Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana rantsuwa akan kusancin saukar (Annabi) Isa dan Nana Maryam - aminci ya tabbata agare shi - dan ya yi hukunci a tsakanin mutane da adalci da shari'ar Annabi muhammadu, kuma shi zai karya gicciyayye (kros) wanda kiristoci suke girmama shi, kuma Annabi Isa - aminci ya tabbata agare shi - zai kashe alade, kuma cewa shi aminci ya tabbata agare shi zai sarayar da jiziya zai dora mutane gaba dayansu a shiga Addinin Musulunci. Kuma dukiya za ta yawaita wani ba zai karbeta ba; dan yawanta, da wadatuwar kowa da abinda ke hannunsa, da saukar albarka da malalowar alkairai.
- Tabbatar da saukar Annabi Isa - aminci ya tabbata agare shi - a karshen zamani, kuma cewa shi yana daga alamomin Alkiyama .
- Shari'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - watanta ba za ta shafeta ba.
- Saukar albarkoki a dukiya a karshen zamani, tare da cewa mutane zasu guje mata.
- Albishir da wanzuwar Addinin Musulunci ta yadda Annabi Isa - aminci ya tabbata agare shi - zai yi hukunci da shi a karshen zamani.
صحيح البخاري (3/ 82) (2222)، صحيح مسلم (1/ 135) (155)، شرح النووي على مسلم (1/471)، التوضيح (14/555)، عمدة القاري شرح صحيح البخاري (12/ 35).