Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda yake da sama da mace (ɗaya), bai yi adalci tsakanin matansa gwargwadon iko ba na daidaitawa tsakaninsu a ciyarwa da wurin zama da abin sawa da wurin kwana, cewa uƙubarsa a ranar alƙiyama ta kasance ne rabin jikinsa a karkace, kuma karkacewarsa uƙuba ce gare shi akan zalincinsa, kamar yadda ya karkata a cikin mu'amalarsa.
- Wajabcin raban kwana akan namiji tsakanin matansa biyu ko matansa da yawa, kuma karkata zuwa ga ɗayansu ya bar sauran yana haramta, a abinda yake da iko akansa na ciyarwa, da wurin zama, da kyakkyawar tarba, da makamancin hakan.
- Daidaito a rabon kwana da makamancin haka, a abinda mutum yake iya mallakarsa, amma a abinda ba ya iya mallakinsa kamar soyayya da karkata ta zuciya to cewa shi ba ya shiga cikin hadisin, kuma shi ne abin nufi a cikin faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki -: {Ba zaku iya adalci a tsakanin mata ba koda kun yi kwaɗayi} [al-Nisa'i: 129].
- Sakayya tana kasancewa ne daga jinsin aiki, cewa mutum a lokacin da ya karkata a duniya daga wata mace zuwa wata, zai zo a ranar alƙiyama ɗaya daga tsagin jikinsa ya karkace daga ɗayan.
- Girmama haƙƙoƙin bayi, kuma cewa ba'a kau da kai a kansu; domin cewa su ababen ginawa ne akan ƙwauro da sakayya.
- An so taƙaituwa akan mace ɗaya idan namiji ya ji tsoron kada ya yi adalci tsakanin matansa; dan kada ya faɗa a cikin gazawa a cikin Addini; Allah Maɗaukakin sarki Ya ce: {Idan kuka ji tsoron ba zaku yi adalci ba to (ku auri mace) ɗaya} [al-Nisa'i: 3].
سنن أبي داود (3/ 469) (2133). سنن النسائي (7/ 63) (3942). سنن الترمذي (2/ 434) (1141). سنن ابن ماجه (3/ 143) (1969). مسند أحمد (13/ 320) (7936). توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، لعبد الله البسام (5/ 449). فتح ذي الجلال والإكرام شرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (4/ 631). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (7/ 463). عون المعبود شرح سنن أبي داود، ومعه حاشية ابن القيم، محمد أشرف العظيم آبادي (6/ 121).