Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa dukkanin al'ummarsa za su shiga aljanna sai wanda ya ƙi! Sai sahabbai - Allah Ya yarda da su - suka ce: Wa zai ƙi ya Manzon Allah?! Sai (manzon Allah) tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya amsa musu cewa: wanda ya miƙa wuya ya bi Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - zai shiga aljanna, amma wanda ya saɓa bai miƙa wuya ga shari'a ba, to, haƙiƙa ya hanu daga shiga aljanna da ayyukansa munana.
- Lallai cewa bin Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana daga biyayyar Allah, kuma saɓa masa yana daga saɓawa Allah.
- Bin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana wajabta aljanna, saɓa masa kuma yana wajabta wuta.
- Albishir ga masu biyayya daga cikin wannan al'ummar, kuma cewa su dukkaninsu za su shiga aljanna, sai wanda ya saɓawa Allah da Manzonsa.
- Tausayinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ga al'ummarsa, da kwaɗayinsa a kan shiriyarsu.
صحيح البخاري (9/ 92) (7280). فيض القدير شرح الجامع الصغير، للمناوي، المكتبة التجارية الكبرى – مصر، الطبعة: الأولى. بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين لسليم الهلالي، ط1، دار ابن الجوزي، الدمام، 1415هـ. التيسير بشرح الجامع الصغير، للمناوي، مكتبة الإمام الشافعي، الرياض، ط3.