Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lallai Rana ba'a tava tsayar da ita ga wani Mutum ba sai ga Yusha'u a Dararen da ya tafi Baitil maqdis

عن أبي هريرة، قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «إنَّ الشمسَ لم تُحْبَس على بشر إلا ليُوشَع ليالي سار إلى بيت المَقْدِس».
An rawaito daga Abu Huraira, ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Lallai Rana ba'a tava tsayar da ita ga wani Mutum ba sai ga Yusha'u a Dararen da ya tafi Baitil maqdis"
Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Babu wani Mutum da aka tava tsayar Masa da rana ba ta tsaya a falakinta sai Yusha'u Bin Nun kuma shi saurayi ne tare da Annabi Musa da yai tafiya tare da shi zuwa Khidhr lokacin da suka tafi Baitul Maqdis kuma cewa shi yaji tsoron faxuwar ta kafin ya shiga, kuma Ranar ta Kasance Jumu'a da ace ta faxi da ya shiga ne ranae Asabar kuma Yaqi a ranar haramun ne, sai ya ce da Rana ke Baiwar Allah ce nima haka, Ya Ubangiji ka tsayar da ita sai ta tsaya saboda shi har ya shiga Baitul maqdis

Madogara

صحيح البخاري، نشر: دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى، 1422ه. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، نشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت. مسند الإمام أحمد بن حنبل، تحقيق: شعيب الأرنؤوط - عادل مرشد، وآخرون، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الأولى، 1421هـ - 2001م. فيض القدير شرح الجامع الصغير، للمناوي، المكتبة التجارية الكبرى – مصر، الطبعة: الأولى. التنوير شرح الجامع الصغير، لمحمد بن إسماعيل بن صلاح بن محمد الحسني، الكحلاني الأمير الصنعاني، المحقق: د. محمَّد إسحاق محمَّد إبراهيم، الناشر: مكتبة دار السلام، الرياض، الطبعة: الأولى، 1432 هـ - 2011 م. سلسلة الأحاديث الصحيحة وشيء من فقهها وفوائدها، تأليف محمد ناصر الدين الألباني، الناشر: مكتبة المعارف للنشر والتوزيع، الرياض، الطبعة: الأولى، لمكتبة المعارف.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ANNABAWA DA MANZANNI MAGABATA AMINCI A GARESU

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com