Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Dabi'a (ta addinin Musulunci ) guda biyar ce: Kaciya da aske gashin mara, da rage gashin baki, da yanke farata, da tsige gashin hammata

عن أبِي هريرة رضي اللَّه عنه: سمعتُ النبِيّ صلى الله عليه وسلم يقول: «الفِطْرَةُ خمسٌ: الخِتَانُ والاستحدادُ وقصُّ الشَّارِبِ وتقليمُ الأظفارِ وَنَتْفُ الآبَاطِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Dabi'a (ta addinin Musulunci ) guda biyar ce: Kaciya da aske gashin mara, da rage gashin baki, da yanke farata, da tsige gashin hammata".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana ɗabi'u biyar daga addinin Musulunci da kuma sunnonin manzanni: Na farkonsu: Kaciya, ita ce yanke fatar da ta ƙaru a kan azzakari wajen kan kaciya, da kuma yanke kan fata a farjin mace a saman bigiren mashigar azzakari. Na biyunsu: Aske gashin mara, shi ne aske gashin mara wanda ke gefen gaba. Na ukunsu: Rage gashin baki, shi ne rage abin da ya tsiro a kan leɓen sama na namiji inda leɓe yake bayyana. Na huɗunsu: Yanke farata. Na biyar ɗinsu: Aske gashin hammata.

Fa’idoji
  1. Sunnonin manzanni waɗanda Allah Yake sonsu kuma Ya yarda da su, Yake umarni da su, suna kira zuwa ga cika da tsafta da kyau.
  2. Halaccin lazimtar waɗannan abubuwan, da kuma rashin rafkana daga garesu.
  3. Akwai fa'idoji na addini da rayuwa cikin waɗannan ɗabi'un: Daga cikinsu akwai: Kyautata yanayin mutum, da tsaftace jiki, da tabbatar da tsarki, da saɓawa kafirai, da riko (aiwatar da) umarnin Allah.
  4. Awasu hadisan daban an ambaci ƙarin wasu ɗabi'un banda waɗannan biyar ɗin, kamar: Cika gemu, da asuwaki, da wasunsu.
Madogara

صحيح البخاري (7/ 160) (5891). صحيح مسلم (1/ 222) (257). عمدة الأحكام (ص44) (30). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 45). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص58). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 72).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SUNNONIN FITRA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com