Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lallai cewa mafi sauƙin 'yan wuta a azaba wanda yake da takalma biyu da igiyoyi na wuta, ƙwaƙwalwarsa tana tafarfasa kamar yadda (tukunyar) tagulla take tafarfasa, ba ya ganin cewa wani mutum ya fi shi tsananin azaba, kuma shi shi ne mafi sauƙin azabarsu

عَنِ النُّعْمَانِ بْنِ بَشِيرٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّ أَهْوَنَ أَهْلِ النَّارِ عَذَابًا مَنْ لَهُ نَعْلَانِ وَشِرَاكَانِ مِنْ نَارٍ، يَغْلِي مِنْهُمَا دِمَاغُهُ كَمَا يَغْلِ الْمِرْجَلُ، مَا يَرَى أَنَّ أَحَدًا أَشَدُّ مِنْهُ عَذَابًا، وَإِنَّهُ لَأَهْوَنُهُمْ عَذَابًا».
Daga Nu'uman Dan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai cewa mafi sauƙin 'yan wuta a azaba wanda yake da takalma biyu da igiyoyi na wuta, ƙwaƙwalwarsa tana tafarfasa kamar yadda (tukunyar) tagulla take tafarfasa, ba ya ganin cewa wani mutum ya fi shi tsananin azaba, kuma shi shi ne mafi sauƙin azabarsu"
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mafi sauƙin 'yan wuta a azaba a ranar lahira wanda yake da takalma biyu da igiyoyi biyu ƙwaƙwalwarsa tana tafarfasa saboda zafinsu, kamar yadda tukunyar tagulla take tafarfasa, kuma ba ya ganin wani mutum ya fi shi tsananin azaba, kuma shi ne mafi sauƙin azabarsu, hakan dan azabar jiki da ta rai su haɗu a kansa.

Fa’idoji
  1. Tsoratar da masu saɓo da kafirai daga tsoron wannan azabar a cikin wuta; dan su nisanci abinda zai kai zuwa gareta.
  2. Banbacin matsayin masu shiga wuta gwargwadan mummunar ayyukansu.
  3. Tsananin azabar wuta, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya kuɓutar da mu daga gareta.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 115) (6561). صحيح مسلم (1/ 196) (213). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 366). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (6/ 394). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 472). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 295). المعجم الوسيط (1/ 256).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SIFFOFIN ALJANNA DA WUTA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com