Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

WANKA

Hadisai 24

Daga Ummu Habiba ta yi jinin haila na tsawon shekara bakwai, sai ta tambayi Manzo Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi game da haka? sai ya umarce ta da ta yi wanka, tace: ta kasance tana yin wanka a kowace salla.

عن عائشة رضي الله عنها قالت: "إن أم حبيبة اسْتُحِيضَتْ سبع سنين، فسألت رسول الله صلى الله عليه وسلم عن ذلك؟ فأمرها أن تغتسل، قالت: فكانت تغتسل لكل صلاة".
Daga Ummu Habiba ta yi jinin haila na tsawon shekara bakwai, sai ta tambayi Manzo Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi game da haka? sai ya umarce ta da ta yi wanka, tace: ta kasance tana yin wanka a kowace salla.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi -tsira da amincin Allah ya umarci Ummu Habiba da ta yi wanka, a lokacin da ta tambayi shi abin da za ta yi game da jinin istihadha da take fama da shi, don ta kasance tana yin wanka a kowace salla, kuma ta yi fama da jinin istihadwa tsawon shekara bakwai.

Madogara

تأسيس الأحكام للنجمي، ط2، دار علماء السلف، 1414هـ. تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426هـ. تنبيه الأفهام شرح عمدة لأحكام لابن عثيمين، ط1، مكتبة الصحابة، الإمارات، 1426هـ. عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق ، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408هـ. صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422هـ. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kada dayanku ya yi fitsari a cikin ruwan da ba ya gudana, sannan ya yi wanka da shi.

عن أبي هريرة رضي الله عنه مرفوعاً: "لا يَبُولَنَّ أحَدُكم في الماء الدَّائِم الذي لا يجْرِي، ثمَّ يَغتَسِل مِنه". وفي رواية: "لا يغتسل أحدكُم في الماء الدَّائم وهو جُنُب".
An karbo daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - an daga shi zuwa g Annabi: 'kar waninku ya yi fitsari a cikin ruwan da ba ya gudana, sannan ya yi wanka da shi" A wata ruwayar: 'kar waninku ya yi wanka da ruwan da ba ya gudan alhali yana da janaba"
Muslim ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi mai tsira d a aminci ya yi hani ga yin fitsari a cikin ruwan da ba ya gudana, saboda hakan ka iya janyo cakuduwarsa da najasa da cututtukan da fitsarin ke dauke da su, wanda sa iya cutar da wanda ya yi amfani da su, ta iya yiwuwa mai yin fitsarinma da kanshi zai iya yin wanka da shi. to ta yaya zai yi fitsari cikin abin da zai iya zama abin tsarkinsa. Hakanan kuma ya yi hani ga yin wankan janaba a cikin ruwan da ba ya gudana; saboda yin hakan zai iya bata ruwan da datti da kazantar janaba.

Madogara

تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426 هـ. تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام لابن عثيمين، ط1، مكتبة الصحابة، الإمارات، 1426هـ. عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق ، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408هـ. صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422هـ. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ga wani mutum wanda aka kebe shi kuma ba ya yin salla a tsakanin mutane. Ruwa, sannan ya ce: (Dole ne ku isa gare shi, don ya wadatar da ku).

عن عمران بن حصين رضي الله عنهما أن رسول الله صلى الله عليه وسلم رأى رجلًا مُعتزلًا، لم يُصَلِّ في القوم، فقال: (يا فلان، ما منعك أن تصلي في القوم؟) فقال: يا رسول الله أصابتني جنابةٌ، ولا مَاءَ، فقال: (عليك بالصَّعِيدِ، فإنه يَكْفِيَكَ).
Daga Imran bn Husayn - yardar Allah ta tabbata a gare shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ga wani mutum wanda aka kebe shi kuma ba ya yin salla a tsakanin mutane. Ruwa, sannan ya ce: (Dole ne ku isa gare shi, don ya wadatar da ku).
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

الإلمام بشرح عمدة الأحكام لإسماعيل الأنصاري، ط1، دار الفكر، دمشق، 1381هـ. تيسير العلام شرح عمدة الأحكام للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الأمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426هـ. تنبيه الأفهام شرح عمدة لأحكام لابن عثيمين، ط1، مكتبة الصحابة، الإمارات، 1426هـ. عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق ، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408هـ. صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422هـ. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

‌Tsarki ya tabbata ga Allah, lallai mumini ba ya zama najasa

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنه: أَنَّهُ لَقِيَهُ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي طَرِيقٍ مِنْ طُرُقِ الْمَدِينَةِ وَهُوَ جُنُبٌ، فَانْسَلَّ فَذَهَبَ فَاغْتَسَلَ، فَتَفَقَّدَهُ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَلَمَّا جَاءَهُ قَالَ: «أَيْنَ كُنْتَ يَا أَبَا هُرَيْرَةَ؟» قَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ، لَقِيتَنِي وَأَنَا جُنُبٌ فَكَرِهْتُ أَنْ أُجَالِسَكَ حَتَّى أَغْتَسِلَ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «سُبْحَانَ اللهِ، إِنَّ الْمُؤْمِنَ لَا يَنْجُسُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya haɗu da shi a wata hanya cikin hanyoyin Madina alhali shi yana da janaba, sai ya sulale ya tafi ya yi wanka, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bibiye shi, lokacin da ya zo masa sai ya ce: «‌Ina kake ya Abu Huraira?» sai ya ce: Ya Manzon Allah ka haɗu da ni alhali ni ina da janaba sai na ƙyamaci in zauna da kai har sai na yi wanka, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Tsarki ya tabbata ga Allah, lallai mumini ba ya zama najasa».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya haɗu da Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - a sashin hanyoyin Madina, Abu Huraira ya kasance yana da janaba, kuma yana daga cikin girmamawarsa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ƙyamaci zama da shi da kuma hira da shi alhali shi yana kan wannan halin dan yana zatan cewa shi najasa ne, sai ya tafi a ɓoye ya yi wanka, sannan ya dawo, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambaye shi ina ya tafi? Sai ya sanar da shi halin da yake ciki, kuma cewa shi ya ƙyamaci zama da shi ne alhali shi yana najasa saboda janabar (da ta same shi), sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mamaki kuma ya ce masa: Lallai cewa mumini mai tsarki ne ba ya zama najasa akan kowane hali; a raye ko a mace.

Fa’idoji
  1. Janaba kawai tana hana sallah ne da taɓa Alƙur'ani da kuma zama a cikin masallaci, amma bata hana zama tare da musulmai da kuma fuskantarsu, kuma mai janaba ba ya zama najasa saboda ita.
  2. Tsarkakar mumini a raye ko a mace.
  3. Girmama ma'abota falala, da ilimi, da salaha, da kuma zama da su akan yanayi mai kyau.
  4. Halaccin neman izinin mai bi ga wanda ake bi idan zai tafi, haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - inkarin tafiyarsa ba tare da saninsa ba, hakan domin cewa neman izini yana daga cikin kyakkyawan ladabi.
  5. Faɗin: Subhanal Lahi, a lokacin yin mamaki.
  6. Halaccin zantar da mutum game da kansa da abinda ake jin kunya daga gare shi dan maslaha.
  7. Kafiri najasa ne, sai dai najasarsa ta ma'ana ce dan munin aƙidarsa.
  8. Nawawi ya ce: A cikin wannan hadisin akwai ladubba cewa malami idan ya ga daga wanda yake binsa wani al'amarin da yake jin tsoro a kansa wanda a cikinsa akwai saɓanin daidai to ya tambaye shi, kuma ya faɗa masa daidai, ya kuma bayyana masa hukuncinsa. Allah ne Mafi sani.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 65) (285). صحيح مسلم (1/ 282) (371). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 46). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص61). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 74).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

SIFFAR WANKAN JANABA

عَنْ مَيْمُونَةُ أُمِّ المؤمِنينَ رضي الله عنها قَالتْ: وَضَعْتُ لِلنَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ غُسْلًا، فَسَتَرْتُهُ بِثَوْبٍ، وَصَبَّ عَلَى يَدَيْهِ، فَغَسَلَهُمَا، ثُمَّ صَبَّ بِيَمِينِهِ عَلَى شِمَالِهِ، فَغَسَلَ فَرْجَهُ، فَضَرَبَ بِيَدِهِ الأَرْضَ، فَمَسَحَهَا، ثُمَّ غَسَلَهَا، فَمَضْمَضَ وَاسْتَنْشَقَ، وَغَسَلَ وَجْهَهُ وَذِرَاعَيْهِ، ثُمَّ صَبَّ عَلَى رَأْسِهِ وَأَفَاضَ عَلَى جَسَدِهِ، ثُمَّ تَنَحَّى، فَغَسَلَ قَدَمَيْهِ، فَنَاوَلْتُهُ ثَوْبًا فَلَمْ يَأْخُذْهُ، فَانْطَلَقَ وَهُوَ يَنْفُضُ يَدَيْهِ.
Daga Maimuna Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Na ajiye wa annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ruwan wanka, sai na kare shi da tufafi, sai ya saka a hannayensa, sai ya wankesu, sannan ya zuba da damansa akan hagunsa, sai ya wanke gabansa, sai ya goga hannunsa a kasa, sai ya shafe shi, sannan ya wanke shi, sai ya kuskure baki ya shaƙi ruwa, ya wanke fuskarsa da zira'in hannunsa biyu, sannan ya zuba a kansa sai ya kwaranyo ruwan akan jikinsa, sannan sai ya gusa kadan, sai ya wanke diga-digansa, sai na ba shi tufafi bai karɓa ba, sai ya tafi alhali yana kakkaɓe hannayensa.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Uwar muminai Nana Maimuna - Allah Ya yarda da ita - ta bada labari game da siffar wankan annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - na tsarki, lokacin da ta ajiye masa ruwa dan ya yi wanka da shi, kuma ta kare shi da labule, sai annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aikata abinda ke tafe: N farko: Ya zuba ruwa a hannayensa sai ya wanke su kafin ya shigar da su cikin abin wanka. Na biyu: Ya zuba ruwa da hannunsa na dama akan hannunsa na hagu sai ya wanke gabansa; dan tsarkake shi daga abinda ya maƙale na alamar janaba. Na uku: Ya bugi ƙasa da hannunsa sai ya shafe shi sannan ya wanke shi dan ya gusar da ƙazanta daga gare shi. Na huɗu: Ya kurkure baki; ta hanyar shigar da ruwa a cikin bakinsa ya motsa shi ya kuma kurkure shi sannan ya zubar da shi, sai ya shaƙi ruwa; ta hanyar da ya shigar da ruwa a cikin hancinsa da nunfashinsa, sannan ya fitar da shi dan ya tsarkake shi. Na biyar: Ya wanke fuskarsa da zira'insa biyu. Na shida: Ya zuba ruwa a kansa. Na bakwai: Ya zuba ruwa a sauran jikinsa. Na takwas: Ya juya daga gurinsa sai ya wanke diga-digansa a wani wurin daban ta inda bai wankesu ba kafin nan. Sannan ta kawo masa wani mayafi dan ya tsane da shi, bai karɓa ba, sai ya fara shafe ruwan jikinsa da hannunsa yana karkaɗe shi.

Fa’idoji
  1. Himmatuwar matan annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - da siffanta mafi tsirfafan bayanan rayuwarsa; dan sanar da al'ummarsa.
  2. Wannan siffar wankan ɗaya ce daga cikin siffofin da suka tabbata daga annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - a cikin siffar cikakken wanka na janaba, amma siffa mai isarwa to ita ce ya game jikinsa da ruwa tare da kurkure baki da shaƙa ruwa.
  3. An halatta tsane jiki da mayani ko a bar shi bayan wanka ko alwala.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 63) (276). صحيح مسلم (1/ 254) (317). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص64). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 78).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai yi wankan janaba, sai ya wanke hannayensa, ya yi alwala alwalarsa domin sallah, sannan ya yi wanka

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤمنين رضي الله عنها قَالَتْ: كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا اغْتَسَلَ مِنَ الجَنَابَةِ، غَسَلَ يَدَيْهِ، وَتَوَضَّأَ وُضُوءَهُ لِلصَّلاَةِ، ثُمَّ اغْتَسَلَ، ثُمَّ يُخَلِّلُ بِيَدِهِ شَعَرَهُ، حَتَّى إِذَا ظَنَّ أَنَّهُ قَدْ أَرْوَى بَشَرَتَهُ، أَفَاضَ عَلَيْهِ المَاءَ ثَلاَثَ مَرَّاتٍ، ثُمَّ غَسَلَ سَائِرَ جَسَدِهِ، وَقَالَتْ: كُنْتُ أَغْتَسِلُ أَنَا وَرَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مِنْ إِنَاءٍ وَاحِدٍ، نَغْرِفُ مِنْهُ جَمِيعًا.
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita -: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai yi wankan janaba, sai ya wanke hannayensa, ya yi alwala alwalarsa domin sallah, sannan ya yi wanka, sannan ya tsettsefe gashinsa da hannunsa har sai ya tabbar cewa ya jika fatarsa, sai ya zuba ruwa akansa sau uku, sannan ya wanke ragowar jijkinsa. Ta ce: Na kasance ina wanka ni da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga kwarya daya muna kanfatowa daga gareta gaba daya.
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya yi nufin wankan janaba sai ya fara wanke hannayensa, sannna ya yi alwala kamar yadda yake alwalar sallah, sannan ya zuba ruwa a jikinsa, sannan ya tsattsefe gashin kansa da hannayensa, har sai ya tabbar cewa ruwa yakai tushen gashin, ya jika fatar, sai ya zuba ruwa akansa sau uku sannan ya wanke ragowar jijkinsa. Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Na kasance ina wanka ni da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a kwarya daya, muna kanfatowa daga gareta gaba daya.

Fa’idoji
  1. Wanka (Wankan tsarki) nau'i biyu ne: Mai isarwa da kuma cikakke, amma mai isarwa sai mutum ya yi niyyar tsarki, sannan ya game jikinsa da ruwa tare da kuskurar baki da shaka ruwa. Amma cikakken wanka sai ya yi wanka kamar yadda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wanka a wannan hadisin.
  2. Ana anfani da lafazin janaba ga dukkanin wanda ya fitar da maniyyi, ko ya tara da matarsa koda bai yi maniyyi ba.
  3. Halaccin kallon daya daga ma'aurata al'aurar dayan, da kuma wankansu daga kwarya daya.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 63) (272، 273). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 48). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص62). خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص33).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ya Manzon Allah, Allah baya jin kunya game da gaskiya,shin mace zata yi wanka idan tayi mafarki?sai Manzon Allah -tsira da amincin Allah- yace: Eh, zata yi amma in ta ga ruwa

عن أم سلمة رضي الله عنها قالت: «جاءت أمُّ سُلَيمٍ امرأةُ أَبِي طَلحة إلى رسول الله صلى الله عليه وسلم فقالت: يا رسول الله، إنَّ الله لا يَسْتَحيِي من الحَقِّ، فهل على المرأة من غُسْلٍ إِذَا هِيَ احْتَلَمَت؟ فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم : نعم، إِذَا رَأَت المَاء».
Daga Ummusalama -Allah ya yarda da ita- tace:"Ummu Sulaim Matar Abi Dalha ta zo wajen Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- tace:"Ya Manzon Allah, Allah baya jin kunya game da gaskiya,shin mace zata yi wanka idan tayi mafarki?sai Manzon Allah -tsira da amincin Allah- yace: Eh, zata yi amma in ta ga ruwa."
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Ummu Sulai 'Yar Madina -Allah ya yarda da ita- ta zo wajen Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- don ta tambaye shi,kasancewar tambayar na da alaka da matunci,akan ji kunyar fada,shi ne ta fara gabatar da yan kalmomin don yin shimfida ga tambayar ta. Sai tace: Allah Madukaki shi ne Gaskiya,bai hana ambaton gaskiya,in dai akwai wani amfani cikin tambayar,bayan Ummu Sulaim ta gabatar da wannan shimfida,sai ta fadi tambayarta kai tsaye,tace:shin mace zata yi wanka in tayi mafarki ana saduwa da ita?Sai Annabi tsira da aminci yace,za ta yi wanka indai har ta ga mani.

Madogara

الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري، ط1، دار الفكر، دمشق، 1381هـ. تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام، حققه وعلق عليه وخرج أحاديثه وصنع فهارسه: محمد صبحي بن حسن حلاق، ط10، مكتبة الصحابة، الإمارات - مكتبة التابعين، القاهرة، 1426هـ. تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين، ط1، مكتبة الصحابة، الإمارات، 1426هـ. عمدة الأحكام من كلام خير الأنام صلى الله عليه وسلم، لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، ط2، دار الثقافة العربية، دمشق، بيروت، مؤسسة قرطبة، 1408هـ. صحيح البخاري، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، ط1، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422هـ. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Na kasance ina wanke janaba daga tufafin manzon Allah mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi- sai ya fita izuwa salla, koda ruwa yayi jirwaye a tufafin

عن عائشة رضي الله عنها قالت: ((كُنْت أَغْسِلُ الْجَنَابَةَ مِنْ ثَوْبِ رَسُولِ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم فَيَخْرُجُ إلَى الصَّلاةِ، وَإِنَّ بُقَعَ الْمَاءِ فِي ثَوْبِهِ)). وَفِي رواية: ((لَقَدْ كُنْتُ أَفْرُكُهُ مِنْ ثَوْبِ رَسُولِ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم فَرْكاً، فَيُصَلِّي فِيهِ)).
Daga A`isha -Allah ya kara yarda a gareta- ta ce: ((Na kasance ina wanke janaba daga tufafin manzon Allah mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi sai ya sai ya fita izuwa masallaci, alhalin lallai akwai danshi a jikin tufafin nashi)). a cikin wata ruwayar kuma: ((Hakika na kasance ina kankare shi daga tufafin manzon Allah mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi kamkarewa, sai yayi sallah a cikin shi))An Hanamu bin raka Jana'iza amma kuma ba hanin dole ba
Muslim ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

A`isha Allah ya kara yarda da ita tana ambatar: cewa maniyyin janaba ya kasance yana shafar tufafin manzon Allah mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi, wani lokacin yana kasancewa danye sai ta wankeshi daga tufafin da ruwa, sai ya fita zuwa salla, alhalin ruwan bai gama bushewa daga tufafin ba, wani lokacin daban kuma, maniyyin yana kasancewa busashshe, a wannan lokacin sai ta kankare shi daga tufafin nashi kankarewa, sai yayi salla a cikinsa.

Madogara

تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق: محمد صبحي حلاق، مكتبة الصحابة، الإمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة: العاشرة 1426هـ - 2006م. تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، محمد بن صالح العثيمين، مكتبة الصحابة، الإمارات، الطبعة: الأولى 1426هـ - 2005م. عمدة الأحكام من كلام خير الأنام -صلى الله عليه وسلم-، لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، دار الثقافة العربية، دمشق، بيروت، مؤسسة قرطبة، الطبعة: الثانية 1408ه - 1988م. صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ. صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، 1423هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
8 cikin 19
Hadisai 19
  1. Daga Ummu Habiba ta yi jinin haila na tsawon shekara bakwai, sai ta tambayi Manzo Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi game da haka? sai ya umarce ta da ta yi wanka, tace: ta kasance tana yin wanka a kowace salla.
  2. Kada dayanku ya yi fitsari a cikin ruwan da ba ya gudana, sannan ya yi wanka da shi.
  3. cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ga wani mutum wanda aka kebe shi kuma ba ya yin salla a tsakanin mutane. Ruwa, sannan ya ce: (Dole ne ku isa gare shi, don ya wadatar da ku).
  4. ‌Tsarki ya tabbata ga Allah, lallai mumini ba ya zama najasa
  5. SIFFAR WANKAN JANABA
  6. Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai yi wankan janaba, sai ya wanke hannayensa, ya yi alwala alwalarsa domin sallah, sannan ya yi wanka
  7. Ya Manzon Allah, Allah baya jin kunya game da gaskiya,shin mace zata yi wanka idan tayi mafarki?sai Manzon Allah -tsira da amincin Allah- yace: Eh, zata yi amma in ta ga ruwa
  8. Na kasance ina wanke janaba daga tufafin manzon Allah mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi- sai ya fita izuwa salla, koda ruwa yayi jirwaye a tufafin
  9. Manzon Allah -tsira da aminci su tabbata a gare shi-yana numfashi wajen shan ruwa sau uku
  10. Wanda zai je Juma'a a cikinku to ya yi wanka
  11. Cewa Annabi SAW ya kasance yana wanka da ragowar ruwan Maimuna -Allah ya yarda da ita
  12. Ni da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mun kasance muna wanka daga wani jirgi, wanda hannayenmu suka banbanta da najasa.
  13. Maimakon haka, ya ishe ka jujjuya kan ka sau uku, sai ka zuba ruwa a kanka ka tsarkaka
  14. Lokacin da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana yin ghusl daga najasa, sai ya fara wanke hannayen sa, sa'annan ya wofintar da hannun dama a gefen hagunsa ya wanke al'aurarsa, sannan ya yi alwala don sallah.
  15. Idan dayanku ya zo ga danginsa sannan yana son komawa, to ya yi alwala a tsakaninsu
  16. Duk wanda yayi alwala ranar juma'a zai samu lafiya, kuma duk wanda yayi alwala shine mafi alkhairi
  17. Manzon Allah -tsira da amincin Allah- ya kasance yanayin bacci alahalin yana da Janaba ba tare da ya tava Ruwa ba
  18. Wajibi ne a kan kowanne musulmi ya yi wanka a kowanne kwana bakwai, ya wanke kansa da jikinsa
  19. Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana karantar da mu Alƙur'ani a kowanne hali muddin dai bai kasance yana da janaba ba

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com