عَن أَبِي أُمَامَةَ قَالَ: حَدَّثَنِي عَمْرُو بْنُ عَبَسَةَ رضي الله عنه أَنَّهُ سَمِعَ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «أَقْرَبُ مَا يَكُونُ الرَّبُّ مِنَ العَبْدِ فِي جَوْفِ اللَّيْلِ الآخِرِ، فَإِنْ اسْتَطَعْتَ أَنْ تَكُونَ مِمَّنْ يَذْكُرُ اللَّهَ فِي تِلْكَ السَّاعَةِ فَكُنْ».
Daga Abu Umamah ya ce: Amr ɗan Abasa - Allah Ya yarda da shi - ya zantar da ni cewa shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Mafi kusancin lokacin da bawa yake kasancewa kusa da Ubangiji a cikin (kason) dare na karshe, idan kana da ikon ka kasance daga wanda yake ambatan Allah a wannan lokacin to ka kasance".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Ubangiji - tsarki ya tabbatar maSa - Shi ne mafi kusa ga bawa a lokacin sulusin dare na karshe; idan an datar da kai kuma ka samu iko - ya kai mumini - da ka kasance daga jumlar masu bauta masu sallah masu ambatan Allah masu tuba a wannan lokacin to shi wani al'amari ne wanda yana kamata a ci ribarsa da kokari a cikinsa.
Fa’idoji
- Kwaɗaitar da musulmi akan zikiri a karshen dare.
- Fifikon lokuta a tsakaninsu ga zikiri da addu'a da sallah.
- Mirik ya ce: A cikin banbanci tsakaknin faɗinsa: "Mafi kusancin lokacin da Ubangiji ya fi kusa da bawa", da tsakanin faɗinsa: " Mafi kusancin lokacin da bawa yake kusa da Ubangijinsa alhali shi yana mai sujjada': Abin nufi a nan bayanin lokacin kasancewar Ubangiji Shi ne mafi kusa ga bawa shi ne tsakiyar dare, abin nufi a can bayanin kusancin halayen bawa ga Ubangiji alhali shi yana halin sujjada.
Madogara
سنن الترمذي (5/ 537) (3579).
سنن أبي داود (2/ 454) (1277).
سنن النسائي (1/ 279) (572).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 1019).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 509).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (17/ 535).
مشكاة المصابيح، للتبريزي (1/ 387).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَيُّهَا النَّاسُ، إِنَّ اللهَ طَيِّبٌ لَا يَقْبَلُ إِلَّا طَيِّبًا، وَإِنَّ اللهَ أَمَرَ الْمُؤْمِنِينَ بِمَا أَمَرَ بِهِ الْمُرْسَلِينَ، فَقَالَ: {يَا أَيُّهَا الرُّسُلُ كُلُوا مِنَ الطَّيِّبَاتِ وَاعْمَلُوا صَالِحًا، إِنِّي بِمَا تَعْمَلُونَ عَلِيمٌ} [المؤمنون: 51] وَقَالَ: {يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُلُوا مِنْ طَيِّبَاتِ مَا رَزَقْنَاكُمْ} [البقرة: 172] ثُمَّ ذَكَرَ الرَّجُلَ يُطِيلُ السَّفَرَ أَشْعَثَ أَغْبَرَ، يَمُدُّ يَدَيْهِ إِلَى السَّمَاءِ: يَا رَبِّ، يَا رَبِّ، وَمَطْعَمُهُ حَرَامٌ، وَمَشْرَبُهُ حَرَامٌ، وَمَلْبَسُهُ حَرَامٌ، وَغُذِيَ بِالْحَرَامِ، فَأَنَّى يُسْتَجَابُ لِذَلِكَ؟».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ya ku mutane ! Lallai Allah Mai tsarki ne ba Ya karba sai mai tsarki, kuma Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci Manzanni da shi, sai Ya ce:
{Ya ku Manzanni ku ci daga tsarkaka kuma ku aikata aiki na gari, lallai cewa Ni Masani ne da abinda kuke aikatawa}.
[al-Mu'uminun: 51] .
Kuma Ya ce: {Ya ku waɗanda suka yi imani ku ci daga tsarkakan abinda muka azirta ku}. [al:Baƙara: 172]. Sannan ya ambaci mutumin da yake tsawaita tafiya kansa ya cukurkuɗe, jikinsa ya yi ƙura, yana ɗaga hannayensa sama: Ya Ubangiji, ya Ubangiji, abin cinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, abin ɗaurawarsa haramun ne, an shayar da shi da haram, to tayaya za'a amsa masa ga hakan?".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah tsarkakakke ne, tsarkakakke abin tsarkakewa daga nakasa kowacce iri da aibuka, kuma Mai siffantuwa ne da cika, ba Ya karɓar ayyuka da maganganu da ƙudirce-ƙudirce sai abinda ya kasance mai tsarki, shi ne tsantsa saboda Allah, wanda ya dace da shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, baya kamata a nemi kusanci zuwa ga Allah sai da hakan, daga mafi girman abinda tsarkin ayyuka yake faruwa ga mumini tsarkin abin cinsa, kuma ya zama na halal ne, da hakan ne aikinsa zai tsarkaka, saboda haka ne Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci manzanni da shi, na cin halal da aiki na gari, sai Ya ce: {Ya ku Manzanni ku ci daga tsarkaka kuma ku aikata aiki na gari, lallai Ni Masani ne da abinda kuke aikatawa} kuma Ya ce: {Ya ku wadanda suka yi imani ku ci daga tsarkakan abinda muka azirtaku}.
Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya gargaɗar daga cin haram wanda yake ɓata aiki kuma yake hana karɓarsa duk irin kokarin da ya yi na sabubban karɓar na zahiri; daga cikinsu:
Na farko: Tsawaita tafiya ta fuskokin ayyukan ɗa'a kamar hajji da jihadi da sada zumunci da wanin hakan.
Na biyu: Cukurkuɗar gashi dan rashin taje shi, wanda launinsa ya canja da launin tufansa daga turɓaya, shi mabuƙaci ne.
Na uku: Yana ɗaga hannayensa sama da addu'a.
Na huɗu: Yana tawassuli zuwa ga Allah da sunayenSa kuma yana nacewa a cikin hakan (yana cewa): Ya Ubangiji ya Ubangiji!
A tare da waɗannan sabubban na amsar addu'a ba'a saurare shi ba; hakan saboda abin cinsa da abin shansa da abin ɗaurawarsa haramun ne, kuma an shayar da shi da haram, to ya nisanta a amsa wa wanda wannan ita ce siffarsa, to ta yaya za'a amsa masa?!
Fa’idoji
- Cikar Allah - Mai girma da ɗaukaka - a cikin zatinSa, da siffofinSa, da ayyukanSa, da hukunce-hukuncenSa.
- Umarni da tsarkake aiki saboda Allah - Mai girma da ɗaukaka -, da bin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Anfani da abinda yake ƙarfafa gwiwa akan aiki, inda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci Manzanni da shi", idan mumini ya san cewa wannan yana daga abubuwan da aka umarci Manzanni to cewa shi zai ƙarfafu zai ji ƙwarin gwiwa akan riko da shi.
- Daga abubuwan da suke hana amsar addu'a (akwai) cin haram.
- Daga cikin sabubban amsar addu'a (akwai) abubuwa biyar: Na farkonsu: Tsawaita tafiya dan abinda ke cikinta na karyewar zuciya wanda shi yana daga mafi girman sabubban amsa addu'a. Na biyu: Halin buƙatuwa. Na uku: Ɗaga hannaye zuwa sama. Na huɗu: Nacewa Allah da maimaita ambatan RububiyyarSa, kuma shi yana daga mafi girman abinda ake neman amsa addu'a da shi. Na biyar: Daddadan abin ci da abin sha.
- Cin halal mai tsarki yana daga sabubba masu taimakawa ga aiki na gari.
- AlƘali ya ce: Mai tsarki kishiyar mummuna ne, idan Allah Maɗaukakin sarki ya siffanta shi da shi ana nufi da shi cewa shi abin tsarkakewa ne daga dukkanin tawaya abin tsarkakewa daga aibuka, idan aka siffanta bawa da shi kai tsaye ana nufi da shi cewa shi mai tsiraita ne daga munanan ɗabi'u kuma mai siffantuwa da kishiyoyin hakan, idan aka siffanta dukiyoyi da shi ana nufin kasancewarta halal ce kuma tana daga zaɓaɓɓun dukiyoyi.
Madogara
صحيح مسلم (2/ 703) (1015).
التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية، لإسماعيل الأنصاري (ص27).
شرح الأربعين النووية، لابن عثيمين (ص141).
الأحاديث الأربعين النووية مع ما زاد عليها ابن رجب وعليها الشرح الموجز المفيد (ص22).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن سهل بن سعد رضي الله عنهما مرفوعاً: «ثنتان لا تُرَدَّانِ، أو قلما تردان: الدعاء عند النداء وعند البأس حِينَ يُلْحِمُ بَعْضُهُ بَعْضًا».
Daga Sahl bin Saad - yardar Allah ta tabbata a gare su - a cikin marfoo ': "Ba a juya mata biyu baya, ko kuma ba safai ake dawo da su ba: Addu'a a lokacin kira da karfin hali, idan aka hade ta."
Abu Daud Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
A cikin wannan hadisin bayani ne a kan falalar jihadi saboda Allah ta yadda Allah - Madaukaki - ke amsa kiran mujahid yayin da yake cikin yaki, haka nan kuma ya bayyana falalar kiran salla yayin da Allah - Madaukaki - ke amsa addu'ar Musulmi a kiran salla da har sai an tsayar da salla.
Madogara
سنن أبي داود، تحقيق: محمد محيي الدين عبد الحميد: المكتبة العصرية، صيدا - بيروت.
كنوز رياض الصالحين بإشراف حمد العمار, دار كنوز إشبيليا, الطبعة الأولى, 1430ه.
دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين لمحمد بن علان الصديقي,تحقيق خليل مأمون شيحا-دار المعرفة-بيروت-الطبعة الرابعة 1425ه.
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين لمجموعة من الباحثين, مؤسسة الرسالة, الطبعة الرابعة عشرة, 1407ه.
صحيح أبي داود، للشيخ الألباني ، مؤسسة غراس، الكويت. الطبعة : الأولى ، 1423 هـ - 2002 م.
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين؛ تأليف سليم الهلالي، دار ابن الجوزي- الطبعة الأولى1418ه.
شرح رياض الصالحين؛ للشيخ محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن، الرياض، 1426هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «أَقْرَبُ مَا يَكُونُ الْعَبْدُ مِنْ رَبِّهِ وَهُوَ سَاجِدٌ، فَأَكْثِرُوا الدُّعَاءَ».
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya ce: "Mafi kusancin lokacin da bawa yake kasancewa ga Ubangijinsa shi ne idan yana mai sujjada, sai ku yawaita addu'a".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa mafi kusancin lokacin da bawa yake kusanci ga Ubangijinsa shi ne alhalin yana mai sujjada; hakan ya kasance ne saboda mai sallah yana sanya mafi ɗaukakar abin da ke jikinsa a kan ƙasa cikin ƙanƙan da kai da ƙasƙantarwa ga Allah - Mai girma da ɗaukaka - alhali shi yana mai sujjada.
Haƙiƙa (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya yi umarni da yawaita addu'a a sujjada, sai ƙanƙar da kai ga Allah ya haɗu da faɗa da aikatawa.
Fa’idoji
- Biyayya tana ƙarawa bawa kusanci ga Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka -.
- An so yawaita addu'a a sujjada; domin cewa ita tana daga wuraren amsawa.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 350) (482).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 509).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل المبارك (ص780).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 506).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «الدُّعَاءُ لاَ يُرَدُّ بَيْنَ الأَذَانِ وَالإِقَامَةِ».
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba'a dawo da addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana falalar addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama, kuma cewa ba'a dawo da ita kuma ta cancanci amsawa, to ku roƙi Allah a cikinsa.
Fa’idoji
- Falalar wannan lokacin dan yin addu'a.
- Idan mai yin addu'a ya siffantu da ladubban addu'a, kuma ya nufi gurarenta da lokutanta masu falala, kuma ya nisanta daga saɓon Allah, Ya tsare kansa daga afkawa a cikin shubuhohi da kokwanto, kuma ya kyautatawa Allah zato: To shi ya cancanci a amsa masa da izinin Allah.
- Al-Manawi ya ce game da amsa addu'a: Wato: Bayan tara sharuɗɗan addu'a da rukunanta da ladubbanta, idan wani abu ya saɓa daga garesu to kada ya zargi kowa sai kansa.
- Amsa addu'a: Kodai a gaggauto masa da abinda ya roka, ko a kawar masa da sharri kwatankwacin sa, ko a ajiye masa ita a lahira; hakan gwargwadan hikimar Allah da rahamarSa.
Madogara
سنن الترمذي (1/ 253) (212).
سنن أبي داود (1/ 392) (521).
السنن الكبرى للنسائي (9/ 32) (9812).
الثمر المستطاب في فقه السنة والكتاب، الألباني (1/ 200).
توضيح الأحكام شرح بلوغ المرام، لعبد الله البسام (1/ 548).
منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (2/ 309).
فتح ذي الجلال والإكرام شرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (1/ 486).
سبل السلام، لمحمد الصنعاني (2/ 707).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن ابن عمر رضي الله عنهما مرفوعاً: «اتَّقُوا دَعَوَاتِ المظلومِ؛ فإنَّها تصعد إلى السماء كأنَّها شَرارٌ».
Daga Abdullahi Bn Umar -Allah ya yarda da su- zuwa ga Manzon Allah "Kuji Tsoron Addu'ar Wanda aka Zalunta saboda tana rashi zuwa Sama kamar tartsatsin Wuta"
Al-Hakim Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Guji zalunci, kuma kaji tsoron kiran wadanda aka zalunta. Ta hau zuwa ga Allah a cikin sama kamar tana sharri, tana kamanta shi da mugunta cikin saurinta yayin hawa, ko kuma saboda ta fito daga zuciya mai ƙuna da wutar zalunci da rashin adalci, kuma a keta alfarmar kamar wata walƙiya ce a cikin tasirin ta
Madogara
المستدرك على الصحيحين، تحقيق: مصطفى عبد القادر عطا، نشر: دار الكتب العلمية – بيروت، لبنان، الطبعة: الأولى، 1411ه – 1990م.
التنوير شرح الجامع الصغير، لمحمد بن إسماعيل بن صلاح بن محمد الحسني، الكحلاني الأمير الصنعاني، المحقق: د. محمَّد إسحاق محمَّد إبراهيم، الناشر: مكتبة دار السلام، الرياض، الطبعة: الأولى، 1432 هـ - 2011 م.
صحيح الجامع الصغير وزياداته، للألباني، نشر: المكتب الإسلامي.
معجم اللغة العربية المعاصرة، للدكتور أحمد مختار عبد الحميد عمر بمساعدة فريق عمل، الناشر: عالم الكتب، الطبعة: الأولى، 1429 هـ - 2008 م.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إنَّ اللَّهَ طَيِّبٌ لَا يَقْبَلُ إلَّا طَيِّبًا، وَإِنَّ اللَّهَ أَمَرَ المُؤْمِنِينَ بِمَا أَمَرَ بِهِ المُرْسَلِينَ، فَقَالَ تَعَالَى: {يَا أَيُّهَا الرُّسُلُ كُلُوا مِنْ الطَّيِّبَاتِ وَاعْمَلُوا صَالِحًا}، وَقَالَ تَعَالَى: {يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُلُوا مِنْ طَيِّبَاتِ مَا رَزَقْنَاكُمْ} ثُمَّ ذَكَرَ الرَّجُلَ، يُطِيلُ السَّفَرَ، أَشْعَثَ، أَغْبَرَ، يَمُدُّ يَدَيْهِ إلَى السَّمَاءِ: يَا رَبِّ! يَا رَبِّ! وَمَطْعَمُهُ حَرَامٌ، وَمَشْرَبُهُ حَرَامٌ، وَمَلْبَسُهُ حَرَامٌ، وَغُذِيَ بِالحَرَامِ، فَأَنَّى يُسْتَجَابُ لَذلك».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Lallai Allah Mai tsarki ne ba Ya karɓa sai mai tsarki, kuma Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci Manzanni da shi, sai Maɗaukakin sarki Ya ce:
{Ya ku Manzanni ku ci daga tsarkaka kuma ku aikata aiki na gari, lallai cewa Ni Masani ne da abinda kuke aikatawa}.
Kuma Allah Maɗaukakin sarki Ya ce: {Ya ku waɗanda suka yi imani ku ci daga tsarkakan abinda muka azirta ku}. Sannan ya ambaci mutumin da yake tsawaita tafiya kansa ya cukurkuɗe, jikinsa ya yi ƙura, yana ɗaga hannayensa sama (yana cewa): Ya Ubangiji! ya Ubangiji! abin cinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, abin ɗaurawarsa haramun ne, an shayar da shi da haram, to ta yaya za'a amsa masa ga hakan?».
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah tsarkakakke ne, tsarkakakke abin tsarkakewa daga nakasa kowacce iri da aibuka, kuma Mai siffantuwa ne da cika, ba Ya karɓar ayyuka da maganganu da ƙudirce-ƙudirce sai abinda ya kasance mai tsarki, shi ne tsantsa saboda Allah, wanda ya dace da shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, baya kamata a nemi kusanci zuwa ga Allah sai da hakan, daga mafi girman abinda tsarkin ayyuka yake faruwa ga mumini tsarkin abin cinsa, kuma ya zama na halal ne, da hakan ne aikinsa zai tsarkaka, saboda haka ne Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci manzanni da shi, na cin halal da aiki na gari, sai Ya ce: {Ya ku Manzanni ku ci daga tsarkaka kuma ku aikata aiki na gari, lallai Ni Masani ne da abinda kuke aikatawa} kuma Ya ce: {Ya ku wadanda suka yi imani ku ci daga tsarkakan abinda muka azirtaku}.
Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya gargaɗar daga cin haram wanda yake ɓata aiki kuma yake hana karɓarsa duk irin kokarin da ya yi na sabubban karɓar na zahiri; daga cikinsu:
Na farko: Tsawaita tafiya ta fuskokin ayyukan ɗa'a kamar hajji da jihadi da sada zumunci da wanin hakan.
Na biyu: Cukurkuɗar gashi dan rashin taje shi, wanda launinsa ya canja da launin tufansa daga turɓaya, shi mabuƙaci ne.
Na uku: Yana ɗaga hannayensa sama da addu'a.
Na huɗu: Yana tawassuli zuwa ga Allah da sunayenSa kuma yana nacewa a cikin hakan (yana cewa): Ya Ubangiji ya Ubangiji!
A tare da waɗannan sabubban na amsar addu'a ba'a saurare shi ba; hakan saboda abin cinsa da abin shansa da abin ɗaurawarsa haramun ne, kuma an shayar da shi da haram, to ya nisanta a amsa wa wanda wannan ita ce siffarsa, to ta yaya za'a amsa masa?!
Fa’idoji
- Cikar Allah - Mai girma da ɗaukaka - a cikin zatinSa, da siffofinSa, da ayyukanSa, da hukunce-hukuncenSa.
- Umarni da tsarkake aiki saboda Allah - Mai girma da ɗaukaka -, da bin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Anfani da abinda yake ƙarfafa gwiwa akan aiki, inda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci Manzanni da shi", idan mumini ya san cewa wannan yana daga abubuwan da aka umarci Manzanni to cewa shi zai ƙarfafu zai ji ƙwarin gwiwa akan riko da shi.
- Daga abubuwan da suke hana amsar addu'a (akwai) cin haram.
- Daga cikin sabubban amsar addu'a (akwai) abubuwa biyar: Na farkonsu: Tsawaita tafiya dan abinda ke cikinta na karyewar zuciya wanda shi yana daga mafi girman sabubban amsa addu'a. Na biyu: Halin buƙatuwa. Na uku: Ɗaga hannaye zuwa sama. Na huɗu: Nacewa Allah da maimaita ambatan RububiyyarSa, kuma shi yana daga mafi girman abinda ake neman amsa addu'a da shi. Na biyar: Daddadan abin ci da abin sha.
- Cin halal mai tsarki yana daga sabubba masu taimakawa ga aiki na gari.
- Alƙali ya ce: Mai tsarki kishiyar mummuna ne, idan aka siffanta Allah Maɗaukakin sarki da shi to ana nufin cewa shi abin tsarkakewa ne daga dukkanin tawaya, abin tsarkakewa ne daga aibuka. Idan kuma aka siffanta bawa da shi kai tsaye ana nufi da shi cewa shi mai tsiraita ne daga munanan ɗabi'u da munanan ayyuka, kuma mai siffantuwa da kishiyoyin hakan ne, idan aka siffanta dukiya da shi ana nufin kasancewarta halal ce kuma taka daga cikin zaɓaɓɓun dukiyoyi.
Madogara
صحيح مسلم (2/ 703) (1015).
التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية، لإسماعيل الأنصاري (ص27).
شرح الأربعين النووية، لابن عثيمين (ص141).
الأحاديث الأربعين النووية مع ما زاد عليها ابن رجب وعليها الشرح الموجز المفيد (ص22).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com