Annbai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah Ya ba shi wasu dabi'u uku (wadanda) bai bada su ga wani daga Annabwa a gabnina ba. Na farko: An bani nasara da tsoro da za'a jefa shi a cikin zukatan maƙiyana koda tsakanina da su akwai tafiyar wata. Na biyu: An sanya mana ƙasa ta zama masallacin da zamu dinga sallah a duk inda muke, kuma mai tsarkakewa da turɓaya a yayin rasa ruwa, ko gaza anfani da shi. Na uku: An halatta mana ganimomin yaƙi, sune waɗanda musulmai suke ɗiba a yaƙoƙinsu tare da kafirai. Na huɗu: An bani ceto mafi girma dan hutar da mutane daga firgicin tsayuwa a ranar Alkiyama. Na biyar: An aikoni zuwa halitta gaba ɗaya mutanensu da Aljanunsun, saɓanin Annabawa kafin ni sun kasance ana aikosu ne zuwa mutanensu ne kawai.
- Halaccin ƙididdigawar bawa ga ni'imomin da Allah da Ya yi masa dan bada labari da kuma godiya ga Allah akansu.
- Falalar Allah - Mai girma da ɗaukaka - ga wannan al'ummar da kuma Annabinta da waɗannan ɗabi'un.
- Wajabcin yin sallah a cikin lokacinta kuma a kowane halin da ta kasance, ya aikata abinda yake da iko akansa na sharuɗɗanta da rukunanta da kuma wajibanta.
- Ceton da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya keɓanta da shi tsakanin Annabwa, nau’uka ne: Na ɗayansu: Cetansa ga halitta a cikin rabe hukunci tsakaninsu. Daga cikinsu: Cetansa a na shigar 'yan aljanna aljanna. Daga cikinsu: Cetansa na musamman ga baffansa Abu Ɗalib na a sawwaƙa wuta gare shi ba ya fita ba; domin cewa shi ya mutu kafiri.
- Ɗabi'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suna da yawa ba'a anbacesu ba a cikin wannan hadisin daga cikinsu: An ba shi dunkulallun kalmomi, kuma an cike annabta da shi, kuma an sanya sahummu kamar sahun mala'iku, da wasunsu daga ɗabi'u.
صحيح البخاري (1/ 74) (335). صحيح مسلم (1/ 370) (521). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص74). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 94).