An tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - menene haƙƙin mata akan mijinta? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci wasu al'amura, daga cikinsu: Na farko: Kada ka keɓanci kanka da abin ci banda ita; kai ka ciyar da ita a duk lokacin da ka ci abin ci. Na biyu: Kada ka keɓanci kanka da tufatarwa da tufafi, kai ka tufatar da ita idan ka tufatar (da kanka), hak idan ka yi aiki kuma ka samu iko. Na uku: Ba'a dukanta sai da wani sababi da buƙatuwa, idan ya buƙatu zuwa dukanta dan ladabtarwa ko dan barinta wasu farillai to sai ya zama duka ba mai sa rauni ba; kuma ba'a dukan fuska; domin cewa fuska ita ce mafi girman gaɓɓai kuma mafi bayyanarsu kuma ta ƙunshi wasu sasanni manya da gaɓɓai masu laushi. Na huɗu: Kada ka yi zagi ko ka ce : Allah Ya munana fuskarki; kada ka danganta koda wani abu daga jikinta zuwa munin da shi ne kishiyar kyau; domin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Shi ne wanda Ya suranta fuskar mutum da jikinsa, kuma Ya kyautata halittar kowane abu, zargin halitta yana komawa ne zuwa zargin Mahalicci tsarki ya tabbata ga Allah. Na biyar: Kada ka ƙaurace sai a wurin kwanciya, kuma kada ka juya mata baya, kada ka juyar da ita zuwa wani gidan daban; wataƙila hakan a cikin abinda afkuwarsa yake sabawa ne daga ƙauracewa tsakanin miji da mata.
- Kwaɗayin sahabbai akan sanin haƙƙoƙin da bada su ga masu su wajibi ne akansu, da kuma sanin haƙƙoƙin su.
- Wajabcin ciyarwa da tufatarwa da wurin zama ga mace akan mijinta.
- Hani daga munanawa na ma'ana da wanda ake gani.
- Daga munanawa wanda aka hana daga gare shi ya ce: Ke ƙabilarki ba ta da daraja, ko daga mummunan dangi kike, ko mai kama da hakan.
سنن أبي داود (3/ 476) (2142). سنن ابن ماجه (3/ 56) (1850). مسند أحمد (33/ 213) (20011). فتح ذي الجلال والاكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (5/ 184). سبل السلام، للصنعاني (2/ 322). توضِيحُ الأحكَامِ مِن بُلوُغ المَرَام، للبسام (6/ 44). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص204). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (8/ 169). التَّنويرُ شَرْحُ الجَامِع الصَّغِيرِ، للأمير الصنعاني (5/ 369).