Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

FALALAR JIHADI

Hadisai 24

"Kwanan dakon Rana da yini yafi Al-khairi daga Azumin wata da kuma tsayuwar Sallarsa, kuma idan Mutum ya Mutu (yanayi) za'a rika rubuta masa lada kamar yana yi, kuma ana bashi Arzikinsa, kuma za'a tsareshi ga barin fitina"

عن سلمان الفارسي رضي الله عنه مرفوعاً: «رباط يوم وليلة خير من صيام شهر وقيامه، وإن مات جرى عليه عمله الذي كان يعمل، وأُجْرِيَ عليه رزقه، وأَمِنَ الفَتَّانَ».
An rawaito daga Salman Al-farisi -Allah ya yarda da shi- daga Manzon Allah: "Kwanan dakon Rana da yini yafi Al-khairi daga Azumin wata da kuma tsayuwar Sallarsa, kuma idan Mutum ya Mutu (yanayi) za'a rika rubuta masa lada kamar yana yi, kuma ana bashi Arzikinsa, kuma za'a tsareshi ga barin fitina"
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Gadin Wuni da dare saboda Allah don kare Musulmai, yafi Al-khairi kan azumin wata, da tsayuwar darensa, kuma idan Mai Jahadi ya Mutu aikin ladansa yana wanzuwa yana ci gaba baya yankwa, kuma za’a rika bashi Arzikin Al-janna, saboda yana raye a wajen Ubangijinsa a Al-janna, kuma yana samun Karama ta yadda Mala’iku biyu basa su masa ba don tamabaya (a Kabari) kuma wancananka saboda ya Mutu ne yana mai dakon kare Addinin Allah Madaukakin Sarki, tare da sanin cewa Mai zaman dako a tafarkin Allah; saboda shi ya lazamci wuraren Iyakoki don kariyar ga Musulmai daga Kafirai

Madogara

- رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين؛ للإمام أبي زكريا النووي، تحقيق د. ماهر الفحل، دار ابن كثير، دمشق، الطبعة الأولى، 1428ه. - دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين؛ لمحمد بن علان الشافعي، دار الكتاب العربي-بيروت. - بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين؛ تأليف سليم الهلالي، دار ابن الجوزي- الطبعة الأولى 1418ه. - نزهة المتقين شرح رياض الصالحين؛ تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة-بيروت، الطبعة الرابعة عشر، 1407هـ. - صحيح مسلم؛ للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبد الباقي، دار عالم الكتب-الرياض، الطبعة الأولى،1417هـ. - شرح رياض الصالحين؛ للشيخ محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن، الرياض، 1426هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

"Kowane Mamaci ana rufe littafin aikinsa sai mai zaman dako a tafarkin Allah, shi ne kadai ake ci gaba da bashi lada har Ranar Al-kiyama, kuma za'a tseratar da shi daga fitinar Kabari"

عن فَضَالَةُ بنُ عُبَيْدٍ وسلمان الفارسي وعقبة بن عامر الجهني رضي الله عنهم مرفوعاً: «كُلُّ مَيِّتٍ يُخْتَمُ على عَمَلِهِ إلا الُمرَابِطَ في سبيل الله، فإنه يَنْمِي لَهُ عَمَلَهُ يوم القيامة، ويُؤَمَّنُ فتنة القبر».
Ukkaz da Mijna da Thul-Majaz a lokacin Jahil;iyya Kasuwanni ne sai kuke ganin laifi ne kuyi kasuwanci a cikinsu lokacin aikin Hajji, Sai Allah ya saukar da: Babu laifi akan ku ku nemi Falala daga Ubangijinku" Bakara:198 a cikin lokacin Hajji...
Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Kowane Mamaci ladan aikinsa yana tsayawa da Mutuwarsa, ba’a rubuta masa komai sabo, sai mai aman dako a tafarkin Allah,shi ne wanda yakr gadin Iyakokin Musulmai saboda Allah saboda haka Allah ya Aurtashi da wanzuwar ladan aikinsa, kuma za’a amuntar das hi daga fitinar Kabari kuma Mala’iku biyu ba asu tambayar shi ba

Madogara

- رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين؛ للإمام أبي زكريا النووي، تحقيق د. ماهر الفحل، دار ابن كثير-دمشق، الطبعة الأولى، 1428ه. - بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين؛ تأليف سليم الهلالي، دار ابن الجوزي- الطبعة الأولى1418ه. - نزهة المتقين شرح رياض الصالحين؛ تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة-بيروت، الطبعة الرابعة عشر، 1407هـ. سنن أبي داود، سليمان بن الأشعث السِّجِسْتاني تحقيق: محمد محيي الدين عبد الحميد: المكتبة العصرية، صيدا - بيروت. سنن الترمذي، محمد بن عيسى، الترمذي، تحقيق وتعليق:أحمد محمد شاكر ومحمد فؤاد عبد الباقي وإبراهيم عطوة عوض، شركة مكتبة ومطبعة مصطفى البابي الحلبي، مصر الطبعة:الثانية، 1395هـ - 1975م. مسند الإمام أحمد بن حنبل، المحقق: شعيب الأرنؤوط - عادل مرشد، وآخرون إشراف: د عبد الله بن عبد المحسن التركي مؤسسة الرسالة الطبعة: الأولى، 1421 هـ - 2001 م. سنن أبي داود، سليمان بن الأشعث، المحقق: محمد محيي الدين عبد الحميد المكتبة العصرية، صيدا - بيروت. مسند الدارمي المعروف بـ (سنن الدارمي) عبد الله بن عبد الرحمن الدارمي، تحقيق: حسين سليم أسد الداراني - دار المغني للنشر والتوزيع، المملكة العربية السعودية الطبعة: الأولى، 1412 هـ - 2000 م. صحيح أبي داود -الأم- محمد ناصر الدين الألباني مؤسسة غراس للنشر والتوزيع، الكويت الطبعة: الأولى، 1423 هـ - 2002 م.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Zaman dakon yini ɗaya saboda Allah shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta

عَنْ سَهْلِ بْنِ سَعْدٍ السَّاعِدِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «رِبَاطُ يَوْمٍ فِي سَبِيلِ اللَّهِ خَيْرٌ مِنَ الدُّنْيَا وَمَا عَلَيْهَا، وَمَوْضِعُ سَوْطِ أَحَدِكُمْ مِنَ الجَنَّةِ خَيْرٌ مِنَ الدُّنْيَا وَمَا عَلَيْهَا، وَالرَّوْحَةُ يَرُوحُهَا العَبْدُ فِي سَبِيلِ اللَّهِ أَوِ الغَدْوَةُ خَيْرٌ مِنَ الدُّنْيَا وَمَا عَلَيْهَا».
Daga Sahl ɗan Sa'ad al-sa'idi - Allah Ya yarda da shi - lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Zaman dakon yini ɗaya saboda Allah shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta, kuma bigiren bulalar ɗayanku a aljanna shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta, yammacin da bawa zai yi shi saboda Allah ko jijjifi shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa lazimtar gurin da yake tsakanin musulmai da kafirai dan gadin musulmai daga gare su a yini ɗaya yana mai tsarkake niyya saboda Allah, shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta, kuma bigiren bulalar da zai yi yaƙi da ita saboda Allah a cikin aljanna shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta, kuma lallai cewa lada da sakamakon tafiya a cikin lokaci daga farkon yini zuwa farkon lokacin azahar, ko yammaci: Daga lokacin azahar zuwa dare saboda Allah sau ɗaya, shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta.

Fa’idoji
  1. Falalar zaman dako saboda Allah, dan abinda ke cikinsa na sadaukar da rai, dan kuma abinda yake jerantuwa a kansa na ɗaukaka kalmar Allah da taimakon AddininSa; saboda haka lallai sakamakon yini ɗaya, shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta.
  2. Wulaƙantar duniya dangane da lahira; domin cewa gurbin bulala na aljanna shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta.
  3. Falalar yaƙi saboda Allah, da girman ladansa; domin ladan yammaci ɗaya ko jijjifi ɗaya shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta.
  4. Faɗinsa; "Saboda Allah" A cikinsa akwai nuni akan muhimmancin tsarkake niyya, kuma cewa lada mai jerantuwa ne a kansa.
Madogara

صحيح البخاري (4/ 35) (2892). صحيح مسلم (3/ 1500) (1881). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص739).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Yin sammako ko yammaci don Allah shi ne mafi alheri: a cikin fitowar Rana da faduwarta

عن أبُي أَيُوب الأنصَارِيّ رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «غَدْوَةٌ فِي سَبِيلِ الله، أَوْ رَوْحَةٌ: خَيْرٌ مِمَّا طَلَعَتْ عَلَيْهِ الشَّمْسُ وَغَرَبَتْ». عن أنس رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «غَدْوَةٌ فِي سَبِيلِ الله، أَوْ رَوْحَةٌ: خَيْرٌ مِنْ الدُّنْيَا وَمَا فِيهَا».
Daga Abu Ayuba Al'ansary -Allah ya yarda dashi- zuwa ga Annabi: "Yin sammako ko yammaci don Allah shi ne mafi alheri: a cikin fitowar Rana da faduwarta". Daga Anas -Allah ya yarda dashi- zuwa ga Annabi: "Yin sammako ko yammaci don Allah: shi ne mafi alheri akan duniya da abin da ke cikinta".
Muslim ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Wadannan hadisai biyu suna nuna mana falalar yin jihadi don Allah koda kuwa dan kadan ne gwargwadon lokacin safiya ko na yamma, ballantana kuma lokaci mai yawa wanda cikinsa akwai tsananin hakuri da gwagwarmaya da abokan gaba, wannan shi ake nufi da yi don Allah, watau yakar kafirai. Kuma ya kamata asan cewa neman ilmin sharia shina bangare ne mai girma na jihadi don Allah, hakanan taimakon gaskiya, hakanan ruguza hujjojin zindikai arna turawa yanmishan masu yakar musulumci masu son gani bayansa shi ne mafi girma cikin jihadi a tafarkin Allah. Manufar jihadi, shi ne bayyana Musulunci da taimaka masa, kuma dakushe arna, yana daga jihadi mai girma. Ya Allah ka datar da Musulmi a wajen taimakawa addininsu, da daukaka kalmarka. Kai ne Makusanci Mai amsawa.

Madogara

صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ. صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423هـ. تأسيس الأحكام، أحمد بن يحيى النجمي، دار علماء السلف، الطبعة: الثانية 1414هـ. تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق: محمد صبحي حلاق، مكتبة الصحابة، الأمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة: العاشرة 1426هـ. الإلمام بشرح عمدة الأحكام، إسماعيل بن محمد الأنصاري، دار الفكر، دمشق، الطبعة: الأولى 1381هـ. عمدة الأحكام من كلام خير الأنام -صلى الله عليه وسلم- لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، دار الثقافة العربية، دمشق، بيروت، مؤسسة قرطبة، الطبعة: الثانية 1408هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ba wani wanda aka yi wa rauni a tafarkin Allah face sai ya zo Ranar Alkiyama, raunin nasa yana jini: kalarsa kalar jini, kanshinsa kuma kanshin almiski

عن أبي هريرة رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم : «ما من مَكْلُومٍ يُكْلَمُ في سبيل الله، إلا جاء يومَ القيامة، وكَلْمُهُ يَدْمَى: اللَّونُ لَوْنُ الدَّمِ، والرِّيحُ رِيحُ المِسْكِ».
Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Ba wani wanda aka yi wa rauni a tafarkin Allah face sai ya zo Ranar Alkiyama, raunin nasa yana jini: kalarsa kalar jini, kanshinsa kuma kanshinalmiski
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah yana bayyana mana falalar jihadi a tafarkin Allah Madaukaki da kuma irin abin da mai jihadi ke samu, na lada, cewa duk wanda aka yiwa rauni a tafarkin Allah ko an kashe shi ko ya warke, to zai zo Ranar kiyama gaban al'umma da damarar yaki, zai zo da ciwonsa danye, yana da launin jini kanshin Almiski.

Madogara

1- صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ. 2- صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423هـ. 3- تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق: محمد صبحي حلاق، مكتبة الصحابة، الإمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة: العاشرة 1426هـ. 4- الإلمام بشرح عمدة الأحكام، إسماعيل بن محمد الأنصاري، دار الفكر، دمشق، الطبعة: الأولى 1381هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Wanda ya roki Allah shahada da gaskiya, Allah Zai kai shi matsayin shahidai, koda ya mutu akan shinfiɗarsa

عَن سَهْلِ بْنِ حُنَيْفٍ رضي الله عنه أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنْ سَأَلَ اللهَ الشَّهَادَةَ بِصِدْقٍ بَلَّغَهُ اللهُ مَنَازِلَ الشُّهَدَاءِ، وَإِنْ مَاتَ عَلَى فِرَاشِهِ».
Daga Sahl ɗan Hunaif - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya roki Allah shahada da gaskiya, Allah Zai kai shi matsayin shahidai, koda ya mutu akan shinfiɗarsa".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda ya nemi shahada da mutuwa a tafarkin Allah, kuma ya kasance mai gaskiya mai tsarkake niyyarsa ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -, Allah Zai ba shi darajojin shahidai saboda niyyarsa ta gaskiya koda ya mutu akan shinfiɗa ba a yaki ba.

Fa’idoji
  1. Gaskiyar niyya tare da aikata abin da za'a iya, sababi ne na samun abin nufi na lada da sakamako, koda bai yi aikin da ake nema ba.
  2. Kwaɗaitarwa akan jihadi da neman shahada a tafarkin Allah - Mai girma da ɗaukaka -.
  3. Baiwar Allah - Mai girma da ɗaukaka - ga wannan al'ummar, shi (Allah) yana bada mafi ɗaukakar darajoji a cikin aljanna da kankanin aiki.
Madogara

صحيح مسلم (3/ 1517) (1909). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 123). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 87).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

wani mutum ya ce wa Annabi - Salatin Allah da amincin Allah su tabbata a gare shi - a ranar Lahadi: Shin kun ga ko an kashe ni, ina nake? Ya ce: “A sama,” ya jefa dabino a hannunsa, sannan ya yi faɗa har sai an kashe shi.

عن جابر بن عبد الله رضي الله عنهما قال رجل للنبي صلى الله عليه وسلم يومَ أُحُدٍ: أَرَأَيْتَ إن قُتِلْتُ فَأَيْنَ أَنَا؟ قال: «في الجَنَّةِ» فأَلْقَى تَمراتٍ كُنَّ في يَدِه، ثم قاتل حتى قُتِلَ.
Daga Jabir bin Abdullah - Allah ya yarda da shi - wani mutum ya ce wa Annabi - Salatin Allah da amincin Allah su tabbata a gare shi - a ranar Lahadi: Shin kun ga ko an kashe ni, ina nake? Ya ce: “A sama,” ya jefa dabino a hannunsa, sannan ya yi faɗa har sai an kashe shi.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

- رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين؛ للإمام أبي زكريا النووي، تحقيق د. ماهر الفحل، دار ابن كثير-دمشق، الطبعة الأولى، 1428ه. - نزهة المتقين شرح رياض الصالحين؛ تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة-بيروت، الطبعة الرابعة عشر، 1407هـ. - صحيح البخاري –الجامع الصحيح-؛ للإمام أبي عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري، عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ. - صحيح مسلم؛ للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبد الباقي، دار عالم الكتب-الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ - تطريز رياض الصالحين؛ تأليف فيصل آل مبارك، تحقيق د. عبد العزيز آل حمد، دار العاصمة-الرياض، الطبعة الأولى، 1423هـ. - فتح الباري لابن حجر العسقلاني، دار المعرفة، 1379.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Duk wanda ya shirya mayaki a tafarkin Allah to hakika ya yi yaki, wanda ya maye gurbin wani mayaki a tafarkin Allah (a gidansa) da alheri to hakika ya yi yaki

عَن زَيْدِ بْنِ خَالِدٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنْ جَهَّزَ غَازِيًا فِي سَبِيلِ اللَّهِ فَقَدْ غَزَا، وَمَنْ خَلَفَ غَازِيًا فِي سَبِيلِ اللَّهِ بِخَيْرٍ فَقَدْ غَزَا».
Daga Zaid ɗan Khalid - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Duk wanda ya shirya mayaki a tafarkin Allah to hakika ya yi yaki, wanda ya maye gurbin wani mayaki a tafarkin Allah (a gidansa) da alheri to hakika ya yi yaki".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya tanadarwa wani mayaki a tafarkin Allah sabubban tafiyarsa da abinda yake bukatuwa gare shi daga abinda babu makawa gare shi na makami da abin hawa, da abinci, da ciyarwa da waninsu; to shi yana cikin hukuncin mai yin yaki, kuma ladan mayaki zai same shi . wanda ya jibinci al'amarin mayaki da alheri, kuma ya maye gurbinsa a cikin kula da iyalansa a lokacin da ba ya nan to shi yana cikin hukuncin mayaki yake.

Fa’idoji
  1. Kwaɗaitar da musulmai akan taimakekeniya akan ayyukan alheri.
  2. Ibnu Hajar ya ce: A cikin wannan Hadisin a kwai kwaɗaitarwa akan kyautatawa ga wanda ya aikata wata maslaha ga musulmai, ko ya tsaya da wani al'amari daga abubuwan da ya shafesu.
  3. Ka'ida gamammiya: Cewa wanda ya taimaki wani mutum a cikin aikin ɗa'a daga ayyukan ɗa'a ga Allah to yana da kwatankwacin ladansa, ba tare da an rage wani abu daga ladansa ba.
Madogara

صحيح البخاري (4/ 27) (2843). صحيح مسلم (3/ 1506) (1895). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 267). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص143). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (3/ 588). لسان العرب، لابن منظور (15/ 123). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 374). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 202).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
8 cikin 24
Hadisai 24
  1. "Kwanan dakon Rana da yini yafi Al-khairi daga Azumin wata da kuma tsayuwar Sallarsa, kuma idan Mutum ya Mutu (yanayi) za'a rika rubuta masa lada kamar yana yi, kuma ana bashi Arzikinsa, kuma za'a tsareshi ga barin fitina"
  2. "Kowane Mamaci ana rufe littafin aikinsa sai mai zaman dako a tafarkin Allah, shi ne kadai ake ci gaba da bashi lada har Ranar Al-kiyama, kuma za'a tseratar da shi daga fitinar Kabari"
  3. Zaman dakon yini ɗaya saboda Allah shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta
  4. Yin sammako ko yammaci don Allah shi ne mafi alheri: a cikin fitowar Rana da faduwarta
  5. Ba wani wanda aka yi wa rauni a tafarkin Allah face sai ya zo Ranar Alkiyama, raunin nasa yana jini: kalarsa kalar jini, kanshinsa kuma kanshin almiski
  6. Wanda ya roki Allah shahada da gaskiya, Allah Zai kai shi matsayin shahidai, koda ya mutu akan shinfiɗarsa
  7. wani mutum ya ce wa Annabi - Salatin Allah da amincin Allah su tabbata a gare shi - a ranar Lahadi: Shin kun ga ko an kashe ni, ina nake? Ya ce: “A sama,” ya jefa dabino a hannunsa, sannan ya yi faɗa har sai an kashe shi.
  8. Duk wanda ya shirya mayaki a tafarkin Allah to hakika ya yi yaki, wanda ya maye gurbin wani mayaki a tafarkin Allah (a gidansa) da alheri to hakika ya yi yaki
  9. Allah na gafarta wa shahidi komai sai addini.
  10. Yi nasara saboda Allah, duk wanda ya yi yaki saboda Allah ya zarce rakumi mace kuma ya cancanci aljanna
  11. Mutumin da ya yi kuka saboda tsoron Allah ba zai shiga wuta ba har sai madara ta dawo a cikin nono, kuma babu tarin kura saboda Allah da hayakin Jahannama
  12. Diga-digan wani bawa ba su taɓa ƙura a cikin tafarkin Allah ba, kuma wuta ta shafe shi
  13. Babu abinda Shahidi yake samunsa (Na Zafi) sai kamar abunda dayanku yake ji idan Turuwa ta cije shi
  14. Misalin mujahid a tafarkin Allah shi ne misalin mai azumi yana tsaye ga ayoyin Allah wanda ba ya kasawa daga azumi, ko salla, har sai mujahid din ya dawo saboda Allah
  15. Duk wanda ya turke Doki Saboda Allah, don yayi Imani da Allah, kuma ya gasgata da Alkawarinsa, to cewa koshinsa da kuma Ruwansa da Bayan gidansa da futsarinsa ya na cikin abunda za'a auna Masa lada a Ranar Al-kiyama
  16. Ya Abu Sa'id, wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayin Addini, da (Annabi) Muhammad a matsayin Annabi, aljanna ta wajaba a gare shi
  17. Duk wanda ya jefa kibiya a cikin hanyar Allah to ya 'yanta adalci
  18. Duk wanda ya yi yaki a tafarkin Allah daga wani mutum musulmi wanda ya fi makiyayi, aljanna ta wajaba a gare shi, kuma duk wanda ya ji rauni a tafarkin Allah ko kuma ya gamu da wata masifa: masifa ce. Launinsa saffron ne, kamshinsa kuwa kamar miski ne
  19. Yawon buda ido na al'ummata na jihadi saboda Allah - mai girma da daukaka
  20. Babu wasu kwanaki da aiki na ƙwarai a cikinsu ya fi soyuwa a wurin Allah sama da waɗannan kwanakin". Wato kwanaki goman
  21. Waye a cikinku yabar abinda ya saba ya bayarwa a gidansa, da dukiyarsa na Al-khairi to yana da kwatankwacin rabin ladan Mai futa
  22. "Dawowa daga Yaki kamar Tafiya yakin ce"
  23. Duk wanda bai yi yaki ba ko kuma ya shirya Mayaki ko kuma ya Wakilci Mayakin da Alkairi a cikin Iyalansa, Sai Allah ya same shi da Makwakwashiya kafin Ranar Al-kiyama
  24. Duk wanda bai yi yaki kuma bai zantar da kansa zai yi yaki ba to zai mutu cikin Sifar Munafurci

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com