Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

‌Haƙiƙa mata da yawa sun kewaye iyalan (Annabi) Muhammad suna kawo ƙarar mazajensu to waɗannan ba zaɓaɓɓunku ba ne

عَنْ إِيَاسِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ أَبِي ذُبَابٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا تَضْرِبُوا إِمَاءَ اللَّهِ» فَجَاءَ عُمَرُ إِلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: ذَئِرْنَ النِّسَاءُ عَلَى أَزْوَاجِهِنَّ، فَرَخَّصَ فِي ضَرْبِهِنَّ، فَأَطَافَ بِآلِ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ نِسَاءٌ كَثِيرٌ يَشْكُونَ أَزْوَاجَهُنَّ، فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَقَدْ طَافَ بِآلِ مُحَمَّدٍ نِسَاءٌ كَثِيرٌ يَشْكُونَ أَزْوَاجَهُنَّ، لَيْسَ أُولَئِكَ بِخِيَارِكُمْ».
Daga Abdullahi Dan Iyas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «‌Kada ku daki bayin Allah mata» sai Umar ya zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Mata sun yi wa mazajensu tawaye, sai ya yi rangwami a dukansu, sai mata da yawa suka kewaye iyalan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suna kawo ƙarar mazajensu, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Haƙiƙa mata da yawa sun kewaye iyalan (Annabi) Muhammad suna kawo ƙarar mazajensu to waɗannan ba zaɓaɓɓunku ba ne».
Abu Dawud ne ya ruwaito shi da ibn MajahDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana dukan mata, sai sarkin muminai Umar Ibnu Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya zo kuma ya ce: Ya Manzon Allah mata sun yi wa mazajensu tawaye kuma ɗabi'unsu sun munana. Sai (Manzon Allah) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi rangwami da dukansu dukan da ba zai sa ciwo ba idan an samu sababin yin hakan, kamar idan sun ƙi bada haƙƙin miji da kuma saɓa masa da makamancin haka. Sai wasu mata suka zo a bayansa wurin matan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suna kawo ƙara akan dukan mazajensu dukan da ba zai sa rauni ba, saboda mummunan aiki da wannan rangwamen, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Waɗannan mazajen waɗanda suke dukan matansu dukan da ba zai sa rauni ba ba zaɓɓɓunku ba ne.

Fa’idoji
  1. Bayanin falalar yin kyakkyawar mu'amala da mata, da kuma yin haƙuri akansu da kau da kai daga abinda yake kasancewa daga gurinsu shi ne ya fi daga dukansu.
  2. Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya sanya ƙarshen matakin maganin taurin kan mata, sai Ya ce: (Waɗanda kuke jin tsoron kangarewarsu, to ku yi musu wa'azi, kuma ku ƙaurace musu a wajen kwanciya, kuma ku dokesu; amma idan sun yi muku ɗa'a, to kada ku nemi wata hanyar cutar da su. Lallai Allah Ya kasance Maɗaukaki ne Mai girma. [al-Nisa'i: 34]. Kuma wadannan (matakai) ukun a jere suke, ba wai ahaɗe suke a lokaci ɗaya ba, sai ya fara da yin nasiha da wa'azi da gargaɗi idan ya fa'idantar to alhamdu lillah, idan bai amfanar ba sai ya ƙaurace mata a wurin kwanciya, idan bai fa'idantar ba sai ya daketa dukan ladabtarwa ba dukan ɗaukar fansa ba.
  3. Namiji mai kiwo ne a cikin gidansa, dan haka yana wajaba ya tarbiyyantar da su ya kuma tsaftace tarbiyyarsu da hikima da wa'azi mai kyau.
  4. Halaccin nazarin malami a cikin fatawarsa; dan sanin ƙarshenta da kuma makomarta.
  5. Halaccin kai ƙara ga sarki ko malami idan cuta ta riski mai kawo ƙara.
Madogara

سنن أبي داود (3/ 479) (2146). سنن ابن ماجه (3/ 152) (1985). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 363). مرقاة المفاتيح، لعلي القاري (5/ 2127).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALOLI DA LADUBBA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com