَهُ، فَقَالَ: إِنِّي أَعْلَمُ أَنَّكَ حَجَرٌ، لاَ تَضُرُّ وَلاَ تَنْفَعُ، وَلَوْلاَ أَنِّي رَأَيْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُقَبِّلُكَ مَا قَبَّلْتُكَ.
Daga Umar - Allah ya yarda da shi -: Cewa shi ya zo wurin Hajarul Aswad (Baƙin dutse) sai ya sumbace shi, sai ya ce: Lallai ni nasan cewa kai dutse ne, baka cutarwa kuma baka anfanarwa, da badan cewa ni naga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana sunbatarka ba da ban sunbaceka ba.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Sarkin muminai Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya zo wajen Hajarul Aswad a kusurwar Ka'aba sai ya sunbace shi, sai ya ce: Lallai ni nasan cewa kai dutse ne, baka cutarwa kuma baka anfanarwa, da badan cewa ni na ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana sunbatarka ba da ban sunbaceka ba.

Fa’idoji
  1. Halaccin sunbatar Hajarul Aswad ga masu ɗawafi lokacin da suka yi daura da shi, idan zai yi wu kuma cikin sauƙi.
  2. Abin nufi daga sunbatar Hajaraul Aswad, shi ne bin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  3. Nawawi ya ce: Ma'anarsa cewa babu wani iko gare shi akan anfanarwa ko cutarwa, kuma cewa shi dutse ne abin halitta kamar ragowar halittun da basa cutarwa kuma basa anfanarwa, kuma (sayyadina) Umar ya yaɗa wannan ne a lokacin Mausim (Hajji); dan ya shaida waa kasashe, kuma ma'abota Mausim (Hajji) mabanbantan ƙasashe su kiyaye.
  4. Ibadu a tsaye suke (ababen shara'antawa ne daga Allah da ManzonSa kadai); ba'a shara'anta wani abu na ibada sai abinda Allah da ManzonSa suka shara'anta.
  5. Idan ibada ta inganta za’a yi aiki da ita koda ba'asan hikimarta ba; domin cewa rikon da mutane suka yi da umarni da kuma biyayyarsu a kan tsayuwa da ita yana daga hikimomi ababen nufi.
  6. Hani daga sunbatar abinda shari'a ba ta zo da sunbatarsa ba ta hanyar bauta na duwatsu da wasunsu.
Madogara

صحيح البخاري (2/ 149) (1597). صحيح مسلم (2/ 925) (1270). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص394). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (3/ 527).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALAR SAHABBAI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com