Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya tashi da daddare yana goge bakinsa da asuwaki

عَنْ حُذَيْفَةَ رضي الله عنه قَالَ: كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا قَامَ مِنَ اللَّيْلِ يَشُوصُ فَاهُ بِالسِّوَاكِ.
Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya tashi da daddare yana goge bakinsa da asuwaki.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance lokuta da yawa yana yin asuwaki kuma yana umarni da a yi shi, hakan yana karfafuwa a wasu lokuta, daga cikinsu: Asuwaki lokacin tashi da daddare, lokacin da tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cuccuɗawa kuma yana wanke bakinsa da asuwaki.

Fa’idoji
  1. Karfafuwar halaccin asuwaki bayan baccin dare, hakan domin barci yana hukunta canzawar bashin baki ne, shi kuma asuwaki shi ne kayan tsaftace shi.
  2. Karfafuwar halaccin asuwaki a lokacin canjawar bashi a baki, dan yin riko da ma'anar data gabata.
  3. Shar’antuwar tsafta ta fuskar gamewa, kuma ita tana daga sunnar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma tana daga manyan ladubba.
  4. Yin asuwaki a baki gabaɗayansa ya kunshi: Hakora, da dadashi, da harshe.
  5. Asuwaki shi ne itacen da ake yanko shi daga bishiyar kirya ko waninta, ana anfani da shi a tsaftace baki da hakora, kuma yana daɗaɗa baki, yana gusar da warin da ba'a so.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 58) (245). صحيح مسلم (1/ 220) (255). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص47). خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص24).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SUNNONIN FITRA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com