Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya rasa Sabitu Dan Ƙais - Allah Ya yarda da shi - ya yi tambaya game da shi (ya yi cigiyarsa), sai wani mutum ya ce: Ni zan samo maka labarinsa, da dalilin fakuwarsa, sai ya tafi wurinsa sai ya same shi yana cikin baƙin ciki yana mai sunkuyar da kansa a gidansa, sai ya tambaye shi : Meke damunka? sai Sabitu ya ba shi labarin abin da ke tare da shi na sharri; domin cewa ya kasance yana ɗaga sautinsa sama da sautin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma haƙiƙa Allah Ya yi alkawarin narko daga aikata hakan da ɓacin aikinsa, kuma cewa shi yana daga 'yan wuta! Sai mutumin ya dawo zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya sanar da shi da hakan, sai Annabi - tsaira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umarce shi ya koma wa Sabitu ɗan Ƙais ya yi masa albishir da cewa shi ba ya daga 'yan wuta, sai dai yana daga 'yan aljanna, domin cewa ya kasance mai babbar murya ne a halitta, domin shi ya kasance mai huɗubar Manzon Allah ne - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -. kuma mai yi wa mutanen Madina huɗuba.
- Bayanin falalar Sabitu ɗan Ƙais - Allah Ya yarda da shi - kuma cewa shi yana daga cikin 'yan aljanna.
- Damuwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da sahabbai da bibiyarsa garesu.
- Tsoron sahabbai - Allah Ya yarda da su - game da ɓacin aikinsu.
- Wajabcin ladabi wajen yi masa magana - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a rayuwarsa, da ƙanƙan da muryoyi a lokacin jin sunnarsa bayan ya rasu.
صحيح البخاري (4/ 201) (3613)، صحيح مسلم (1/ 110) (119)، فتح الباري لابن حجر (6/ 620)، عمدة القاري شرح صحيح البخاري (16/ 146)، النهاية في غريب الحديث والأثر (ص 183).