Mu'azah al'adawiyya - ta tambayi uwar muminai Nana A'isha - Allah Yarda da ita -, sai ta ce: Me yasa mai al’ada take rama azimi, bata rama sallah? Sai ta ce mata: Shin ke daga Khawarijawa Hirarura’a kike ne ? waɗanda suke yawaita tambaya dan ta'annuti da kuma tsanantawa? Na ce: Ni ba baharuriyyababa ce, sai dai tambaya nake yi, ta ce: al’ada tana samunmu tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai a umarcemu da rama azimi, ba'a umartarmu da rama sallah.
- Yin inkari akan dukkan wanda ya yi tambaya irin ta ta'annitanci da kuma jayayya.
- Haruriyya an dangantasu ga wani gari kusa da Kufa, sunansa "Hiraura’a'; wasu jama'a ne daga Khwarijawa, ta kamantata da su ne saboda tsanantawarsu a cikin al'amarinsu da kuma yawan tayambayarsu da ta'annitancinsu da ita.
- Malami ya bayyanawa wanda ya neme shi dan neman sani da kuma neman shiriya.
- Bada amsa da nassi ya fi; domin cewa Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - bata bijiro da ma'anar da mai tambayar ta tambayeta ba; hakan domin cewa amsa da nassi ya fi yanke musu.
- Sallamawa hukuncin Allah da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - koda bawa bai san hikimar ba.
- Nawawi ya ce: Ma'anar faɗin Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - cewa wasu jama'a daga Khwarij suna wajabtawa mai al’ada rama sallar da ta wuce a lokacin al’ada, wannan kuwa saɓanin Ijma'in musulmai ne, wannan tambayar da Nana A'isha ta tambayeta tambaya ce ta inkari wato: Wannan hanyar Haruriyya ce tir da wannan hanyar.
صحيح البخاري (1/ 71) (321). صحيح مسلم (1/ 265) (335). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 68). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص81).