Mafi kusancin lokacin da bawa yake kasancewa ga Ubangijinsa shi ne idan yana mai sujjada, sai ku yawaita addu'a
عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «أَقْرَبُ مَا يَكُونُ الْعَبْدُ مِنْ رَبِّهِ وَهُوَ سَاجِدٌ، فَأَكْثِرُوا الدُّعَاءَ».
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya ce: "Mafi kusancin lokacin da bawa yake kasancewa ga Ubangijinsa shi ne idan yana mai sujjada, sai ku yawaita addu'a".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa mafi kusancin lokacin da bawa yake kusanci ga Ubangijinsa shi ne alhalin yana mai sujjada; hakan ya kasance ne saboda mai sallah yana sanya mafi ɗaukakar abin da ke jikinsa a kan ƙasa cikin ƙanƙan da kai da ƙasƙantarwa ga Allah - Mai girma da ɗaukaka - alhali shi yana mai sujjada.
Haƙiƙa (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya yi umarni da yawaita addu'a a sujjada, sai ƙanƙar da kai ga Allah ya haɗu da faɗa da aikatawa.
Fa’idoji
Biyayya tana ƙarawa bawa kusanci ga Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka -.
An so yawaita addu'a a sujjada; domin cewa ita tana daga wuraren amsawa.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 350) (482).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 509).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل المبارك (ص780).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 506).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com