Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

ANNABIMMU MUHAMMAD TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI

Hadisai 18

Na rantse da wanda ran Muhammad yake a hannunSa , babu wani daya daga wannan al'ummar da zai ji ni Bayahude ne ko Kirista, sannan ya mutu bai yi imani da abinda aka aikoni da shi ba sai ya zama cikin 'yan wuta

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنْ رَسُولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم أنه قال: «وَالَّذِي نَفْسُ مُحَمَّدٍ بِيَدِهِ لَا يَسْمَعُ بِي أَحَدٌ مِنْ هَذِهِ الْأُمَّةِ يَهُودِيٌّ وَلَا نَصْرَانِيٌّ، ثُمَّ يَمُوتُ وَلَمْ يُؤْمِنْ بِالَّذِي أُرْسِلْتُ بِهِ إِلَّا كَانَ مِنْ أَصْحَابِ النَّارِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Na rantse da wanda ran Muhammad yake a hannunSa , babu wani daya daga wannan al'ummar da zai ji ni Bayahude ne ko Kirista, sannan ya mutu bai yi imani da abinda aka aikoni da shi ba sai ya zama cikin 'yan wuta".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana rantsuwa da Allah cewa wani daya daga wannan al'ummar ba zai ji shi ba, Bayahude ne ko Kirista ko waninsu (ba zai ji) kiran Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya isa zuwa gare shi ba, sannan ya mutu bai yi imani da shi ba sai ya zama daga 'yan wuta yana madawwami a cikinta har abada.

Fa’idoji
  1. Gamewar sakon Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - zuwa dukkanin halittu, da wajabcin binsa, da shari'arsa ta shafe dukkanin shari'o'i.
  2. Wanda ya kafirce da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata aagre shi - ikirarins na imani da waninsa daga Annabawa - tsira da aminci ya tabbata agare su baki daya - ba zai amfanar da shi da komai ba.
  3. Wanda bai ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba, kuma sakon musulunci bai isa zuwa gare shi ba to shi yana da uzuri, al'amarinsa a lahira yana ga Allah - Madaukakin sarki -.
  4. Amfanuwa da musulunci yana tabbata koda kafin mutuwa ne, koda a halin tsananin rashin lafiya ne, muddin dai rai bai kai makogwaro ba.
  5. Inganta Addinin kafirai - daga cikinsu akwai yahudawa da kiristoci - kafirci ne.
  6. Ambaton yahudawa da kiristoci - a cikin hadisin - dan fadakarwa ne akan wasunsu; hakan domin cewa yahudawa da kiristoci suna da littafi, idan hakan ya zama sha'aninsu, to wasunsu daga wadanda ba su da littafi ya fi cancanta, dukkaninsu shiga Addininsa da biyayya gareshi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zama dole akansu.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 134) (153). شرح النووي على مسلم (2/ 186). الإفصاح عن معاني الصحاح، لابن هبيرة (8/ 192). طرح التثريب في شرح التقريب، لعبد الرحيم العراقي (7/ 159).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Sai muka ce: Kai ne shugabanmu, sai ya ce: "Shugaba Shi ne Allah", muka ce: Mafificinmu a fifiko, kuma mafi girmanmu a kyauta, sai ya ce: "Ku fadi maganarku, ko wani bangare na maganarku, kada Shaidan ya yi amfani daku

عَن عَبدِ الله بنِ الشِّخِّير رضي الله عنه قَالَ: انْطَلَقْتُ في وَفدِ بَنِي عَامِرٍ إِلى رَسُولِ الله صلى الله عليه وسلم، فَقُلنا: أَنتَ سيّدُنَا، فقال: «السَّيدُ اللهُ»، قُلنا: وَأَفْضَلُنا فَضْلاً، وأعظَمُنا طَوْلاً، فقال: «قُولُوا بِقَولِكُم، أَو بَعضِ قولِكُم، وَلَا يَسْتَجْرِيَنَّكُم الشَّيطَانُ».
Daga Abdullahi Dan Shikkhir - Allah Ya yarda dashi - ya ce: Na tafi a cikin jama'ar Banu Amir zuwa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, Sai muka ce: Kai ne shugabanmu, sai ya ce: "Shugaba Shi ne Allah", muka ce: Mafificinmu a fifiko, kuma mafi girmanmu a kyauta, sai ya ce: "Ku fadi maganarku, ko wani bangare na maganarku, kada Shaidan ya yi amfani daku".
Abu Dawud ne ya Rawaito shi da Kuma AhmadDarajaIngantacce ne
Sharhi

Wasu jama'a suka zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, lokacin da suka iso wurinsa sai suka fadi - suna masu yabonsa - wasu daga cikin kalmomin da tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ki su, sai suka ce ; "Kai ne shugabanmu", sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Shugaba (Shi ne) Allah" Cikakken shugabanci nasa ne akan halittarSa su bayinSa ne. Suka ce : Kai ne "Mafificinmu a fifiko" kuma mafi daukakarmu a daraja da daukaka. kuma kaine "Mafi girmanmu a kyauta" mafi yawaitawarmu a kyauta da daukaka da daraja. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nuna musu su fadi maganarsu ta al'ada kada su kallafawa kansu lafazai, kuma kada Shaidan ya Ja su zuwa wuce gona da iri da kanbawar da zata afkar cikin abinda aka haramta na shirka da hanyoyinta.

Fa’idoji
  1. Girman darajar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a rayukan sahabbansa da girmamawarsu gare shi .
  2. Hani daga matsama kai a lafazi, da takaituwa a magana.
  3. Kariya ga Tauhidi daga abinda zai bata shi na maganganu da ayyuka.
  4. Hani daga wuce gona da iri a yabo, shi yana daga hanyoyin Shaidan,
  5. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne shugaban 'ya'yan Adam, abinda ya zo a hadisi shi yana babin kankar da kai ne, kuma a babin tsoro garesu kar su fada a wuce iyaka.
Madogara

سنن أبي داود (7/ 184) (4806). مسند أحمد (26/ 234) (16307). الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص424). الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص472). مشكاة المصابيح، للألباني مشكاة المصابيح (3/ 1373).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Daga kanka ka fada za'a ji, ka roka a baka, ka nemi ceto za'a baka ceton

عن أنس بن مالك رضي الله عنه مرفوعاً: أخبر النبي صلى الله عليه وسلم : "أنه يأتي فيسجد لربه ويحمده [لا يبدأ بالشفاعة أولا]، ثم يقال له: "ارفع رأسك وقل يُسمع، وسَلْ تُعط، واشفع تُشفَّع".
Daga Anas Dan Malik - Allah ya yarda da shi - an daga hadisin zuwa ga Annabi, Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi ya bada labari cewa: " shi zai zo y yi sujjada ga Ubangijinsa ya kuma yi godiya [ba da ceto zai fara ba] , sai a ce da shi: " Dago kanka ka fada za'a ji, ka roka a baka, ka nemi ceto za'a baka ceton."
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Manzo mai tsira da amincin Allah zai zo ranar kiyama sai ya yi sujjada ga Allah ya kuma roke shi,sai Allah ya yi masa izini da yin ceto mafi girma, sai Ubangjinsa yace da shi: roki a baka kuma ka nemi ceto a baka, duk bukatarka an karba maka, cetonka kuma an baka

Madogara

1- القول المفيد على كتاب التوحيد، دار ابن الجوزي، المملكة العربية السعودية، الطبعة: الثانية, محرم، 1424ه. 2- صحيح البخاري، المحقق: محمد زهير بن ناصر الناصر، الناشر: دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى، 1422هـ. 3- صحيح مسلم، المحقق: محمد فؤاد عبد الباقي، الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

An bani abubuwa biyar, wadanda ba a baiwa wani daga cikin (Annabawa) a gabani na ba

عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ رضي الله عنهما أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «أُعْطِيتُ خَمْسًا لَمْ يُعْطَهُنَّ أَحَدٌ قَبْلِي: نُصِرْتُ بِالرُّعْبِ مَسِيرَةَ شَهْرٍ، وَجُعِلَتْ لِي الأَرْضُ مَسْجِدًا وَطَهُورًا، فَأَيُّمَا رَجُلٍ مِنْ أُمَّتِي أَدْرَكَتْهُ الصَّلاَةُ فَلْيُصَلِّ، وَأُحِلَّتْ لِي المَغَانِمُ، وَلَمْ تَحِلَّ لِأَحَدٍ قَبْلِي، وَأُعْطِيتُ الشَّفَاعَةَ، وَكَانَ النَّبِيُّ يُبْعَثُ إِلَى قَوْمِهِ خَاصَّةً وَبُعِثْتُ إِلَى النَّاسِ عَامَّةً».
Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "An bani abubuwa biyar, wadanda ba a baiwa wani daga cikin (Annabawa) a gabani na ba : An bani cin nasara ta hanyar tsoro (da ake jefawa abokan gaba) wata daya (gabanin haduwar mu), kuma an sanya mini kasa ta zama wajen yin sallah ta kuma mai tsarkakewa, don haka duk wanda sallah ta riske shi cikin al'umma ta to sai ya yi ta, kuma an halarta min ganima, ba'a taba halartawa wani kafin ni ba, kuma an bani ceto, ya kasance ana aiko Annabi zuwa ga mutanensa kadai , ni kuwa an aiko ni zuwa ga mutane baki daya".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annbai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah Ya ba shi wasu dabi'u uku (wadanda) bai bada su ga wani daga Annabwa a gabnina ba. Na farko: An bani nasara da tsoro da za'a jefa shi a cikin zukatan maƙiyana koda tsakanina da su akwai tafiyar wata. Na biyu: An sanya mana ƙasa ta zama masallacin da zamu dinga sallah a duk inda muke, kuma mai tsarkakewa da turɓaya a yayin rasa ruwa, ko gaza anfani da shi. Na uku: An halatta mana ganimomin yaƙi, sune waɗanda musulmai suke ɗiba a yaƙoƙinsu tare da kafirai. Na huɗu: An bani ceto mafi girma dan hutar da mutane daga firgicin tsayuwa a ranar Alkiyama. Na biyar: An aikoni zuwa halitta gaba ɗaya mutanensu da Aljanunsun, saɓanin Annabawa kafin ni sun kasance ana aikosu ne zuwa mutanensu ne kawai.

Fa’idoji
  1. Halaccin ƙididdigawar bawa ga ni'imomin da Allah da Ya yi masa dan bada labari da kuma godiya ga Allah akansu.
  2. Falalar Allah - Mai girma da ɗaukaka - ga wannan al'ummar da kuma Annabinta da waɗannan ɗabi'un.
  3. Wajabcin yin sallah a cikin lokacinta kuma a kowane halin da ta kasance, ya aikata abinda yake da iko akansa na sharuɗɗanta da rukunanta da kuma wajibanta.
  4. Ceton da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya keɓanta da shi tsakanin Annabwa, nau’uka ne: Na ɗayansu: Cetansa ga halitta a cikin rabe hukunci tsakaninsu. Daga cikinsu: Cetansa a na shigar 'yan aljanna aljanna. Daga cikinsu: Cetansa na musamman ga baffansa Abu Ɗalib na a sawwaƙa wuta gare shi ba ya fita ba; domin cewa shi ya mutu kafiri.
  5. Ɗabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suna da yawa ba'a anbacesu ba a cikin wannan hadisin daga cikinsu: An ba shi dunkulallun kalmomi, kuma an cike annabta da shi, kuma an sanya sahummu kamar sahun mala'iku, da wasunsu daga ɗabi'u.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 74) (335). صحيح مسلم (1/ 370) (521). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص74). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 94).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

ya wuce, kuma babu wani abu a gidana da wani mai hanta zai iya ci sai guntun sha’ir a cikin rake domin ni.

عن عائشة رضي الله عنها قالت: تُوُفِّيَ رسول الله صلى الله عليه وسلم وما في بيتي من شيء يَأكُلُهُ ذُو كَبدٍ إلا شَطْرُ شَعير في رَفٍّ لي، فأكَلتُ منه حتى طال عليَّ، فَكِلْتُهُ فَفَنِيَ.
A kan hadisin A’isha, Allah Ya yarda da ita, ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya wuce, kuma babu wani abu a gidana da wani mai hanta zai iya ci sai guntun sha’ir a cikin rake domin ni.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

كنوز رياض الصالحين، أ.د. حمد بن ناصر بن عبد الرحمن العمار، دار كنوز إشبيليا، الطبعة الأولى: 1430 هـ. بهجة الناظرين، الشيخ: سليم بن عيد الهلالي، دار ابن الجوزي. نزهة المتقين، د. مصطفى سعيد الخن، د. مصطفى البغا، محيي الدين مستو، علي الشرجبي، محمد أمين لطفي، مؤسسة الرسالة، بيروت، الطبعة الأولى: 1397 هـ 1977 م، الطبعة الرابعة عشرة 1407 هـ 1987م. شرح صحيح البخاري لابن بطال، المؤلف: ابن بطال أبو الحسن علي بن خلف بن عبد الملك، تحقيق: أبو تميم ياسر بن إبراهيم، دار النشر: مكتبة الرشد - السعودية، الرياض، الطبعة: الثانية، 1423هـ - 2003م. رياض الصالحين، د. ماهر بن ياسين الفحل، الناشر: دار ابن كثير للطباعة والنشر والتوزيع، دمشق - بيروت، الطبعة: الأولى، 1428 هـ - 2007 م. صحيح مسلم، المؤلف: مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، المحقق: محمد فؤاد عبد الباقي، الناشر: دار إحياء التراث العربي - بيروت. صحيح البخاري، المؤلف: محمد بن إسماعيل أبو عبدالله البخاري الجعفي، المحقق: محمد زهير بن ناصر الناصر، الناشر: دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى، 1422هـ. المنهاج شرح صحيح مسلم بن الحجاج، المؤلف: أبو زكريا محيي الدين يحيى بن شرف النووي، الناشر: دار إحياء التراث العربي - بيروت، الطبعة: الثانية، 1392.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Dukkanin al'ummata za su shiga aljanna sai wanda ya ƙi

عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «كُلُّ أُمَّتِي يَدْخُلُونَ الْجَنَّةَ إِلَّا مَنْ أَبَى»، قَالُوا: يَا رَسُولَ اللهِ، وَمَنْ يَأْبَى؟ قَالَ: «مَنْ أَطَاعَنِي دَخَلَ الْجَنَّةَ، وَمَنْ عَصَانِي فَقَدْ أَبَى».
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce: "Dukkanin al'ummata za su shiga aljanna sai wanda ya ƙi", suka ce: ya Manzon Allah, wa zai ƙi? ya ce: "Wanda ya bi ni zai shiga aljanna, wanda ya saɓa min to haƙiƙa ya ƙi".
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa dukkanin al'ummarsa za su shiga aljanna sai wanda ya ƙi! Sai sahabbai - Allah Ya yarda da su - suka ce: Wa zai ƙi ya Manzon Allah?! Sai (manzon Allah) tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya amsa musu cewa: wanda ya miƙa wuya ya bi Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - zai shiga aljanna, amma wanda ya saɓa bai miƙa wuya ga shari'a ba, to, haƙiƙa ya hanu daga shiga aljanna da ayyukansa munana.

Fa’idoji
  1. Lallai cewa bin Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana daga biyayyar Allah, kuma saɓa masa yana daga saɓawa Allah.
  2. Bin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana wajabta aljanna, saɓa masa kuma yana wajabta wuta.
  3. Albishir ga masu biyayya daga cikin wannan al'ummar, kuma cewa su dukkaninsu za su shiga aljanna, sai wanda ya saɓawa Allah da Manzonsa.
  4. Tausayinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ga al'ummarsa, da kwaɗayinsa a kan shiriyarsu.
Madogara

صحيح البخاري (9/ 92) (7280). فيض القدير شرح الجامع الصغير، للمناوي، المكتبة التجارية الكبرى – مصر، الطبعة: الأولى. بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين لسليم الهلالي، ط1، دار ابن الجوزي، الدمام، 1415هـ. التيسير بشرح الجامع الصغير، للمناوي، مكتبة الإمام الشافعي، الرياض، ط3.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

cewa Annabi, aminci ya tabbata a gare shi, ya kira tukunyar ruwa

عن أنس بن مالك رضي الله عنه قال: حَضَرَتِ الصلاةُ فقامَ مَنْ كان قريبَ الدارِ إلى أَهْلِهِ، وبَقِيَ قَوْمٌ، فأُتِيَ رسولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم بِمِخْضَبٍ مِنْ حِجَارَةٍ، فَصَغُرَ المِخْضَبُ أَنْ يَبْسُطَ فيهِ كَفَّهُ، فتَوَضَّأَ القومُ كلهم. قالوا: كم كنتم؟ قال: ثمانينَ وزيادةً. وفي رواية: أَنَّ النبيَّ صلى الله عليه وسلم دعا بإناءٍ من مَاءٍ، فأُتِيَ بقَدَحٍ رَحْرَاحٍ فيهِ شَيْءٌ من ماءٍ، فوضعَ أَصَابِعَهُ فيهِ، قال أنس: فَجَعَلْتُ أَنْظُرُ إلى الماءِ يَنْبُعُ مِنْ بَيْنِ أَصَابِعِهِ، فَحَزَرْتُ مَنْ تَوَضَّأَ ما بَيْنَ السبعينَ إلى الثمانينَ.
Daga Anas bn Malik, yardar Allah ta tabbata a gare shi, ya ce: Sallah ta zo, sai wadanda suke kusa da gidan suka tashi ga danginsu, sai mutane suka ci gaba da zama a ciki, don haka sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya zo wurin makiyaya. Sai suka ce: Ku nawa ne? Ya ce: Takwas da ƙari. A cikin littafin: cewa Annabi, aminci ya tabbata a gare shi, ya kira tukunyar ruwa, ya kawo ta Bakdh Rahrah wani abu na ruwa, sai ya sanya yatsun sa a ciki, Anas ya ce: sun sanya ganin ruwa mai tushe daga tsakanin yatsun sa, Vhzrt wanda ke yin wudoo 'tsakanin saba'in zuwa tamanin.
Bukhari da Muslim Suka Rawaito shida Riwayoyin nasa daban dabanDarajaIngantacce ne
Sharhi

Anas, Allah ya yarda da shi, yana cewa: “Na halarci Sallah,” wato yayin da Sahabbai ke tare da Annabi – SAW- a Madina, sun halarci sallar la’asar. Don haka wadanda suke kusa da masallacin suka tashi, ma'ana wadanda gidansa yake kusa da wannan wurin sun je gidan don yin alwala daga gare shi. Kuma wasu mutane sun kasance, wato wadanda suka rayu a gidajensu sun yi nisa tare da Annabi mai tsira da amincin Allah. Don haka Annabi - SAW- ya zo da datti na duwatsu da ruwa a ciki, ma'ana ya kawo wa Annabi - SAW- wani karamin jirgin ruwa ne na dutse da ruwa kadan a ciki. Kuma karamar lakar ita ce shimfida tafin hannunsa a ciki, wato, karamin jirgin ya kuntata a tafin manzon Allah - SAW- lokacin da yake son tsawaita shi a tsakiya. Anas ya ce: “Sannan dukkan mutane suka yi alwala, sai muka ce, Ku nawa ne?” Ya ce: Takwas da ƙari, ma’ana: tamanin ko sama da haka.

Madogara

دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين، لابن علان، نشر دار الكتاب العربي، بدون تاريخ. نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الرابعة عشر، 1407هـ - 1987م. بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، للهلالي، نشر: دار ابن الجوزي. الطبعة الأولى 1418هـ. كنوز رياض الصالحين، نشر: دار كنوز إشبيليا، الطبعة: الأولى، 1430هـ - 2009م. صحيح البخاري، نشر: دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، نشر: دار إحياء التراث العربي، بيروت.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Abu Jumah Al-Ansari ya zo mana, sai ya ce: Mun kasance tare da Manzon Allah - Salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - kuma Moaz bin Jabal yana tare da mu goma, sai muka ce: Ya Rasulallahi, shin akwai wanda ya fi mu lada mai girma?

عن ابن جُبير، قال: قَدِم علينا أبو جُمعة الأنصاري، قال: كنَّا مع رسول الله صلى الله عليه وسلم ومَعَنا معاذ بن جَبَل عاشرَ عشرةٍ فقلنا: يا رسول الله هل مِن أَحَدَ أعْظَمُ مِنَّا أجرًا، آمنَّا بك واتَّبَعْناك؟ قال: «وما يَمْنَعُكم من ذلك ورسولُ الله بيْن أَظْهُرِكم، يأتيكم بالوَحْي من السماء؟ بل قومٌ يأتون مِنْ بَعْدِكم يأتيهم كتابٌ بيْن لَوْحَيْن فيؤمنون به ويعملون بما فيه، أولئك أعظمُ منكم أجرًا».
Daga bakin Ibn Jubayr, ya ce: Abu Jumaa al-Ansari ya zo wurinmu, ya ce: Mun kasance tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kuma Muadh bin Jabal na goma tare da mu. Ya ce: «Me ya hana ku daga wannan, alhali kuwa Manzon Allah, a kan bayyanarsa, ya zo muku da wahayi daga sama? Maimakon haka, mutane za su zo daga bayanka, kuma littafi zai zo musu a tsakanin allunan biyu, kuma za su yi imani da shi kuma su aikata abin da ke ciki .Wadancan sun fi ka lada.
Bukhari Ya Rawaito shi a babin Halittar Ayyukan Bayi - Al-Tabrani Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

- خلق أفعال العباد، لمحمد بن إسماعيل بن إبراهيم بن المغيرة البخاري، المحقق: د. عبد الرحمن عميرة، الناشر: دار المعارف السعودية – الرياض. - المعجم الكبير، لسليمان بن أحمد بن أيوب بن مطير الطبراني، المحقق: حمدي بن عبد المجيد السلفي، دار النشر: مكتبة ابن تيمية – القاهرة، الطبعة: الثانية. - فتح الباري شرح صحيح البخاري، لابن حجر العسقلاني، تحقيق: محب الدين الخطيب، نشر: دار المعرفة-بيروت، 1379ه. - سلسلة الأحاديث الصحيحة وشيء من فقهها وفوائدها، تأليف محمد ناصر الدين الألباني، الناشر: مكتبة المعارف للنشر والتوزيع، الرياض، الطبعة: الأولى، لمكتبة المعارف. - إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري, أحمد بن محمد بن أبى بكر بن عبد الملك القسطلاني القتيبي المصري, الناشر: المطبعة الكبرى الأميرية، مصر, الطبعة: السابعة، 1323 هـ. - مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي بن سلطان الملا الهروي القاري، الناشر: دار الفكر، بيروت – لبنان، الطبعة: الأولى، 1422هـ - 2002م.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
8 cikin 18
Hadisai 18
  1. Na rantse da wanda ran Muhammad yake a hannunSa , babu wani daya daga wannan al'ummar da zai ji ni Bayahude ne ko Kirista, sannan ya mutu bai yi imani da abinda aka aikoni da shi ba sai ya zama cikin 'yan wuta
  2. Sai muka ce: Kai ne shugabanmu, sai ya ce: "Shugaba Shi ne Allah", muka ce: Mafificinmu a fifiko, kuma mafi girmanmu a kyauta, sai ya ce: "Ku fadi maganarku, ko wani bangare na maganarku, kada Shaidan ya yi amfani daku
  3. Daga kanka ka fada za'a ji, ka roka a baka, ka nemi ceto za'a baka ceton
  4. An bani abubuwa biyar, wadanda ba a baiwa wani daga cikin (Annabawa) a gabani na ba
  5. ya wuce, kuma babu wani abu a gidana da wani mai hanta zai iya ci sai guntun sha’ir a cikin rake domin ni.
  6. Dukkanin al'ummata za su shiga aljanna sai wanda ya ƙi
  7. cewa Annabi, aminci ya tabbata a gare shi, ya kira tukunyar ruwa
  8. Abu Jumah Al-Ansari ya zo mana, sai ya ce: Mun kasance tare da Manzon Allah - Salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - kuma Moaz bin Jabal yana tare da mu goma, sai muka ce: Ya Rasulallahi, shin akwai wanda ya fi mu lada mai girma?
  9. Lallai Allah ya Zavi Kinanata daga cikin 'ya'yan Isma'il, kuma ya zavi Quraishawa daga cikin Kinanata, kuma ya zavi bani Hashim daga cikin Quraishawa, kuma ya zavoni daga cikin Bani hashim, saboda haka mi me Shugaban "yan Adam kuma babu Al-fahari, kuma ni ne farkon wanda Qasa zata keto masa, kuma farkon Mai ceto kuma farkon wanda za'a ceta
  10. Ina da Sunaye guda Biyar: Ni ne Muhammadu da Ahmad, Kuma ni ne Al-mahi wanda da ni Allah yake shafe kafirci, kuma ni ne Alhashir wanda Allah zai tashi Mutane a bayana, kuma ni Al-aqib
  11. Manzon Allah SAW ya gaya mana wasu sunayaensa wasu daga ciki mun riqe, sai ya ce: "Ni Muhammad da Ahmad da Al-muqaffa, da Al-hashir, da Annabin rahama"
  12. Maye ya xagaka ya kai Baban Huzaim?
  13. Na rantse da wanda raina yake a hannunSa, Ibnu Maryam (Annabi Isa) ya kusa ya sauka a cikinku yana mai hukunci mai adalci, sai ya karya gicciyayye (cross), ya kashe alade, ya sarayar da jizya, dukiya ta yawaita har babu wanda zai karbeta
  14. Ni ne Dimam dan Sa'alabata dan uwan Banu Sa'ad dan Bakar
  15. An saukarwa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali shi yana da shekara arba'in
  16. Ka rubuta, na rantse da wanda raina yake a hannunSa babu abin da zai fito daga cikinsa sai gaskiya
  17. Lallai ni na fiku tsoron Allah kuma na fiku saninSa
  18. Babu wani Annabi daga cikin Annabawa face an ba shi daga cikin ayoyi waɗanda mutane za su yi imani da shi

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com