عَنِ شُرَيْحٍ بنِ هانِئٍ قَالَ: سَأَلْتُ عَائِشَةَ، قُلْتُ: بِأَيِّ شَيْءٍ كَانَ يَبْدَأُ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا دَخَلَ بَيْتَهُ؟ قَالَتْ: بِالسِّوَاكِ.
Daga Shuraih ɗan Hani'i ya ce: Na tambayi Nana A'isha, na ce: Da wane abu Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yakasance yake farawa idan ya shiga gidansa? ta ce: Da asuwaki.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Ya kasance daga shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne yana farawa da asuwaki idan ya shiga gidansa a kowane lokaci da daddare ko da rana.
Fa’idoji
- Halaccin yin asuwaki a game a dukkan lokuta, hakan yana ƙarfafa: A cikin lokutan da Shari’a ta so (a yi asuwaki) a cikinsu, daga garesu: A yayin shiga gida, da lokacin sallah, da lokacin alwala, da bayan farkawa daga bacci, da lokacin canjawar bashin baki.
- Bayanin kwaɗayin tabi'ai akan tambaya game da halayen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da sunnoninsa; dan su yi koyi da shi.
- Ɗaukar ilimi daga ma'abotansa daga kuma wanda ya fi shi sani, inda aka tambayi Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - game da halin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a lokacin shiga gida.
- Kyakkyawan mu'amalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga iyalansa, inda ya kasance yana tsarkake bakinsa a lokacin shiga gida.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 220) (253). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 341). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 851). المنهاج شرح صحيح مسلم بن الحجاج، النووي (3/ 144).