Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bawa Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - labarin cewa wanda ya yi imani da Allah kuma ya yarda da Shi a matsayin Ubangiji abin bauta kuma shugaba kuma mai umarni, kuma da Musulunci a matsayin Addini dan jawuwa da miƙa wuya da dukkanin umarce-umarcensa da hane-hanensa, da kuma (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a matsayin Annabi da dukkan abinda aka aiko shi da shi kuma ya isar da shi; to aljanna ta tabbata gareshi, sai Abu Sa'id - Allah Ya yarda da shi - ya yi mamaki ga (wannan maganar), sai ya ce: Ka maimaita mini ita ya Manzon Allah, sai ya aikata, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Kuma ina da wata dabi'ar daban wacce Allah Yake daukaka darajar bawa da ita sau dari a cikin aljanna, tsakanin kowace darajoji biyu kamar tsakanin sama da kasa ne, Abu Sa'ida ya ce: Waccece ya Manzon Allah? ya ce: Jihadi a tafarkin Allah, jihhadi a tafarkin Allah.
- Daga abubuwan da suke tabbatar da shiga aljanna yarda da Allah da kuma Musulunci a matsayin Addini da (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a matsayin Annabi.
- Girmama al'amarin jihadi a tafarkin Allah - Maɗaukakin sarki -.
- Ɗaukaka matsayin yaƙi a cikin aljanna.
- Akwai wasu darajoji a cikin aljanna ba sa ƙirguwa, da matsayin da ba za su ƙirgu ba, kuma mayaƙa suna da darajoji ɗari daga cikinsu.
- Soyayyar sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga sanin alheri, da ƙofofinsa da kuma sabubbansa.
صحيح مسلم (3/ 1501) (1884). نزهة المتقين، لمجموعة من الباحثين (2/ 910). بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (3/ 423). النهاية في غريب الحديث والأثر، لابن الأثير (5/ 153).