Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

HAILA DA BIƘI DA ISTIHALA

Hadisai 8

Wannan dinnan jijiya ce, saidai ki bar sallah a gwargwadan kwanukan da kika kasance kina haila a cikinsu, sannan ki yi wanka ki yi Sallah

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤمنين رضي الله عنها أَنَّ فَاطِمَةَ بِنْتَ أَبِي حُبَيْشٍ سَأَلَتِ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَتْ: إِنِّي أُسْتَحَاضُ فَلاَ أَطْهُرُ، أَفَأَدَعُ الصَّلاَةَ؟ فَقَالَ: «لَا، إِنَّ ذَلِكِ عِرْقٌ، وَلَكِنْ دَعِي الصَّلاَةَ قَدْرَ الأَيَّامِ الَّتِي كُنْتِ تَحِيضِينَ فِيهَا، ثُمَّ اغْتَسِلِي وَصَلِّي».
Daga A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - cewa Fatima 'yar Abu Hubaishi ta tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ta ce : Ni ina yin jinin cuta bana tsarkaka, shin zan bar sallah ne? sai ya ce: "A'a, Wannan dinnan jijiya ce, saidai ki bar sallah a gwargwadan kwanukan da kika kasance kina haila a cikinsu, sannan ki yi wanka ki yi Sallah.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Fadima 'yar Hubaishin ta tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ta ce: Lallai ni jini ba ya yanke mini, yana zarcewa har a lokacin da ba na al’ada ba, shin hukuncin hakan zai zama hukuncin al’ada sai inbar sallah? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce mata: Lallai shi jinin cuta ne, shi jinin rashin lafiya ne yana faruwa daga yankewar jijiya a mahaifa, ba jinin haila ba ne, Idan lokacin haila ya zo wanda kika kasance kina haila a cikinsa akan al'adarki ta wata kafin ki yi rashin lafiya da jinin cuta, to ki bar sallah da azimi da wasunsu , na abinda haila take hanawa a lokacin al’ada . Idan gwargwadan lokacin ya kare sai ki zama kin yi tsrki, to sai ki wanke gurin jinin, sannan ki wanke jikinki cikakken wankewa dan dauke hadasi, sannan ki yi sallah.

Fa’idoji
  1. Wajabcin wanka akan mace a yayin karewar kwanukan al’adarta.
  2. Wajabcin sallah akan mai jinin cuta.
  3. Haila: Jini ne na dabi'a da mahaifa take turo shi ta gaban mace baliga, da yake samunta a wasu kwanuka sanannu.
  4. Jinin cuta: Zubar jini ba'a lokacinsa ba daga kasan mahaifa ba daga can cikin mahaifa ba.
  5. Banbanci tsakanin jinin haila da jinin cuta: Cewa jinin haila baki ne mai kauri mai wari, amma jinin cuta to shi jane siriri ba shi da wari.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 72) (325). صحيح مسلم (1/ 262) (333). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص77). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 63). خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص40).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Daga Ummu Habiba ta yi jinin haila na tsawon shekara bakwai, sai ta tambayi Manzo Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi game da haka? sai ya umarce ta da ta yi wanka, tace: ta kasance tana yin wanka a kowace salla.

عن عائشة رضي الله عنها قالت: "إن أم حبيبة اسْتُحِيضَتْ سبع سنين، فسألت رسول الله صلى الله عليه وسلم عن ذلك؟ فأمرها أن تغتسل، قالت: فكانت تغتسل لكل صلاة".
Daga Ummu Habiba ta yi jinin haila na tsawon shekara bakwai, sai ta tambayi Manzo Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi game da haka? sai ya umarce ta da ta yi wanka, tace: ta kasance tana yin wanka a kowace salla.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi -tsira da amincin Allah ya umarci Ummu Habiba da ta yi wanka, a lokacin da ta tambayi shi abin da za ta yi game da jinin istihadha da take fama da shi, don ta kasance tana yin wanka a kowace salla, kuma ta yi fama da jinin istihadwa tsawon shekara bakwai.

Madogara

تأسيس الأحكام للنجمي، ط2، دار علماء السلف، 1414هـ. تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426هـ. تنبيه الأفهام شرح عمدة لأحكام لابن عثيمين، ط1، مكتبة الصحابة، الإمارات، 1426هـ. عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق ، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408هـ. صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422هـ. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Na tambayi Nana A'isha, sai na ce: Me yasa mai al’ada take rama azimi, bata rama sallah?

عَنْ مُعَاذَةَ قَالَتْ: سَأَلْتُ عَائِشَةَ، فَقُلْتُ: مَا بَالُ الْحَائِضِ تَقْضِي الصَّوْمَ، وَلَا تَقْضِي الصَّلَاةَ؟ فَقَالَتْ: أَحَرُورِيَّةٌ أَنْتِ؟ قُلْتُ: لَسْتُ بِحَرُورِيَّةٍ، وَلَكِنِّي أَسْأَلُ. قَالَتْ: كَانَ يُصِيبُنَا ذَلِكَ، فَنُؤْمَرُ بِقَضَاءِ الصَّوْمِ، وَلَا نُؤْمَرُ بِقَضَاءِ الصَّلَاةِ.
Daga Mu'azah ta ce : Na tambayi Nana A'isha, sai na ce: Me yasa mai al’ada take rama azimi, bata rama sallah? Sai ta ce: Shin ke baharuriyyace? na ce: Ni ba baharuriyya ba ce, sai dai tambaya nake. Ta ce: Hakan yana samunmu, sai a umarcemu da rama azimi, ba'a umartarmu da rama sallah.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Mu'azah al'adawiyya - ta tambayi uwar muminai Nana A'isha - Allah Yarda da ita -, sai ta ce: Me yasa mai al’ada take rama azimi, bata rama sallah? Sai ta ce mata: Shin ke daga Khawarijawa Hirarura’a kike ne ? waɗanda suke yawaita tambaya dan ta'annuti da kuma tsanantawa? Na ce: Ni ba baharuriyyababa ce, sai dai tambaya nake yi, ta ce: al’ada tana samunmu tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai a umarcemu da rama azimi, ba'a umartarmu da rama sallah.

Fa’idoji
  1. Yin inkari akan dukkan wanda ya yi tambaya irin ta ta'annitanci da kuma jayayya.
  2. Haruriyya an dangantasu ga wani gari kusa da Kufa, sunansa "Hiraura’a'; wasu jama'a ne daga Khwarijawa, ta kamantata da su ne saboda tsanantawarsu a cikin al'amarinsu da kuma yawan tayambayarsu da ta'annitancinsu da ita.
  3. Malami ya bayyanawa wanda ya neme shi dan neman sani da kuma neman shiriya.
  4. Bada amsa da nassi ya fi; domin cewa Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - bata bijiro da ma'anar da mai tambayar ta tambayeta ba; hakan domin cewa amsa da nassi ya fi yanke musu.
  5. Sallamawa hukuncin Allah da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - koda bawa bai san hikimar ba.
  6. Nawawi ya ce: Ma'anar faɗin Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - cewa wasu jama'a daga Khwarij suna wajabtawa mai al’ada rama sallar da ta wuce a lokacin al’ada, wannan kuwa saɓanin Ijma'in musulmai ne, wannan tambayar da Nana A'isha ta tambayeta tambaya ce ta inkari wato: Wannan hanyar Haruriyya ce tir da wannan hanyar.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 71) (321). صحيح مسلم (1/ 265) (335). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 68). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص81).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Manzo Allah -tsira da aminci ya kasance yana kishingide kan cinya ta, yana karanta Alqur'ani alhali ina haila.

عن عَائِشَة رضي الله عنها قالت: «كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يَتَكِّئُ فِي حِجرِي، فَيَقرَأُ القرآن وأنا حَائِض».
Daga Aisha -Allah ya yarda da ita- tace "Manzon Allah -tsira da amincin Allah- ya kasance yana kishingide kan cinya ta, yana karanta Alqur'ani alhali ina haila"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Aisha-Allah ya yarda da ita- ta fadi cewar Annabi tsira da aminci ya kasance yana kishingida kan cinyarta ya karanta Alqur'ani alhali tana haila, wannan shi ke nuna cewa jikin mai haila tsarkakakke ne, ba ya zama najasa saboda haila.

Madogara

تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق: محمد صبحي حلاق، مكتبة الصحابة، الإمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة: العاشرة 1426هـ. تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، محمد بن صالح العثيمين، مكتبة الصحابة، الإمارات، الطبعة: الأولى 1426هـ. عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، دار الثقافة العربية، دمشق، بيروت، مؤسسة قرطبة، الطبعة: الثانية 1408هـ. صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ. صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Tana kankare shi, sannan ta wanke shi da Ruwa, ta kuma yayyafa masa Ruwa, kuma tayi sallah da shi

عن أسماءَ رضي الله عنها قالت: جاءت امرأةٌ النبيَّ صلى الله عليه وسلم فقالت: أرأَيْتَ إحدانا تَحِيضُ في الثَّوب، كيف تصنعُ؟ قال: «تَحُتُّهُ، ثم تَقْرُصُه بالماء، وتَنْضَحُه، وتُصَلِّي فيه».
Daga Asma'a -Allah ya yarda da ita- ta ce: Wata Mata jazo Wajen Manzon Allah SAW sai ta ce: Mai kake gani xayan mu idan tayi haila a cikin kaya, yaya zata yi? ya ce: "
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

صحيح البخاري، تأليف: محمد بن إسماعيل البخاري، تحقيق: محمد زهير الناصر، الناشر: دار طوق النجاة الطبعة: الأولى، 1422هـ. صحيح مسلم، تأليف: مسلم بن الحجاج النيسابوري، المحقق: محمد فؤاد عبد الباقي - الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت. توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، تأليف: عبد الله بن عبد الرحمن بن صالح البسام، الناشر: مكتبة الأسدي، مكة المكرّمة الطبعة: الخامِسَة، 1423 هـ - 2003 م. نيل الأوطار, محمد بن علي الشوكاني اليمني, تحقيق: عصام الدين الصبابطي, دار الحديث، مصر, الطبعة: الأولى، 1413هـ - 1993م. سبل السلام شرح بلوغ المرام، تأليف : محمد بن إسماعيل بن صلاح الصنعاني، الناشر: دار الحديث الطبعة: بدون طبعة وبدون تاريخ. تسهيل الإلمام بفقه الأحاديث من بلوغ المرام، تأليف: صالح بن فوزان بن عبد الله الفوزان، الطبعة: الأولى، 1427 ه _ 2006 م فتح ذي الجلال والإكرام شرح بلوغ المرام لمحمد بن صالح بن محمد العثيمين، تحقيق: صبحي بن محمد رمضان، وأُم إسراء بنت عرفة، ط1، المكتبة الإسلامية، مصر، 1427ه. منحة العلام في شرح بلوغ المرام، تأليف: عبد الله بن صالح الفوزان، الناشر: دار ابن الجوزي الطبعة: الأولى، 1427 ه - 1431 هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Mun kasance ba ma daukar kalar hanta-hanta da fatsi-fatsi a bakin komai bayan tsarki

عن أُمِّ عَطِيَّةَ رَضي الله عنها، وكَانَتْ بايَعَت النبيَّ صلى الله عليه وسلم، قالت: كُنَّا لا نَعُدّ الكُدرَةَ والصُّفْرَةَ بعدَ الطُّهرِ شيئًا.
Daga Ummu Adiyya - Allah Ya yarda da ita -, ta kasance ta yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - caffa, ta ce: Mun kasance ba ma daukar kalar hanta-hanta da fatsi-fatsi a bakin komai bayan tsarki.
Abu Dawud ne ya ruwaito shi da wannan lafazin, kuma Bukhari ya ruwaito shi ba tare da ƙarin (bayan tsarki) baDarajaIngantacce ne
Sharhi

Sahabiyya Ummu Adiyya - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa mata a zamanin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba sa daukar ruwan da yake fita daga farji - wanda launinsa yake karkata zuwa baƙi, ko fatsi-fatsi - bayan ganin tsarki cewa yana daga al’ada, saboda haka ba sa barin sallah ko azimi saboda shi.

Fa’idoji
  1. Ruwan da yake zuba daga farjin mace - bayan tsarkaka daga al’ada - ba'a izina da shi koda a tare da shi akwai launin hanta-hanta da fatsi-fatsi wanda ya samu ta hanyar jini.
  2. Zubar hanta-hanta da fatsi-fatsi a lokacin al’ada da al'ada ana daukarsa a matsayin al’ada; Domin cewa shi jini ne a lokacinsa, sai dai mai cakuduwa ne da ruwa.
  3. Mace ba ta barin sallah ko azimi saboda hanta-hanta da fatsi-fatsi wanda yake a bayan tsarki, kawai ta yi alwala ta yi sallah.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 72) (326). سنن أبي داود (1/ 226) (307). توضيح الأحكام، للبسام (1/ 450). سُبل السلام، للصنعاني (1/ 153).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ki zauna gwargwadan abinda hailarki take riƙe ki, sannan ki yi wanka

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنينَ رَضي الله عنها أَنَّهَا قَالَتْ: إِنَّ أُمَّ حَبِيبَةَ بِنْتَ جَحْشٍ الَّتِي كَانَتْ تَحْتَ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ عَوْفٍ شَكَتْ إِلَى رَسُولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم الدَّمَ، فَقَالَ لَهَا: «امْكُثِي قَدْرَ مَا كَانَتْ تَحْبِسُكِ حَيْضَتُكِ، ثُمَّ اغْتَسِلِي». فَكَانَتْ تَغْتَسِلُ عِنْدَ كُلِّ صَلَاةٍ.
Daga Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Cewa Ummu Habiba 'yar Jahsh wacce take ƙarƙashin Abdurrahman Dan Awf ta kawo koken (zubar) jini ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce mata: "Ki zauna gwargwadan abinda hailarki take riƙe ki, sannan ki yi wanka". Ta kasance tana wanka a kowacce sallah.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Daya daga cikin sahabbai mata ta kawo koken zubar jini (jinin Istihara) zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da take fama da shi, sai ya umarceta ta dakatar da sallah gwargwadan abinda hailarta take tsareta kafin zuubar wannan al'amarin da ya faru da ita, sannan ta yi wanka ta yi sallah, ta kasance tana wanka dan neman lada a kowacce sallah.

Fa’idoji
  1. Jinin cuta (Wato jinin istihala) shi ne: Fitar jini ya zarce ga mace bayan kwanukan hailarta data saba.
  2. Mai jinin cuta tana daukar kanta mai haila gwargwadan kwanukan da haila taka zo mata a cikinsu, kafin abinda ya sameta ya sameta na jinin cuta.
  3. Idan gwargwadan kwanukan al'adarta na asali suka shude, to ita ana daukarta mai tsarki daga al’ada - koda cewa jinin cuta yana tare da ita - sai ta yi wankan daukewar jinin al’ada.
  4. Mai jinin cuta wanka ba ya wajaba akanta a kowacce sallah; domin wankanta - Allah Ya yarda da ita - ya kasance da ijtihadi ne daga gareta, da a ce ya kasance wajibi ne da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana mata shi.
  5. Alwala tana wajaba akan Mai jinin cuta a kowacce sallah; domin hadasinta madawwami ne ba mai yankewa ba ne, misalinta dukkan wanda karinsa madawwami ne kamar wanda a tare da shi akwai yoyon fitsari, ko fitar tusa mai a koyaushe.
  6. Tambayar ma'abota ilimi daga abinda yake rikitarwa a al'amuran Addini, yayin da wannan matar ta kawo kuka ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ta tambaye shi game da yawan jinin da yake samunta.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 264) (334). توضيح الأحكام، للبسام (1/ 447). شرح النووي على مسلم، (4/ 25). فتح ذي الجلال والإكرام بشرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (1/ 390).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Tsarki ya tabbata ga Allah, wannan daga Shaidan ne don zama a filin ajiye motoci, kuma idan ta ga fitowar ruwan toka a saman ruwan, to sai ta yi ghusl daya na la’asar da la’asar, da kuma wankan daya na Magrib da na dare, daya kuma na nafilar, da na wankan janaba, da kuma yin alwala a tsakani.

عن أسماء بنت عُمَيْس رضي الله عنها قالت: قلت: يا رسول الله، إن فاطمة بنت أبي حُبَيْش اسْتُحِيضَتْ -مُنْذُ كذا وكذا- فلم تُصَل فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «سُبحان الله، إن هذا من الشَّيطان لِتَجْلِسْ في مِرْكَنٍ، فإذا رأت صُفْرَة فوق الماء فلتَغْتَسِل للظهر والعصر غُسْلاً واحدا، وتغتسل للمغرب والعشاء غسلا واحدا، وتغتسل للفجر غسلا واحدا، وتتوضأ فيما بَيْنَ ذلك».
A kan Asmaa bint Umayyis - Allah ya yarda da ita - ta ce: Na ce: Ya Manzon Allah, Fatimah bint Abi Habeesh ta yi haila - tunda irin wannan - kuma ba ta yi salla ba, don haka Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: "Godiya ta tabbata ga Allah, wannan daga Shaidan ne don ya zauna a ciki Kuma idan ta ga wani kirim mai launin rawaya sama da ruwan, to sai ta yi ghusl daya na la’asar da la’asar, da kuma daya maghrib da abincin dare, da kuma ghusl daya don fitowar alfijir, kuma ta yi alwala tsakanin hakan.
Abu Daud Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

سنن أبي داود، تأليف: سليمان بن الأشعث السِّجِسْتاني، تحقيق: محمد محيي الدين عبد الحميد، الناشر: المكتبة العصرية، صيدا. مشكاة المصابيح، تأليف: محمد بن عبد الله التبريزي، تحقيق: محمد ناصر الدين الألباني، الناشر: المكتب الإسلامي، الطبعة: الثالثة، 1985م. تسهيل الإلمام بفقه الأحاديث من بلوغ المرام، تأليف: صالح بن فوزان بن عبد الله الفوزان، الطبعة: الأولى، 1427هـ - 2006 م. توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، تأليف: عبد الله بن عبد الرحمن بن صالح البسام، الناشر: مكتبة الأسدي، مكة المكرّمة، الطبعة الخامِسَة، 1423 هـ - 2003 م. فتح ذي الجلال والإكرام، شرح بلوغ المرام، تأليف: محمد بن صالح بن محمد العثيمين، الناشر: المكتبة الإسلامية، تحقيق: صبحي بن محمد رمضان، وأُم إسراء بنت عرفة. منحة العلام في شرح بلوغ المرام، تأليف: عبد الله بن صالح الفوزان، الناشر: دار ابن الجوزي، الطبعة: الأولى، 1427 هـ ـ 1431هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com