Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

An sa mana lokaci a rage gashin baki, da yanke farata, da cire gashin hammata, da aske gashin mara, kada mu bari sama da dare arba'in

عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: وُقِّتَ لَنَا فِي قَصِّ الشَّارِبِ، وَتَقْلِيمِ الْأَظْفَارِ، وَنَتْفِ الْإِبِطِ، وَحَلْقِ الْعَانَةِ، أَلَّا نَتْرُكَ أَكْثَرَ مِنْ أَرْبَعِينَ لَيْلَةً.
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: An sa mana lokaci a rage gashin baki, da yanke farata, da cire gashin hammata, da aske gashin mara, kada mu bari sama da dare arba'in.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iyakance akan rage gashin bakin namiji, da yanke farcen hannaye da ƙafafuwa, da cire gashin hammata, da aske gashin mara, cewa kada a barsu sama da kwanaki arba'in.

Fa’idoji
  1. Shaukani ya ce: Abin aka fi so shi ne a iyakance kwana arba'in waɗanda manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iyakance su dan haka ba ya halatta a ƙetaresu, wanda ya bar askewar da makamncinsa bayan tsawo har zuwa ƙarshen waccan lokacin na kwanaki arba’in to ba za'a ƙirga shi cikin wanda ya saɓawa sunnah ba.
  2. Ibnu Hubaira ya ce: Wannan hadisin shi ne matuƙa a jinkirta hakan, abinda ya fi a yi riƙo da ƙasa da wannan matuƙar.
  3. Kulawar musulunci da tsafta da tsarkaka da kuma ado.
  4. Rage gashin baki, shi ne a rage wasu daga gashin da ya tsiro akan leɓe na sama.
  5. Cire gashin hammata, yana kasancewa ne da kawar da gashin da yake tsirowa da shi, shi ne gurin da yake kasancewa ƙasan mararrabar zira'i da kafaɗa.
  6. Aske gashin mara, shi ne gashi mai kaushi wanda ya tsiro a gefen gaba daga namiji da mace.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 222) (258). شرح سنن أبي داود لابن رسلان (16/ 559). مرشد ذوي الحجا والحاجة إلى سنن ابن ماجه والقول المكتفى على سنن المصطفى (3/ 115).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SUNNONIN FITRA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com