Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Sai muka ce: Kai ne shugabanmu, sai ya ce: "Shugaba Shi ne Allah", muka ce: Mafificinmu a fifiko, kuma mafi girmanmu a kyauta, sai ya ce: "Ku fadi maganarku, ko wani bangare na maganarku, kada Shaidan ya yi amfani daku

عَن عَبدِ الله بنِ الشِّخِّير رضي الله عنه قَالَ: انْطَلَقْتُ في وَفدِ بَنِي عَامِرٍ إِلى رَسُولِ الله صلى الله عليه وسلم، فَقُلنا: أَنتَ سيّدُنَا، فقال: «السَّيدُ اللهُ»، قُلنا: وَأَفْضَلُنا فَضْلاً، وأعظَمُنا طَوْلاً، فقال: «قُولُوا بِقَولِكُم، أَو بَعضِ قولِكُم، وَلَا يَسْتَجْرِيَنَّكُم الشَّيطَانُ».
Daga Abdullahi Dan Shikkhir - Allah Ya yarda dashi - ya ce: Na tafi a cikin jama'ar Banu Amir zuwa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, Sai muka ce: Kai ne shugabanmu, sai ya ce: "Shugaba Shi ne Allah", muka ce: Mafificinmu a fifiko, kuma mafi girmanmu a kyauta, sai ya ce: "Ku fadi maganarku, ko wani bangare na maganarku, kada Shaidan ya yi amfani daku".
Abu Dawud ne ya Rawaito shi da Kuma AhmadDarajaIngantacce ne
Sharhi

Wasu jama'a suka zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, lokacin da suka iso wurinsa sai suka fadi - suna masu yabonsa - wasu daga cikin kalmomin da tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ki su, sai suka ce ; "Kai ne shugabanmu", sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Shugaba (Shi ne) Allah" Cikakken shugabanci nasa ne akan halittarSa su bayinSa ne. Suka ce : Kai ne "Mafificinmu a fifiko" kuma mafi daukakarmu a daraja da daukaka. kuma kaine "Mafi girmanmu a kyauta" mafi yawaitawarmu a kyauta da daukaka da daraja. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nuna musu su fadi maganarsu ta al'ada kada su kallafawa kansu lafazai, kuma kada Shaidan ya Ja su zuwa wuce gona da iri da kanbawar da zata afkar cikin abinda aka haramta na shirka da hanyoyinta.

Fa’idoji
  1. Girman darajar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a rayukan sahabbansa da girmamawarsu gare shi .
  2. Hani daga matsama kai a lafazi, da takaituwa a magana.
  3. Kariya ga Tauhidi daga abinda zai bata shi na maganganu da ayyuka.
  4. Hani daga wuce gona da iri a yabo, shi yana daga hanyoyin Shaidan,
  5. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne shugaban 'ya'yan Adam, abinda ya zo a hadisi shi yana babin kankar da kai ne, kuma a babin tsoro garesu kar su fada a wuce iyaka.
Madogara

سنن أبي داود (7/ 184) (4806). مسند أحمد (26/ 234) (16307). الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص424). الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص472). مشكاة المصابيح، للألباني مشكاة المصابيح (3/ 1373).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ANNABIMMU MUHAMMAD TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com