Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

ZAMANTAKEWA TSAKANIN MA'AURATA

Hadisai 11

"Idan Mutum ya kirawo Matarsa saboda bukatarsa to taje masa kuma ko da ta kasance takan Tanderu ne"

عن أبي علي طلق بن علي رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «إذا دعا الرجل زوجته لحاجته فَلْتَأتِهِ وإن كانت على التَّنُور».
An rawaito daga Abu Talq Bn Ali -Allah ya yarda da shi- cewa Annabi -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Idan Mutum ya kirawo Matarsa saboda bukatarsa to taje masa kuma ko da ta kasance takan Tanderu ne"
Al-Tirmithi Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Idan Mutum ya kirawo Matarsa don Jima'i to ya wajaba akanta ta amsa bukatarsa, kuma koda tana cikin Shagala wani aiki wanda ba za'a iya yi ba sai ita, Kamar tana yin Gurasa ko tana girki.

Madogara

سنن الترمذي، نشر: شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي الحلبي – مصر، الطبعة: الثانية، 1395هـ - 1975م. صحيح الجامع الصغير وزبادته, تأليف: أبو عبدالرحمن محمد ناصر الدين الألباني, الناشر: المكتب الإسلامي. مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح, تأليف: علي بن سلطان القاري, الناشر: دار الفكر, ط1 عام 1422. تحفة الأحوذي بشرح جامع الترمذي, تأليف: أبو العلا محمد عبدالرحمن المباركفوري, الناشر: دار الكتب العلمية. دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين، لابن علان، نشر دار الكتاب العربي. تحفة الأبرار شرح مصابيح السنة, تأليف: القاضي ناصر الدين عبدالله البيضاوي, تحقيق: لجنة مختصة بإشراف نور الدين طالب, الناشر: وزارة الأوقاف بالكويت, عام 1433. بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين, تأليف: سليم بن عيد الهلالي, دار ابن الجوزي.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Mafi cikar muminai a imani shi ne mafificinsu a kyawawan ɗabi’u, mafificinku shi ne mafificinku ga iyalinsa

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «أَكْمَلُ الْمُؤْمِنِينَ إِيمَانًا أَحْسَنُهُمْ خُلُقًا، وَخَيْرُكُمْ خَيْرُكُمْ لِنِسَائِهِمْ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Mafi cikar muminai a imani shi ne mafificinsu a kyawawan ɗabi’u, mafificinku shi ne mafificinku ga iyalinsa.
Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da AhmadDarajaHasan ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayanin mafi cikar imani a cikin mutane shi ne wanda ɗabi’unsa suka kyautata, ta hanyar sakin fuska, da bayar da abu mai kyau, da kyakkyawar magana, da barin cutarwa. Mafi alherin muminai shi ne mafi alherinsu ga iyalansa, kamar matarsa da ‘ya'yansa mata, da ‘yan’uwansa mata, da danginsa mata, domin su ne suka fi kowa haƙƙin a kyautata musu.

Fa’idoji
  1. Falalar kyawawan dabi’u da cewar suna cikin imani.
  2. Aiki yana cikin imani, shi kuma imani yana ƙaruwa yana raguwa.
  3. Musulunci ya darajta mace, ya kwaɗaitar a kan kyautata musu.
Madogara

سنن أبي داود (7/ 70) (4682). سنن الترمذي (2/ 454) (1162). مسند أحمد ط الرسالة (12/ 364) (7402). سلسلة الأحاديث الصحيحة وشيء من فقهها وفوائدها، للألباني (1/ 573). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 362). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 130). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (5/ 234).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Dukkaninku masu kiwone to abin tambayane daga abinda yake kiwonta,

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بنِ عُمرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُما أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «كُلُّكُمْ رَاعٍ فَمَسْئُولٌ عَنْ رَعِيَّتِهِ، فَالأَمِيرُ الَّذِي عَلَى النَّاسِ رَاعٍ وَهُوَ مَسْئُولٌ عَنْهُمْ، وَالرَّجُلُ رَاعٍ عَلَى أَهْلِ بَيْتِهِ وَهُوَ مَسْئُولٌ عَنْهُمْ، وَالمَرْأَةُ رَاعِيَةٌ عَلَى بَيْتِ بَعْلِهَا وَوَلَدِهِ وَهِيَ مَسْئُولَةٌ عَنْهُمْ، وَالعَبْدُ رَاعٍ عَلَى مَالِ سَيِّدِهِ وَهُوَ مَسْئُولٌ عَنْهُ، أَلاَ فَكُلُّكُمْ رَاعٍ وَكُلُّكُمْ مَسْئُولٌ عَنْ رَعِيَّتِهِ».
Daga Abdullahi Ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Dukkaninku masu kiwone to abin tambayane daga abinda yake kiwonta, shugaban mutane mai kiwo ne shi abin tambayane game da su, mutum mai kiwone ga iyalan gidansa kuma shi abin tambaya ne game da su, mace mai kiwo ce a dakin mijinta da ’yayansa kuma ita abar tambaya ce game da su,, bawa mai kiwo ne akan dukiyar shugabansa shi abin tambaya ne game da ita, ku saurara dukkaninku abin tambaya ne game da abin da aka ba shi kiwonsa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa akwai nauyi akan kowanne musulmi a cikin zamantakewa da zai kula da ita kuma take akan sa, Shugaba da sarki mai kiwo ne a abinda Allah Ya ba shi kulawarsa, to ya wajaba akansa kiyaye shari'unsu, da kiyayesu daga wanda zai zalincesu, da yakar makiyinsu, da rashin tozarta hakkokinsu, Mutum a iyalan gidansa wanda aka dorawa tsayuwa kula da su ne da ciyar da su, da kyakkyawar mu'amala, da koyar da su da ladabtar da su, mace a cikin gidan mijinta mai kiwo ce ta hanyar kyawun sarrafa gidansa, da tarbiyyar 'ya'yansa, kuma ita abar tambaya ce game da hakan, bawa wanda aka mallaka da wanda aka yake aiki a biya shi abin tambaya ne a dukiyar mai gidansa ta hanyar tsayuwa da kiyaye abinda ke hannunsa daga gare shi , da hidimarsa, kuma shi abin tambaya ne game da hakan, kowanne mutum mai kiwo ne a abinda aka ba shi kiwon sa, kuma kowa abin tambaya ne game da abin kiwonsa.

Fa’idoji
  1. Nauyi a cikin al’umma ta Musulmai gamamman al’amari ne, kuma kowa da gwargadansa da ikonsa da kuma nauyin da aka dora masa.
  2. Girman nauyin da yake kan mace, hakan ta hanyar tsayuwa da hakkin gidan mijinta da wajibin dake kanta na 'ya'yanta.
Madogara

صحيح البخاري (3/ 150) (2554). صحيح مسلم (3/ 1459) (1829). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 369). إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري، القسطلاني (4/ 326).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

‌Haƙiƙa mata da yawa sun kewaye iyalan (Annabi) Muhammad suna kawo ƙarar mazajensu to waɗannan ba zaɓaɓɓunku ba ne

عَنْ إِيَاسِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ أَبِي ذُبَابٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا تَضْرِبُوا إِمَاءَ اللَّهِ» فَجَاءَ عُمَرُ إِلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: ذَئِرْنَ النِّسَاءُ عَلَى أَزْوَاجِهِنَّ، فَرَخَّصَ فِي ضَرْبِهِنَّ، فَأَطَافَ بِآلِ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ نِسَاءٌ كَثِيرٌ يَشْكُونَ أَزْوَاجَهُنَّ، فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَقَدْ طَافَ بِآلِ مُحَمَّدٍ نِسَاءٌ كَثِيرٌ يَشْكُونَ أَزْوَاجَهُنَّ، لَيْسَ أُولَئِكَ بِخِيَارِكُمْ».
Daga Abdullahi Dan Iyas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «‌Kada ku daki bayin Allah mata» sai Umar ya zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Mata sun yi wa mazajensu tawaye, sai ya yi rangwami a dukansu, sai mata da yawa suka kewaye iyalan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suna kawo ƙarar mazajensu, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Haƙiƙa mata da yawa sun kewaye iyalan (Annabi) Muhammad suna kawo ƙarar mazajensu to waɗannan ba zaɓaɓɓunku ba ne».
Abu Dawud ne ya ruwaito shi da ibn MajahDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana dukan mata, sai sarkin muminai Umar Ibnu Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya zo kuma ya ce: Ya Manzon Allah mata sun yi wa mazajensu tawaye kuma ɗabi'unsu sun munana. Sai (Manzon Allah) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi rangwami da dukansu dukan da ba zai sa ciwo ba idan an samu sababin yin hakan, kamar idan sun ƙi bada haƙƙin miji da kuma saɓa masa da makamancin haka. Sai wasu mata suka zo a bayansa wurin matan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suna kawo ƙara akan dukan mazajensu dukan da ba zai sa rauni ba, saboda mummunan aiki da wannan rangwamen, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Waɗannan mazajen waɗanda suke dukan matansu dukan da ba zai sa rauni ba ba zaɓɓɓunku ba ne.

Fa’idoji
  1. Bayanin falalar yin kyakkyawar mu'amala da mata, da kuma yin haƙuri akansu da kau da kai daga abinda yake kasancewa daga gurinsu shi ne ya fi daga dukansu.
  2. Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya sanya ƙarshen matakin maganin taurin kan mata, sai Ya ce: (Waɗanda kuke jin tsoron kangarewarsu, to ku yi musu wa'azi, kuma ku ƙaurace musu a wajen kwanciya, kuma ku dokesu; amma idan sun yi muku ɗa'a, to kada ku nemi wata hanyar cutar da su. Lallai Allah Ya kasance Maɗaukaki ne Mai girma. [al-Nisa'i: 34]. Kuma wadannan (matakai) ukun a jere suke, ba wai ahaɗe suke a lokaci ɗaya ba, sai ya fara da yin nasiha da wa'azi da gargaɗi idan ya fa'idantar to alhamdu lillah, idan bai amfanar ba sai ya ƙaurace mata a wurin kwanciya, idan bai fa'idantar ba sai ya daketa dukan ladabtarwa ba dukan ɗaukar fansa ba.
  3. Namiji mai kiwo ne a cikin gidansa, dan haka yana wajaba ya tarbiyyantar da su ya kuma tsaftace tarbiyyarsu da hikima da wa'azi mai kyau.
  4. Halaccin nazarin malami a cikin fatawarsa; dan sanin ƙarshenta da kuma makomarta.
  5. Halaccin kai ƙara ga sarki ko malami idan cuta ta riski mai kawo ƙara.
Madogara

سنن أبي داود (3/ 479) (2146). سنن ابن ماجه (3/ 152) (1985). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 363). مرقاة المفاتيح، لعلي القاري (5/ 2127).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

"Wata Mace bata taba Cutar Mijinta a Duniya ba sai Matar sa ta Hur Al'aini ta ce kada ki cuce shi Allah ya tsine miki saboda a wajenki bako ne ya kusa da ya rabu dake zuwa gare mu"

عن معاذ بن جبل رضي الله عنه مرفوعاً: «لا تؤذي امرأةٌ زوجَها في الدنيا إلا قالت زوجته من الحُورِ العِينِ لا تُؤْذِيهِ قاتلك الله! فإنما هو عندك دَخِيلٌ يُوشِكُ أن يفارقَكِ إلينا».
An rawaito daga Mu'az bn Jabal -Allah ya yarda da shi- daga Annabi "Wata Mace bata taba Cutar Mijinta a Duniya ba sai Matar sa ta Hur Al'aini ta ce kada ki cuce shi Allah ya tsine miki saboda a wajenki bako ne ya kusa da ya rabu dake zuwa gare mu"
Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

- رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين؛ للإمام أبي زكريا النووي، تحقيق د. ماهر الفحل، دار ابن كثير-دمشق، الطبعة الأولى، 1428ه. - دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين؛ لمحمد بن علان الشافعي، دار الكتاب العربي-بيروت - بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين؛ تأليف سليم بن عيد الهلالي، دار ابن الجوزي- الطبعة الأولى1418ه. - مرقاة المفاتيح :علي بن سلطان القاري -دار الفكر، بيروت – لبنان الطبعة -الأولى، 1422هـ - 2002م. - سنن الترمذي - محمد بن عيسى ، الترمذي، تحقيق وتعليق:أحمد محمد شاكر ومحمد فؤاد عبد الباقي وإبراهيم عطوة عوض -شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي الحلبي – مصر-الطبعة: الثانية، 1395 هـ - 1975 م. - سنن ابن ماجه : أبو عبد الله محمد بن يزيد القزويني، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي- دار إحياء الكتب العربية - فيصل عيسى البابي الحلبي. - مسند الإمام أحمد بن حنبل المحقق: شعيب الأرنؤوط - عادل مرشد، وآخرون إشراف: د عبد الله بن عبد المحسن التركي مؤسسة الرسالة الطبعة: الأولى، 1421 هـ - 2001 م. - سلسلة الأحاديث الصحيحة وشيء من فقهها وفوائدها/محمد ناصر الدين، الألباني مكتبة المعارف للنشر والتوزيع، الرياض-الطبعة: الأولى، (مكتبة المعارف).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

"Da zan Umarci wani Mutum da yayi sujada ga wani wallahi da na Umarci Mace ta yi Sujada ga Mijinta"

عن أبي هريرة رضي الله عنه مرفوعاً: «لو كنت آمِرًا أحدًا أن يسجد لأحد لأمرت المرأة أن تسجد لزوجها».
An rawaito daga Abu huraira -Allah ya yarda da shi- Daga Annabi: "Da zan Umarci wani Mutum da yayi sujada ga wani wallahi da na Umarci Mace ta yi Sujada ga Mijinta"
Al-Tirmithi Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

الجامع الكبير (سنن الترمذي), تأليف: محمد بن عيسى الترمذي, تحقيق وتعليق: أحمد محمد شاكر ومحمد فؤاد عبد الباقي وإبراهيم عطوة عوض -شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي الحلبي - مصر - الطبعة: الثانية، 1395 هـ - 1975 م. إرواء الغليل في تخريج أحاديث منار السبيل, تأليف: محمد ناصر الدين الألباني, الناشر: المكتب الإسلامي, ط2 عام 1405. بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين, تأليف: سليم بن عيد الهلالي, دار ابن الجوزي. مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح, تأليف: علي بن سلطان القاري, الناشر: دار الفكر, ط1 عام 1422.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

An anbaci Azalu ga Manzon Allah-Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- sai ya ce: Kuma babu dayanku da ya aikata ta? saboda babu wani rai da Allah ya halitta sai ya halicceta"

عن أبي سعيد الخدري رضي الله عنه : «ذُكِرَ َالعزل لرسول الله صلى الله عليه وسلم فقال: ولم يفعل ذلك أحدكم؟ -ولم يقل: فلا يفعل ذلك أحدكم؟-؛ فإنه ليست نفس مخلوقة إلا الله خالقها».
An rawaito daga Abu Sa'id Al-khudri -Allah ya yarda da shi-:An anbaci Azalu ga Manzon Allah-Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- sai ya ce: Kuma babu dayanku da ya aikata ta? saboda babu wani rai da Allah ya halitta sai ya halicceta"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

- صحيح البخاري –الجامع الصحيح-؛ للإمام أبي عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري، عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ. - صحيح مسلم؛ للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبد الباقي، دار عالم الكتب-الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ. - الإلمام بشرح عمدة الأحكام للشيخ إسماعيل الأنصاري-مطبعة السعادة-الطبعة الثانية 1392ه. - تيسير العلام شرح عمدة الأحكام-عبد الله البسام-تحقيق محمد صبحي حسن حلاق- مكتبة الصحابة- الشارقة- الطبعة العاشرة- 1426ه.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

"Mun kasance Munayin Azalu kuma Qurani yana sauka, sufyan: da ace abu ne da aka hana da Qur'ani ya Hanamu"

عن جابر بن عبد الله رضي الله عنهما قال: "كنا نعزل والقرآن ينزل". قال سفيان: لو كان شيئا ينهى عنه؛ لنهانا عنه القرآن.
An rawaito daga jabir Bn Abdullahi -Allah ya yarda da su- ya ce: "Mun kasance Munayin Azalu kuma Qurani yana sauka, sufyan: da ace abu ne da aka hana da Qur'ani ya Hanamu"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

- صحيح البخاري، للإمام أبي عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري، عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ. - صحيح مسلم، للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبد الباقي، دار عالم الكتب - الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ. - الإلمام بشرح عمدة الأحكام، للشيخ إسماعيل الأنصاري -مطبعة السعادة- الطبعة الثانية، 1392ه. - تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله البسام، تحقيق محمد صبحي حسن حلاق، مكتبة الصحابة، الشارقة، الطبعة العاشرة، 1426ه. - خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، فيصل بن عبد العزيز بن فيصل ابن حمد المبارك الحريملي النجدي، الطبعة الثانية، 1412هـ - 1992م. - منحة العلام في شرح بلوغ المرام، تأليف عبد الله الفوزان - طبعة دار ابن الجوزي - الطبعة الأولى، 1428ه. - توضيح الأحكام شرح بلوغ المرام، تأليف عبد الله البسام- مكتبة الأسدي، مكة المكرمة، الطبعة الخامِسَة، 1423هـ - 2003م. - فتح ذي الجلال والإكرام بشرح بلوغ المرام، للشيخ ابن عثيمين، المكتبة الإسلامية، القاهرة، تحقيق صبحي رمضان وأم إسراء بيومي- الطبعة الأولى، 1427ه. - الإفهام في شرح عمدة الأحكام، عبد العزيز بن عبد الله بن باز، حققه واعتنى به وخرج أحاديثه: د. سعيد بن علي بن وهف القحطاني- توزيع مؤسسة الجريسي.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
8 cikin 11
Hadisai 11
  1. "Idan Mutum ya kirawo Matarsa saboda bukatarsa to taje masa kuma ko da ta kasance takan Tanderu ne"
  2. Mafi cikar muminai a imani shi ne mafificinsu a kyawawan ɗabi’u, mafificinku shi ne mafificinku ga iyalinsa
  3. Dukkaninku masu kiwone to abin tambayane daga abinda yake kiwonta,
  4. ‌Haƙiƙa mata da yawa sun kewaye iyalan (Annabi) Muhammad suna kawo ƙarar mazajensu to waɗannan ba zaɓaɓɓunku ba ne
  5. "Wata Mace bata taba Cutar Mijinta a Duniya ba sai Matar sa ta Hur Al'aini ta ce kada ki cuce shi Allah ya tsine miki saboda a wajenki bako ne ya kusa da ya rabu dake zuwa gare mu"
  6. "Da zan Umarci wani Mutum da yayi sujada ga wani wallahi da na Umarci Mace ta yi Sujada ga Mijinta"
  7. An anbaci Azalu ga Manzon Allah-Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- sai ya ce: Kuma babu dayanku da ya aikata ta? saboda babu wani rai da Allah ya halitta sai ya halicceta"
  8. "Mun kasance Munayin Azalu kuma Qurani yana sauka, sufyan: da ace abu ne da aka hana da Qur'ani ya Hanamu"
  9. Yana daga sunna in ya auri budurwa: sai ya yi kwana bakwai a dakinta sannan ya raba kwana, in kuma bazawara ya aura sai yayi kwana uku a wajenta sannan ya raba kwana
  10. Na ce: Ya Manzon Allah, menene haƙƙin matar ɗayanmu a kansa?, ya ce; "Ka ciyar da ita idan kaci, ka tufatar da ita idan ka tufatar (da kanka), ko ka yi aiki, kada ka daki fuska, kada ka munana, kuma kada ka ƙaurace sai a ɗaki
  11. Wanda yake da mata biyu sai ya karkata zuwa ɗayansu, zai zo ranar alƙiyama alhali ɓarin jikinsa a karkace

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com