Daga Abu Abs Abdurrahman ɗan Jabr - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Diga-digan wani bawa ba su taɓa ƙura a cikin tafarkin Allah ba, kuma wuta ta shafe shi".
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi albishir da cewa wanda ƙura ta samu diga-digansa alhali shi yana yaƙi a tafarkin Allah cewa wuta ba zata shafe shi ba.
Fa’idoji
Albishir ga mai yaƙi a tafarkin Allah da tsira daga wuta.
Ya ambaci diga-digai duk da cewa ƙura tana game dukkan jiki; domin cewa mafi yawancin mayaƙa a wancan zamanin masu tafiyar ƙasa ne, diga-digai kuwa suna ƙura akowane hali.
Ibnu Hajar ya ce: Idan mujarradin taɓa ƙura ga diddige yana haramta masa wuta; to ta yaya ga wanda ya yi ƙoƙari iya ƙoƙarinsa ya ƙarar da ƙarfinsa.
Madogara
صحيح البخاري (4/ 20) (2811)، (2/ 7) (907).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 424).
التنوير شرح الجامع الصغير، للصنعاني (7/ 361).
فيض القدير شرح الجامع الصغير، للمناوي (5/ 437).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 911).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com