Mun kasance ba ma daukar kalar hanta-hanta da fatsi-fatsi a bakin komai bayan tsarki
عن أُمِّ عَطِيَّةَ رَضي الله عنها، وكَانَتْ بايَعَت النبيَّ صلى الله عليه وسلم، قالت: كُنَّا لا نَعُدّ الكُدرَةَ والصُّفْرَةَ بعدَ الطُّهرِ شيئًا.
Daga Ummu Adiyya - Allah Ya yarda da ita -, ta kasance ta yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - caffa, ta ce: Mun kasance ba ma daukar kalar hanta-hanta da fatsi-fatsi a bakin komai bayan tsarki.
Abu Dawud ne ya ruwaito shi da wannan lafazin, kuma Bukhari ya ruwaito shi ba tare da ƙarin (bayan tsarki) baDarajaIngantacce ne
Sharhi
Sahabiyya Ummu Adiyya - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa mata a zamanin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba sa daukar ruwan da yake fita daga farji - wanda launinsa yake karkata zuwa baƙi, ko fatsi-fatsi - bayan ganin tsarki cewa yana daga al’ada, saboda haka ba sa barin sallah ko azimi saboda shi.
Fa’idoji
Ruwan da yake zuba daga farjin mace - bayan tsarkaka daga al’ada - ba'a izina da shi koda a tare da shi akwai launin hanta-hanta da fatsi-fatsi wanda ya samu ta hanyar jini.
Zubar hanta-hanta da fatsi-fatsi a lokacin al’ada da al'ada ana daukarsa a matsayin al’ada; Domin cewa shi jini ne a lokacinsa, sai dai mai cakuduwa ne da ruwa.
Mace ba ta barin sallah ko azimi saboda hanta-hanta da fatsi-fatsi wanda yake a bayan tsarki, kawai ta yi alwala ta yi sallah.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 72) (326).
سنن أبي داود (1/ 226) (307).
توضيح الأحكام، للبسام (1/ 450).
سُبل السلام، للصنعاني (1/ 153).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com