Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ba'a dawo da addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama

عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «الدُّعَاءُ لاَ يُرَدُّ بَيْنَ الأَذَانِ وَالإِقَامَةِ».
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba'a dawo da addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama".
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana falalar addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama, kuma cewa ba'a dawo da ita kuma ta cancanci amsawa, to ku roƙi Allah a cikinsa.

Fa’idoji
  1. Falalar wannan lokacin dan yin addu'a.
  2. Idan mai yin addu'a ya siffantu da ladubban addu'a, kuma ya nufi gurarenta da lokutanta masu falala, kuma ya nisanta daga saɓon Allah, Ya tsare kansa daga afkawa a cikin shubuhohi da kokwanto, kuma ya kyautatawa Allah zato: To shi ya cancanci a amsa masa da izinin Allah.
  3. Al-Manawi ya ce game da amsa addu'a: Wato: Bayan tara sharuɗɗan addu'a da rukunanta da ladubbanta, idan wani abu ya saɓa daga garesu to kada ya zargi kowa sai kansa.
  4. Amsa addu'a: Kodai a gaggauto masa da abinda ya roka, ko a kawar masa da sharri kwatankwacin sa, ko a ajiye masa ita a lahira; hakan gwargwadan hikimar Allah da rahamarSa.
Madogara

سنن الترمذي (1/ 253) (212). سنن أبي داود (1/ 392) (521). السنن الكبرى للنسائي (9/ 32) (9812). الثمر المستطاب في فقه السنة والكتاب، الألباني (1/ 200). توضيح الأحكام شرح بلوغ المرام، لعبد الله البسام (1/ 548). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (2/ 309). فتح ذي الجلال والإكرام شرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (1/ 486). سبل السلام، لمحمد الصنعاني (2/ 707).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SABABAI NA AMSAR ADDU'A DA MASU HANA AMSARTA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com