عَنْ حُذَيْفَةَ رضي الله عنه قَالَ: كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا قَامَ مِنَ اللَّيْلِ يَشُوصُ فَاهُ بِالسِّوَاكِ.
Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya tashi da daddare yana goge bakinsa da asuwaki.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance lokuta da yawa yana yin asuwaki kuma yana umarni da a yi shi, hakan yana karfafuwa a wasu lokuta, daga cikinsu: Asuwaki lokacin tashi da daddare, lokacin da tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cuccuɗawa kuma yana wanke bakinsa da asuwaki.
Fa’idoji
- Karfafuwar halaccin asuwaki bayan baccin dare, hakan domin barci yana hukunta canzawar bashin baki ne, shi kuma asuwaki shi ne kayan tsaftace shi.
- Karfafuwar halaccin asuwaki a lokacin canjawar bashi a baki, dan yin riko da ma'anar data gabata.
- Shar’antuwar tsafta ta fuskar gamewa, kuma ita tana daga sunnar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma tana daga manyan ladubba.
- Yin asuwaki a baki gabaɗayansa ya kunshi: Hakora, da dadashi, da harshe.
- Asuwaki shi ne itacen da ake yanko shi daga bishiyar kirya ko waninta, ana anfani da shi a tsaftace baki da hakora, kuma yana daɗaɗa baki, yana gusar da warin da ba'a so.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 58) (245).
صحيح مسلم (1/ 220) (255).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص47).
خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص24).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبِي هريرة رضي اللَّه عنه: سمعتُ النبِيّ صلى الله عليه وسلم يقول: «الفِطْرَةُ خمسٌ: الخِتَانُ والاستحدادُ وقصُّ الشَّارِبِ وتقليمُ الأظفارِ وَنَتْفُ الآبَاطِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Dabi'a (ta addinin Musulunci ) guda biyar ce: Kaciya da aske gashin mara, da rage gashin baki, da yanke farata, da tsige gashin hammata".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana ɗabi'u biyar daga addinin Musulunci da kuma sunnonin manzanni:
Na farkonsu: Kaciya, ita ce yanke fatar da ta ƙaru a kan azzakari wajen kan kaciya, da kuma yanke kan fata a farjin mace a saman bigiren mashigar azzakari.
Na biyunsu: Aske gashin mara, shi ne aske gashin mara wanda ke gefen gaba.
Na ukunsu: Rage gashin baki, shi ne rage abin da ya tsiro a kan leɓen sama na namiji inda leɓe yake bayyana.
Na huɗunsu: Yanke farata.
Na biyar ɗinsu: Aske gashin hammata.
Fa’idoji
- Sunnonin manzanni waɗanda Allah Yake sonsu kuma Ya yarda da su, Yake umarni da su, suna kira zuwa ga cika da tsafta da kyau.
- Halaccin lazimtar waɗannan abubuwan, da kuma rashin rafkana daga garesu.
- Akwai fa'idoji na addini da rayuwa cikin waɗannan ɗabi'un: Daga cikinsu akwai: Kyautata yanayin mutum, da tsaftace jiki, da tabbatar da tsarki, da saɓawa kafirai, da riko (aiwatar da) umarnin Allah.
- Awasu hadisan daban an ambaci ƙarin wasu ɗabi'un banda waɗannan biyar ɗin, kamar: Cika gemu, da asuwaki, da wasunsu.
Madogara
صحيح البخاري (7/ 160) (5891).
صحيح مسلم (1/ 222) (257).
عمدة الأحكام (ص44) (30).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 45).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص58).
تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 72).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن ابن عمر رضي الله عنهما عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «أحْفُوا الشَّوَارِبَ وأَعْفُوا اللِّحَى».
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku rage gashin baki, ku cika gemu".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana umarni da rage gashin baki, kuma kada a barshi, kawai a rageshi, kuma a kai matuƙa a hakan.
A ɗaya ɓangaren kuma yana umarni da cika gemu da kuma barinsa a cike.
Fa’idoji
- Haramcin aske gemu.
Madogara
صحيح البخاري (7/ 160) (5892).
صحيح مسلم (1/ 222) (259).
رياض الصالحين (ص338) (1205).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 345).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخِن (2/ 853).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 228).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (14/ 507).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص676).
منار القاري شرح مختصر صحيح البخاري، لحمزة محمد قاسم (5/ 236).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي موسى الأشعري رضي الله عنه قال: ((أتَيتُ النبي صلى الله عليه وسلم وهو يَسْتَاكُ بِسِوَاك رَطْب، قال: وطَرَفُ السِّوَاك على لسانه، وهو يقول: أُعْ، أُعْ، والسِّوَاك في فِيه، كأنَّه يَتَهَوَّع)).
Daga Abu Musa Al-Ash'ari - yardar Allah ta tabbata a gare shi - ya ce: (((Na zo wa Annabi - Salatin Allah da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da yake amfani da abin goge baki), sai ya ce: Karshen sawa yana kan harshensa, sai ya ce: Ya, ka taimaka, kuma tsabtar tana cikin ta, kamar yana cikinta).
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، إسماعيل بن محمد الأنصاري، دار الفكر، دمشق، الطبعة: الأولى، 1381هـ.
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، عبد الله بن عبد الرحمن البسام، تحقيق: محمد صبحي حلاق، مكتبة الصحابة، الأمارات، مكتبة التابعين، القاهرة، الطبعة: العاشرة، 1426هـ.
تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، محمد بن صالح العثيمين، مكتبة الصحابة، الإمارات، الطبعة: الأولى، 1426هـ.
عمدة الأحكام من كلام خير الأنام -صلى الله عليه وسلم-، لعبد الغني المقدسي، دراسة وتحقيق: محمود الأرناؤوط، مراجعة وتقديم: عبد القادر الأرناؤوط، دار الثقافة العربية، دمشق، بيروت، مؤسسة قرطبة، الطبعة: الثانية، 1408هـ.
صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى، 1422هـ.
صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أنس رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «أكْثَرْتُ عليكم في السِّوَاك».
Daga Anas Dan Malik - Allah ya yarda da shi - ya ce Manon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Na yawaita muku magana kan Aswaki"
Buhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Ma'anar hadisin: Cewa Annabi –SAW- ya kasance mafi muhimmanci ga al-ummarsa a cikin sha'anin amfani da siwaaki da kuma juriya da shi a dukkan lamura, kamar yadda yake mustahabbi ne, ba mai kyau ba Wancan kuwa saboda manyan fa'idodi da kyawawan halaye da ke ƙunshe a ciki, kuma don girmanta kuma mafi girma daga cikinsu shi ne cewa yarda ne ga Ubangiji - tsarki ya tabbata a gare Shi.
Madogara
رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين؛ للإمام أبي زكريا النووي، تحقيق د. ماهر الفحل، دار ابن كثير-دمشق، الطبعة الأولى، 1428ه .
- بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين؛ تأليف سليم الهلالي، دار ابن الجوزي- الطبعة الأولى1418ه
- نزهة المتقين شرح رياض الصالحين؛ تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة-بيروت، الطبعة الرابعة عشر، 1407هـ.
- صحيح البخاري –الجامع الصحيح-؛ للإمام أبي عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري، عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عائشة رضي الله عنها قالت: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «السِّوَاكُ مَطْهَرَةٌ لِلْفَمِ، مَرْضَاةٌ لِلرَّبِّ».
Daga Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yace: "Asiwaki mai tsarkake baki ne, mai sa yardar Ubangiji ne".
Nasa'i ne ya ruwaito shi da AhmadDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana sanar damu cewa tsaftace hakora da itaciyar urak da makamancinta yana tsaftace baki daga datti da wari wadanda suke abin ki. Kuma cewa shi yana daga sabubban yardar Allah ga bawa; domin cewa a cikinsa akwai biyayya ga Allah da amsa umarninSa, da kuma abinda ke cikinsa na tsaftar da Allah - Madaukakin sarki - yake son ta.
Fa’idoji
- Falalar asiwaki, da kwadaitarwar da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi ga al'ummarsa da yawaitawa hakan.
- Abinda yafi ga asiwaki shi ne yin amfani da itacan urak (kirya), yin amfani da makilin da burush yana tsayawa a madadinta.
Madogara
سنن النسائي (1/ 10) (5).
مسند أحمد (40/ 240) (24203).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 342).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمصطفى الخِن وغيره (2/ 852).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص675).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنِ شُرَيْحٍ بنِ هانِئٍ قَالَ: سَأَلْتُ عَائِشَةَ، قُلْتُ: بِأَيِّ شَيْءٍ كَانَ يَبْدَأُ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا دَخَلَ بَيْتَهُ؟ قَالَتْ: بِالسِّوَاكِ.
Daga Shuraih ɗan Hani'i ya ce: Na tambayi Nana A'isha, na ce: Da wane abu Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yakasance yake farawa idan ya shiga gidansa? ta ce: Da asuwaki.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Ya kasance daga shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne yana farawa da asuwaki idan ya shiga gidansa a kowane lokaci da daddare ko da rana.
Fa’idoji
- Halaccin yin asuwaki a game a dukkan lokuta, hakan yana ƙarfafa: A cikin lokutan da Shari’a ta so (a yi asuwaki) a cikinsu, daga garesu: A yayin shiga gida, da lokacin sallah, da lokacin alwala, da bayan farkawa daga bacci, da lokacin canjawar bashin baki.
- Bayanin kwaɗayin tabi'ai akan tambaya game da halayen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da sunnoninsa; dan su yi koyi da shi.
- Ɗaukar ilimi daga ma'abotansa daga kuma wanda ya fi shi sani, inda aka tambayi Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - game da halin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a lokacin shiga gida.
- Kyakkyawan mu'amalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga iyalansa, inda ya kasance yana tsarkake bakinsa a lokacin shiga gida.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 220) (253).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 341).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 851).
المنهاج شرح صحيح مسلم بن الحجاج، النووي (3/ 144).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عائشة رضي الله عنها مرفوعاً: «عَشْرٌ من الفِطْرة: قَصُّ الشَارب، وإعْفَاء اللِّحْية، والسِّواك، وَاسْتِنْشَاقُ الماء، وقص الأظْفَار، وغَسْل البَرَاجِم، ونَتْف الإبْط، وحلق العَانة، وانْتِقَاصُ الماء» قال الراوي: ونَسِيْتُ العاشرة إلا أن تكون المَضْمَضَة. قال وكِيع - وهو أحد رواته - انْتِقَاص الماء: يعني الاسْتِنْجَاء.
cikin hadisin A’isha - Allah Ya yarda da ita - da isnadi: “Goma daga cikin ranakun azumi: yanke gashin baki, barin gemu, amfani da abin goge baki, shakar ruwa, yanke farce, wanke farce, da wankin kwarkwata, guntun kafa da makogwaro.” Wakeh - wanda yana daga cikin maruwaitansa - ya ce, "Alwala na ruwa": na nufin tsarkakewa.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
- رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين؛ للإمام أبي زكريا النووي، تحقيق د. ماهر الفحل، دار ابن كثير-دمشق، الطبعة الأولى، 1428ه.
- دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين؛ لمحمد بن علان الشافعي، دار الكتاب العربي-بيروت
- بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين؛ تأليف سليم الهلالي، دار ابن الجوزي- الطبعة الأولى1418ه
- نزهة المتقين شرح رياض الصالحين؛ تأليف د. مصطفى الخِن وغيره، مؤسسة الرسالة-بيروت، الطبعة الرابعة عشر، 1407هـ.
- صحيح مسلم؛ للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبد الباقي، دار عالم الكتب-الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ.
- تطريز رياض الصالحين؛ تأليف فيصل آل مبارك، تحقيق د. عبد العزيز آل حمد، دار العاصمة-الرياض، الطبعة الأولى، 1423هـ.
- كنوز رياض الصالحين، لحمد بن ناصر العمار، دار كنوز إشبيليا- الطبعة الأولى1430ه
- شرح رياض الصالحين؛ للشيخ محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن، الرياض، 1426هـ.
- بهجة قلوب الأبرار وقرة عيون الأخيار في شرح جوامع الأخبار :عبد الرحمن بن سعدي - المحقق: عبد الكريم بن رسمي ال الدريني دار النشر: مكتبة الرشد للنشر والتوزيع الطبعة: الأولى 1422هـ - 2002م
- فتاوى اللجنة الدائمة للبحوث العلمية والإفتاء - المجموعة الأولى - رئاسة إدارة البحوث العلمية والإفتاء - الإدارة العامة للطبع - الرياض.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com