Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

SUNNONI DA LADUBBAN WANKA

Hadisai 2

Wanda ya yi wanka irin wankan janaba a ranar Juma`a, sannan ya tafi, kamar ya bayar da sadakar rakuma ne

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَنِ اغْتَسَلَ يَوْمَ الجُمُعَةِ غُسْلَ الجَنَابَةِ ثُمَّ رَاحَ، فَكَأَنَّمَا قَرَّبَ بَدَنَةً، وَمَنْ رَاحَ فِي السَّاعَةِ الثَّانِيَةِ، فَكَأَنَّمَا قَرَّبَ بَقَرَةً، وَمَنْ رَاحَ فِي السَّاعَةِ الثَّالِثَةِ، فَكَأَنَّمَا قَرَّبَ كَبْشًا أَقْرَنَ، وَمَنْ رَاحَ فِي السَّاعَةِ الرَّابِعَةِ، فَكَأَنَّمَا قَرَّبَ دَجَاجَةً، وَمَنْ رَاحَ فِي السَّاعَةِ الخَامِسَةِ، فَكَأَنَّمَا قَرَّبَ بَيْضَةً، فَإِذَا خَرَجَ الإِمَامُ حَضَرَتِ المَلاَئِكَةُ يَسْتَمِعُونَ الذِّكْرَ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yi wanka irin wankan janaba a ranar Juma`a, sannan ya tafi, kamar ya bayar da sadakar rakuma ne, wanda ya tafi a lokaci na biyu, kamar ya bayar da sadakar saniya ne. wanda ya tafi a lokaci na uku kamar ya bayar da sadakar rago ne mai ƙaho. wanda ya tafi a lokaci na huɗu kamar ya bayar da kaza ne, wanda kuma ya tafi a lokaci na biyar kamar ya bayar da ƙwai ne. Idan liman ya fito Mala`iku za su halarto suna sauraron zikiri (Huɗuba)".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari game da falalar gaggawar tafiya zuwa sallar Juma'a. Gaggawa tana farawa ne daga bullowar rana zuwa lokacin zuwan liman; shi ne sa'o'i biyar, ana karkasasu kaso biyar gwargwadan lokaci tsakanin bullowar rana har zuwa shigowar liman da hawansa minbari dan huɗuba: Na farko: Wanda ya yi wanka cikakke kamar wankan janaba, sannan ya tafi masallacin Juma'a a lokaci na farko kamar ya yi sadaka da taguwa ne. Na biyu: Wanda ya tafi a lokaci na biyu kamar ya yi sadaka da saniya ne. Na uku; Wanda ya tafi a lokaci na uku kamar ya yi sadaka ne da rago - shi ne namijin tinkiya - mai ƙahuhhuna. Na huɗu: Wanda ya tafi a lokaci na huɗu kamar ya yi sadaka ne da kaza. Na biyar: Wanda ya tafi a lokaci na biyar kamar ya yi sadaka ne da ƙwai. Idan liman ya fito dan huɗuba; sai mala'ikun da suke zaune a ƙofofi dan rubuta masu shiga masallaci na farko da mai biye da shi sai su dakatar da rubutu, sai su zo suna jin zikiri da huɗuba.

Fa’idoji
  1. Kwaɗaitarwa akan yin wanka ranar Juma'a, kuma yana kasancewa ne kafin tafiya zuwa sallah.
  2. Falalar gaggawa zuwa sallar Juma'a daga farkon sa'o'in yini.
  3. Kwaɗaitarwa akan gaggawa ga ayyuka na gari.
  4. Halartowar mala'iku sallar Juma'a da sauraransu ga huɗuba.
  5. Mala'iku suna ƙofofin masallatai, suna rubuta masu shigowa, na farko sai mai beye da shi, a zuwa sallar Juma'a.
  6. Ibnu Rajab ya ce: Faɗinsa: "Wanda ya yi wanka ranar Juma'a, sannan ya tafi" yana nuni akan cewa wankan da ake so dan Juma'a farkonsa shi ne bullowar alfijir, ƙarshensa kuma tafiya zuwa Juma'a.
Madogara

صحيح البخاري (2/ 3) (881). صحيح مسلم (2/ 582) (850). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله البسام (ص244). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (2/ 308). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، إسماعيل الأنصاري (1/ 196). معالم السنن (شرح سنن أبي داود)، أبو سليمان الخطابي (1/ 109). تهذيب اللغة، محمد الأزهري (14/ 102).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance Sa’i ɗaya na ruwa yana isarsa a wankan tsarki, kuma musun Nabiy ɗaya yana isarsa a alwala

عَنْ سَفِينَةَ رَضيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ: كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُغَسِّلُهُ الصَّاعُ مِنَ المَاءِ مِنَ الجَنَابَةِ، وَيُوَضِّئُهُ المُدُّ.
Daga Safina - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance Sa’i ɗaya na ruwa yana isarsa a wankan tsarki, kuma musun Nabiy ɗaya yana isarsa a alwala.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana wankan tsarki da sa’i ɗaya, kuma yana alwala da mudun Nabiy ɗaya. Sa'i: Mudun Nabiy haɗu ne, mudun Nabiy kuma: Gwargwadan cikin tafuka biyu na mutum madaidaicin halitta.

Fa’idoji
  1. Halaccin tattali a ruwan alwala da wanka, da rashin ɓarna, koda ruwan ya kasance mai sauƙin samu ne.
  2. An so ƙaranta ruwan alwala da wanka gwargwadan buƙata, kuma wannan ita ce shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  3. Abin nufi cikawa a alwala da wanka tare da kula da sunnoni da ladubba ba tare da ɓarna ko ƙwauro ba, kuma a kiyaye lokaci da yawan ruwan da ƙarancinsa da wanin hakan.
  4. Ana anbaton janaba ga dukkan wanda ya fitar da maniyyi ko ya yi jima'i, kuma an anbaceta da hakan dan mai ita yana nisantar sallah da ibadu har sai ya tsarkaka daga gareta.
  5. Sa'i: wani abin awo ne sananne, abin nufi da shi sa'in Annabi, awonsa ya kai nauyi (480) na alkama mai kyau, a lita kuma (lita 3).
  6. Mudun Nabiy: Awo ne na shari'a, shi kuma cikin tafuka biyu ne na mutum madaidaici idan ya cikasu ya miƙe hannunsa da su. Mudun Nabiy shi ne ɗaya bisa huɗu na sa'i da haɗuwar masana fiƙihu, gwargwadansa ML (750).
Madogara

صحيح مسلم (1/ 258) (326). البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (8/ 52).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com